BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 71 to 80 (The End)

Wayo yar muleka????????????????

???????????????? *BAK’A CE* ????????????????

                            Na

                     *SAJIDA*

                          8️⃣4️⃣

*KUTKALE* (PRISON)

*AURE YAKIN MATA NE*

*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*

daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA*  in sha Allah,

……..kar ku bari a baku labari…..

Yana sake saken tarin mugunta ya karasa gidan,

Bai yiwa kowa magana ba, bai shiga hurumin kowa ba  kamar yanda ya fita ya nufi hanyar sada shi da ciki, inda kowa ya shiga tatara kafafuwansa yana barin wajen dan ba zai so abinda za.a kula da wani laifi nasa ba,

Bata falo, hakan ya sa ya zarce dakinta na barci,

Nanma bata nan, dan haka ya fito ya nufi kicin,

Dago kan da zata yi ta ganshi ya nufota,

Yannayin fuskarsa ya sakata sakin nade naman da take cikin kabeji zata yi name,

Da sauri ta mike daga kan kujerar mai ruwan silba ta daga kafarta,

Kafin ta shige inda zata shige dan ta san wannan zuwan nata je, dan irin kallon zaki ci yan garinkun da ya yi mata ya saka hanjin cikinta motsewa waje guda,

Rikotan da ya yi da karfi sannan ya fincikota baya ya jefar cikin kicin din,

Yau ta ga rana ta ga tashin hankali domin binta ya yi inda take yaden nan ya wanka mata wani lafiyayen marin da ya dauke jin ta,

Tabas wani dummmm ta ji na lokaci mai dan tsayi domin za.a kai second ashirin hakan ya saka bata ji fadansa na farko farko ba sai da kunnen nata ya dawo ta fara tsintar fadansa kamar haka” *Ba zai yiwu kema ki wulakanta min zuciya kamar yanda ta wulakanta min ba!* ta yayama zan fita daga gidannan raina bace , baki damu da yi min wani abin da zai faranta min ba sai faman ki dura min abinci kafin na fita bayan ina azumi? Ya zan je ma.aikata kin san wani irin aiki nake yi aman ki turon message gatsai gatsai da rashin tauna zance ya zama dadi kamar ke ce gaba da ni ki turo min, oho o na ji abinda zan ji ko? Da wannan dan iskan ne da ya zo wajen diner mai dogon wuyan nan yana launi uwa lagwani da kin zauna kin ware yare kin masa tausasa ko? Da ace tsohon mijinki ne kin iya yi masa kalamai, wanda nima shaidar shi mai daraja ne ana bashi kulawa ne ko? Ni zaki turowa sako da kama sunana kai tsaye tamkar dan gidanki? Sai mutun ya gama mutuwar muku ku wulakanta shi ku zubar da shi ku kara gaba abinku ko? Ku buzayen nan haka halayenku yake? To bari ki ji, a kaina an tsaya, walahil azim Agaishat hanya a bude take, kafarki ke ta taka waje da niyar barina sai na harbe ki! Sai dai a kashe ni! Jarabawata ce soyaya da buzuwa? Na karba, aman kuma rantsuwata ce ke ce buzuwar karshe da zan ringa mafarki ina juyi kanta! Ke ce zan yiwa son karshe a cikin buzaye na wahala dan buzuwa! Ke ce wace zata rayu da ni ko a wani hali, ke rabon haihuwarki da wani namijin sai dai idan ajali ya dauke ni!

Hannunsa ya buga jikin madubin kicin din da aka kafa kato domin ado inda ya fashe dan kuwa mai fashewar ne, ya tako zuwa gaban Agaishat dake zaune, cikin wani irin firgici da bugawar zuciya mai tsanani ya dubeta ido cikin ido ya ce” ke ko mutuwa na yi, Allah ya isanmin idan wani ya shiga gonata (Dankari, ka ji masifa fa, an taba yin haka dama?),

Sai da ya gama tashin hankalin da ya dirmiyar da ita cikin wani yannayi na furgici da tsoro, kara jin shayinsa, tashin hankalin abinda ya ringa maimaitawa a fadansa *ba zata wulakanta masa zuciya kamar yanda Aisata ta wulakanta masa ba,* sannan ya juya ya fita a kicin din,

Kafafuwanta ta hado gaba daya ta hade a jikinta, barin da jikinta yake yi ta samu ta daidaita ta hanyar adu.a,

Mikewa ta yi ta je wajen kayan da take gyarawa ta harhada komai ta kimtsa still jikinta na rawa sannan tana share hawaye ta ajiye komai wajensa ta fito,

Sai da gabanta ya fadi ganninsa a fallon, bai fita ba kennan, yana waya da alama da Ayya yake dan a tubancin da yake tana tsintar yan kalmomi da kuma sunnan Ayyan

So ta yi ta koma kicin din, sai dai wani abin ya hanata dan haka ta taho a hankali ta raba ta nufi dakinta,

Da kallo ya bita ya ci gaba da wayar, sai da ya gama ya taka zuwa dakinta, tun da ya fara fadan nan ko ci kanka bata ce da shi ba, yanzun ma da ya shigo yana ta muzurai ya bala mata harara kafin ya karasa ya tsaya kusa da ita ya ce” wato ga mahaukaci ko Agaishat? Shine kike nufi na yi na gama ko?

