BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 71 to 80 (The End)

daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA*  in sha Allah,

……..kar ku bari a baku labari…..

*Walahi ma cherie, Madame dakoro ina jin nauyinki da kunyarki, kin kasance mai mugun alkhairi a gare ni, ki sani aminiya kuma yayata ko sako ne ki turo na wanda kike so a farantawa ta hanyar nvl da dukan abinda Allah ya hore min, in sha Allah ba zan baki kunya ba, na gode na gode*

Ya nuna daidai zuciyarsa still kansa na saman cinyarta,

Jinsa yake bashi da wani karfi, jinsa yake bashi da wata dabara, dan Allah kowama ya ji kuma ya shaida yana kaunar yarinyar Ayya, 

Jikin Ayya ne ya mutu, a ranta tana fadin shikenan ya fada, eh lale, aman aurensa fa? Matarsa fa? Aurensu duka duka shekara nawa? Wannan tada ce al.ada ce ta iyaye da kakani, ba.a yiwa macen tubawa kishiya haka gatsal sai idan ta yi haihuwa uku zuwa hudu ko ta samu kwararun shekaru da mijinta a kafan bakwai abinda ya yi sama, daman a dangi a baki suke, an sako su a gaba, komai kanantar abu idan Wardugu ko ita suka yi zaka ji ya yi gagawar zagaya dangi a labe a yi da su aman a gabansu ba.a nunawa sai dai a yi ta masu fadanci, tana cikin rudani……sai dai kuma wannan lamari mai girma ne, ya kasa jurewa, ya kasa kawar da kai, abin na bashi wahalar da ya kasa hadiyewa sai da ya fada! To aman ba a nan gizo ke sakar ba, ita Agaishat din da bata san me yake ciki ba? Bai fada mata ba, bai nemi soyayarta karara ba, shi girma girma, shi bai san ta yaya gododo da shi zai tsaya gaban yarinya ya ce da ita yana sonta ba, gashi ya tada dan karamin yaki a gidansa wanda take fatan Allah ya tsawatarwa abin, aman kuma ya fake a bayan fage,

Ita kam, ba zata taba tirsasawa Agaishat ta so Wardugu ba, aa, ta yaya? Ace da ita me? Dan danta ne? Dan ita ta haife shi? Ita kam tana da kunya!

Yawu ta hadiye kafin ta saka hannunta ta dago da kafadarsa,

Abinda ya cika idonta ta mayar kafin take dan dukansa a kirji ta ce” Wardugu? Dama zaka taba sarewa kan mace? Ka zauna kanai min rigima tamkar wani baby kan yarinyata? To ni me kake so na yi maka bayan ka san lamarin nan ba zai taba yiwuwa ba dan duka duka yaushe ka yi aure? 

Wardugu ya bude jajayen idannuwansa ya dora kan mahaifiyarsa , ya jima a haka kafin ya ce” a gabanki, sai na iya yin kuka, tunda kika haife ni, kika sha gwagwarmayar rayuwa wajen rainona da komai nawa ai ba zancen na kai kukana wani wajen, 

Ayya ni ba zan bude bakina na dubi yarinya karama kamar Agaishat nace da ita ina sonta gatsal haka kawai salon ta raina ni, sannan Mu.azam dake wani takamar ya aureta ya saketa dan ni kennan ya ji dadin kara fada ko me?

Haka fa yarinyar samari ne da ita fa, kin ga wani shegen buzu wuyansa na lauyewa yana jawo shi kwana ya yi ya wuni yana kiranta yau shi ne har wajen dinern nan, Ayya kinfa san yaren nan na zamani ko wasa kake da su yanzu zasu samu hanyar rainaka! 

Ayya ta shiga girgiza kai tana murmushi a kasan zuciyarta ta ayana” da sauranka, zako ka ga halin yarinta! 

A fili kuwa ta ce” Wardugu, maganar Walyn fa? 

Wardugu ya mike tsaye kafin ya koma saman kujerar ya zauna kusa da Ayya sosai ya ce” Ayya, shin adini ne? Aurena da Walyn kusan shekara hudu fa , Ayya kece shaidar irin rayuwar auren da nake da Walyn duda ba zuwa nake ija baki labari ba, aman du lokacin da kuka hadu sai haukan ya bayana , Ayya, yanda kika san rayuwar tumakai haka muke da Walyn, 

Sam bata zauna bama, ta fahimci waye ni, ta fahimci menene ainahin zaman auren bale har ta wani kula da shi, 

Takamarta kyau, wayonta yawo, isarta ta je wajen yawon ta yi gadara da kudin da ni ke nema, 

