BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 71 to 80 (The End)

Tsayuwa ya yi yana dubanta ya ce” me kika zo yi?

Walyn ta yi kalar tausayi ta ce” aman ai gidan mijina ne ko? Na zo a bani part dina na zauna a gidana nima ,

Murmushi ya yi ya girgiza kai ya ce” yau kuma ina maganar al.adu? Yaushe batube ke hada mata gida guda? 

Walyn ta ce” aman ai adalci na nema ko? 

Wardugu ya yi murmushi ya gyada kansa, ya ce” kin ga, bama son rigima, idan nan din kike so, ita sai ta koma can, ko ta koma wani, idan kuwa wani kike so ki je ki zaba ai kin sansu gidajen sai a kara gyara maki ki koma kin ji Walyn?

Walyn ta gyada kanta, can ta ce” dan Allah ka maida ni gida,

Wardugu ya dubeta da kyau ya ce” ki je zan zo,

Walyn ta ce” to motana ba mai, kuma bam fito da cart dina na banki ba,

Wardugu ya gyada kansa, daman ya san maganar dai ba zata fice hakan ba, dan haka ya mika mata cart dinsa ya bata sabon cod din da ya saka , sukai salama ta tafi da niyar sai ya zo,

Cike da kurna take tuki, zako ta zabi gida, gidan da ya hada haya take so, wanda gwamnati ta dauka ake projet a ciki, shi take so a gyara mata ta koma, dan kuwa ta san zata bada kala,

A haka ta karasa gidan mamanta ta kai mata kudin da ta yi mata alkawar sannan ta juya ta nufi gidanta dan kuwa yanzu du ta watsar da kawaye,  dan ta san idanma ta koma cudanya da su zata sha habaici a fakaice ne,

Tana zuwa ta zauna bakin kujerar falonta ta yi jigum, bafa ta da mahaifa! Abinda ko.mahaifiyarya bata sani ba,

An juya mata mahaifa, du dan gudun ta kara samun cikin da wuri, ko kuwa ta haihu du ta lalace dan ta ga daga an haihu ake zama rusheshe ko du a lalace , tana yawan tuna maganar Wardugu da ya ce” me na rage ki da shi da ba zaki haihu da ni ba?

Yana son yara har haka? Yanzu ina zata je a gyara mata mahaifarta? Dan kuwa bata yarda da maganar doctern garinnan ba,

Zata kwontar da hankalinta, ta sada kanta, har ya amince mata ta tafi india a dubata, a yi mata aiki a gyara mata mahaifarya, itama ta dawo ta haihu sai ta ga yanda za.ayi gata ta haifar masa abinda yake so, ta tabata soyayarta zata dawo kamar da a ransa!   

(BAK’A CE BA NA SIYARWA BANE, FANS DU WANDA YA BIYA DAN KARANTA BAK’A CE NI DAI MARUBUCIYARSA KYAUTA NA YI SHI, SAJIDA CE)

washe gari ya kama asabar, tana zaune ta gama waya da Ayya kan ta tsife kanta za.a zo a yi mata kitso, tana zaune tana tsifar kan tana mai jin zuciyarta na tashi haka kawai , bata san me ya shiga turaran wutar da ta saka yau ba, du sai take ji kamar an canza mata shi kamshinsa baki daya,

Tana cikin haka ta ga shigowarsa,

Tana kokarin ta hade gashin ta mike ta hango su,

Su duka uku ne da wata datijuwa mai kama da Anna,

Bata san lokacin da ta mike ta kwala karan murna kamar yanda suka yi ai kuwa da gudu suka makalkale juna,

Ihun murma suke kowace na kama sunnanta, itama sai kama sunnayensu take suna latsa jikinta da mamaki itama sai kallonsu take da mamaki inda Wardugu da Anmou ke tsaye shi yana sakin murmushi dan ba a gidan ya kwana ba, zuwansa kennan ya zo ya sanyo su , anmou kuwa na dariya itama gannin yanda Agaishat ta rasa inda zata tsaya ta kalli wannan ta juya ta kalli wancen sai kawai ta saka kuka ta dora kanta saman kafadar Gaishata ta ce……

???????????????? *BAK’A CE* ????????????????

                            Na

                     *SAJIDA*

                          8️⃣6️⃣

*KUTKALE* (PRISON)

*AURE YAKIN MATA NE*

*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*

daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA*  in sha Allah,

……..kar ku bari a baku labari…..