Agaishat ta dago da idannuwanta da suka rine dan tsabar shiga tashin hankali ta dube shi, 

A hankali ta ce” ka yi hakuri,

Wardugu ya ce” hakuri? Hakurin me zan yi a ciki? Na rashin bani muhali a rayuwarki ko na raina ni da kika yi?

Agaishat ta kuma dago da kanta, wannan karron bata sada duban nata ba ta kafe shi tsai da kallo,

Fitina kawai yake ji, so yake ta biye masa kamar yanda suka saba da matarsa ya tataka banza ya yi gaba abinsa, tabas ta yi rayuwar rashin sannin ciwon kai, aman bata tunanin zata yi rayuwar duka a gidan miji,

A hankali tana dubansa ta ce” menene laifina? Meye na yi mai girma haka? Ka taba nunan baka son sunnan nan? Ince kulunma da shi nake kiran ka kuma ka amsa ba tare da ka nunan bai yi ba, menene? Ganninka a irin halin nan an taba *AISATA!* 

ido ya zaro yana dubanta, kai kai kai,

Agaishat ta ci gaba” dan Allah ka yi hakuri, kar ka saka ni a irin wannan rayuwar, ban iya ba, ban iya wannan rigimar ba, idan na bata maka ne ka yafe min, sannan ka daina tuna baya kana hada ni da wasu gardawa da aurena kuma na san darajar auren nawa, 

Tana magana ne gabanta na dokawa, aman dan karfin hali sai da ta gama cikin sanyin hali tana hankalce da yannayinsa, kafin ta juya a dabarance ta yi wajen bayi ta tsaya gannin bai juyo ta tabatar da tunanin abinda zai mata yake dan haka da dan gagawa ta bude bayin ta shige ta rufo kofar sannan ta duka daga kasa ta ce” kuma Aisata dai ko? Zamu kai kukanmu wajen Allah ya raba tsakanin nan dan haramtace ne!

Da sauri Wardugu ya juyo sai dai ganni ya yi wayam, bata nan,

Kafarsa ya daga ya je ya tura bayin , aman a rufe ruf,

Wai waiwai dukan kofar ya shiga yi yana fadin” me kike nufi? Me zan yi da wannan banzar da ta banzatar da kanta? Me zan yi da macen da ta auri ubana dan abin duniya? Ki bude ki fada min abinda kike nufi da wannan maganar,

Haka ya yi ta bambaminsa kafin yake yin sanyi a hankali ya kai kasa ya zauna jikin bayin ,

Muryarsa ta tabatar mata da kamar ya shiga duniyar tunanin maganarta, inda ya ce” Ya zaki saka na mare ki?

Agaishat dake zaune itama tana sauraronsa, ta lumshe idannuwanta, walahi da ita fara ce ta tabata yau da sai ta nemi maganin tashin fata, aman yanzu haka jin idonta take da nauyi, ta maru fa, 

A hankali ta shafa wajen , muryarta na rawa ta ce” dan me ba zaka mari matar cushe ba?

Wardugu ya dubi kofar bayin , bai san lokacin da ya saki murmushi ba ya ce” ke ce matar cushen?

Agaishat ta gyada kanta tamkar yana kallonta kafin ta ce” haka ne,

Wardugu ya ce” to fito ki ji,

Agaishat ta yi murmushi sannan ta yi irin na yara kafin ta ce” aa,

Aa? Ya maimaita a hankali yana zaro idannuwansa da mamakinta,

Agaishat ta ce” eh, ina tsoron duka, bana son duka,

Wardugu ya yi shiru, nan ya ji tausayinta ya kama shi, bata son duka, ya zo da bacin ransa ya sauke saman kanta, 

Idannuwansa ya lumshe ya ce” kin san menene ma.anar Orronur?

Agaishat dake zaune dandabar cikin bayi daga ita sai yar doguwar riga ta kanti da ta saka take aikinta rigar bata da nauyi , sannan da kadan ta fi gwuiwarta tsayi, kanta ko dan kwali babu 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button