Kishi….sakaran kishi, in ba dan ina tsaye a gidana ba Ayya da Na rantse maki Walyn ko ke sai ta hana ni yiwa magana bale wata mace a duniya, tarota nake , lalabata nake, kwatanta mata nake, fushina nake nuna mata , ko zata yi hankali ? Ko zata gane ni ne gaba da ita? Ni ya dace ta bi? Aman cikin kwakwaluwarta banda kusoshi ba komai, gashi ina zaman zamana, ta sa na shiga wata rayuwar ta shirme! Shirme mana Ayyana …. wai ka zauna tunanin yaro karami? Ayya zan koma kauyensu yarinyar cen, na fadawa iyayenta komai abubuwan dake faruwa, na fada masu ina neman aurenta,

Ayya ta mike ta ce ” kul, kul, kar ka yarda yarinyata bata aminta da kai ba ka wani je neman aurenta, ba wanda zai mata karfi, kana magana rigima na yawo a harshenka, to ka zauna min ba inda zaka yau, dan na san in dai ka fita a gidannan sai ka tafka wani abin !

Ta karashe tana yafa mayafinta ta nufi hanyar kicin inda wardugu ya bita da kallon mamaki,

Ayya kennan, a duniya ba wace yake zuwa ya sanarwa sirinsa mafi sirri irinta, yana da rike abu gaban kowa aman ita yana gagawar sanar da ita damuwarsa ko farin cikinsa, tana kuma iya yinta dan gannij ta shige al.amarinsa, bata taba saka wani ya yi masa abu ba, sai dai yau gashi wai wai shi ya fada mata zai mutu ko zata tsorata? Aman wai tace da shi ya nemi soyayar yarinyar? Daga yanzu ya yarda yarinyar nan ba shi kawai ta gama halakawa ba, har Ayyansa ta kwace! Yar Buzuwa ta iya kwace,

Wayarsa ce ta dauki kuka,

Dagawa ya yi domin mijin Alhinayett ne, 

Mikewa ya yi da kyar ya fice ya nufi can tsakar gidan,

Tarar da su ya yi cikin mota Alhinayett sai kumbura take tana karawa kan ita su biyo kafin su tafi,

Wardugu ya yi tsaye ya kare mata kallo, kafin ya maida dubansa wajen Colonel ya ce” walahi idan ka yi wasa ta fahimci halin da kake ciki na mugun sonta da kake zata mayar da kai hotiho!

Kai yanzu gabjejen kato da kai, ta sakoka gaba ka kawota wai ta ga lafiata lau? Da ni na haifeka yau da sai na baka shegen duka, yo ina anfanin wannan lamari? 

Sai da wardugu ya gama yi masa fada tsaf sannan ya taka ya karasa wajen motar,

Kwonkwasawa ya yi ta bude, tana dubansa kafin ta ce” Wardugu lafiarka kalau? Ina Agaishat din? 

Ce maki na yi bani da lafia?

Wardugu ya fada yana zazaro mata idannuwansa,

Da sauri ta dube shi da kyau kafin ta ce” gani na yi hankalinka a tashe,

Ohk shi ne kika tiso keyar danki ya kawo ki? 

Ya kuma bata amsa yana hararanta,

A ranta ta fadi” To fa,

Wardugu ya nunota da yatsarsa ya ce” walahi na san ciwon kaina, ba zan bari ki wulakanta bawon Allah ba nima Allah ya kama ni ta hanyar saka wani dan rainin wayon ya wulakanta ni, ke yanzu da nine aka tiso keyata zuwa ganninki a lokacin da nake ango me zaki kalen? Alhi, bana son ki kaini wajen da zan rike makogworon wuyanki, walahi a kan aurenki idan baki zama mace mai kyawawan dabi.u abin alfarin mijinta ba, zan tarda ke har inda kike na ya gashinki a kasa ! Ke ni ba nasiha ko rarashinki zan ba, ke kanwata ce, idan kika zubar da mutunci da darajar gidanku , kika aniya wulakanta wannan mutumin ni zan masa aure da kaina sannan na tataka ki idan kina so ki rufe ni,

Kiwit kiwit take da ido bata ce da shi komai ba, dan ta san idan hakuri tace zata bashi yanzu abin zai girmama, yi masa shirun shi ne ya fi sauki, sannan ta yi dan daman bata matsa kan su biyo ba, ita wollah yannayin Agaishat ne ma ya tsaye mata a rai, bata so ko kusa Agaishat ta saka tsoron Walyn a ranta, ta so ta ganta yau ta fada mata abinda ya sa Walyn yi mata haka sannan ta karfafa mata gwuiwa, kanta ta sada har ya gama fadansa wanda tana tunanin taka kaya ne dai suka yi, dan kuwa har colonel din da ya biye mata sai da akai masa ,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button