*ALHAMDULILAH ALHAMDULILAH ALHAMDULILAH*

              *ND*

                        *ND*

                                     *ND*

Wardugu kam juyawa ya yi ya nufi gidan Ayya domin a jiya da ya je gidanta fatatakarsa ta yi kamar kwanakin nan da suka shige,

Yau kuwa da kanta ta yi kiransa tana son ganninsa,

Yana zuwa gidan Ayya ya zarce dakinta,

Kwonce take saman bed sinta idannuwanta lumshe, aman kwonciyar ta mutunci ce domin ko.inanta a rufe ruf,

Da sauri ya karasa ya duka inda take ya ce” Ayya, baki da lafia ne? Me ke damunki Ayyana? Tashi na gani Ayya?

Ayya dake kwonce ta lumshe idannuwanta ta ce” Wardugu, ka zabi mahaifinka yanzu ko? Ka zabe shi a kaina ko?

Wardugu ya kama hannun nata da ta janye ya janyo ya dora gefen fuskarsa ,

Muryarsa ce ta raunana, ya ce” bani da tamkarki du duniya,

Sai dai shima haka,

daga ke sai shi a duniyata,

Ayya ta yi shiru, can ta ce” mutumen da ya zabi mace a kan iyalinsa? Mutumen da ya auri yarinyar da na guji dana ya aura dan ban yarda da tarbiyarta ba, mutumen da mai yiwuwa ya yi zaman aure da macen da dansa ya gama gannin sirinta,  na san baka aikata zina da ita ba Wardugu, aman kuma na san da ba yanda ba zata yi ba dan jan ra.ayinka,

Sai yanzu da ya rasata zai waiwaye mu? Sai yanzu zai san da zaman mu?

Wardugu ya rike hannun Ayya da kyau yana dubanta ya ce” ki yi hakuri, 

Gani gabanki, duke saman gwuiyoyina, ina mai neman sulhu,

Sulhu kawai na roka a wajenki mahaifiyata, ba zan roke ki kara zaman aure da shi ba idan hakan bai maki ba,

Aman ina so ku daina gaba, a fitar da fushin nan ,

Ayya ta mike zaune tana dubansa, 

Kanta ta girgiza kawai sannan ta ce” ba komai, Allah ya shige mana gaba, ni na yafe masa, ba maganar gaba tsakaninmu, aman kuma bana tunanin zan iya rayuwar waje daya da shi again,

A barni na huta,

Wardugu ya amsata yana mai gyada kai, ko ba komai ya ji dadin cirw fushin dake tsakaninsu,

Maganar wancen kuwa, ya barwa Allah zabi,

Haka suka jima suna hira da Ayya , nan yake fada mata zuwan yan uwan Agaishat, daman sun zo sun gaisheta Gukunni ya kawo su satin da ya shige, nan ta yi murna kafin ta ce” Allah ya sa dai kar su fada mata wannan lamarin,

Gabansa ya ji ya fadi, Ruwan tea din da ya dauka zai kai bakinsa ya dakata,

Mikewa ya yi ya yiwa Ayya salama ya dauki hanyar gidansa,

Yana zuwa ya shige ciki direct dakinta domin bata falo, kuma da alama bakin sun jima da tafia,

Kwonce ya ganta cikin bargon, sai rawar dari take,

Da sauri ya ajiye kys din hannunsa ya karasa inda take kwonce ya yaye bargon yana dubanta ya ce”Orronur, lafia? Menene?

Hawayen da ta sha ne ta yo gagawar gogewa cikin dabara da hannunta, kafin ta mike a hankali dan ya kamata so yake ta mike din,

Jikinsa ta shige ta yi lamo tana duban gashin dake kwonce saman hannunsa,

A hankali ta dora hannunta tana shafawa , cikin nutsuwa ta ce” kuma du wannan abin da aka yi dan a tara dukiya aka kare ba komai, karshema yanzu mijin Gaishata ke fadin an nemesa an rasa,

Ribar me ya ci? Ko zaman da aka yi idan ya karbi kudin auren yan uwanmu basa jimawa yake batarwa ta hanyoyin da basu da kyau kuma ya dawo ya shiga hangen wasu, uku sun rasa ransu ta haka,

Ashema duka zaman bai gina shi da aure ba? Ashe mu dukanmu ba daya da aka haifa da aur……….

Hannunsa ya saka ya rufe mata bakinta, 

 Cikin nutsuwa ya  ce” wanda ya halice ku, haka yake son ganninku,

Kuma muma bamu da damuwa da hakan,

Kanta ta dora saman kirjinsa tana mai jin wani girmansa, kunyarsa, kaunarsa na kara shiga cikin jinnin jikinta,

A hankali ya karkata ya sauka da ita ya ja hannunta bayan ya dauki yar ledar pharmaci din da ya shigo da ita ya nufi bayi da ita,

Yar robar dake cikin abin ya mika mata , fuskarsa ya shagwabe kamar wani yaro ya ce” Orronur, dan bani fitsarinki kadan a nan kin ji??

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button