BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 71 to 80 (The End)

Tsarki ya tabata ga Allah, sarkin da ya halici bayi, sarkin sarauta rabih, 

Ga yarinyar nan, wannan itace mai kama da shi din, ga kamarsa karara a fuskar yar, har irin yanda idonsa keda tsaga da girma,

Tsai ta yi tana dubansa, kwarai ta ga kamar fuskarta a tare da wannan mutun , sai dai tunanin ta ina? Ta yaya? Ita yar asalin timiya fuduk zata hada jini da mutun haka Wanda suturar jikinsa kadai ta isa ta shaida shi din ko waye? 

A hankali ta bi hannunta da ya rike da kallo, yatsutsansa irin nata,

Da sauri ta dago zuwa fuskarsa, sai kuma ta juya wajen Ayya gabanta na dokawa ta ce” Ayyana, wanene wannan?

Ayya dake ta kokarin maida kukanta ta ce” Agaishana, kakanki ne, ta karashe tana mai sakin kukan dan ta kasa rikewa,

Agaishat ta janye hannunta tana dubansu su duka, da sauri ta je wajen Ayya ta ce” kukan me kike? Wani ne ya mutu? Kaka kuma? Ni nake da kaka? Me ya saka ki kuka Ayyana?

Wardugu dake duban Ayya kansa kawai yake girgiza mata dan kar ta fadawa Agaishat abinda ya sakata kuka, baya so, abin sai ya yi masa yawa, bai sanba ko zata yi tawakali ta yi hakuri?, dan haka a hankali ya lumshe idannuwansa yana ji Ayya na fada mata gaskiyar waye gukunni a wajenta, wato mahaifin mahaifiyarta, 

Cikin nutsuwa ta warware mata yanda suka hadu da Algabit, sai dai sam Ayya bata fada mata dayar maganar ba,

Farin ciki kam ta ji shi, sosai ta yi murna, sannan ta yi adu.ar shiriya ga mahaifinta, domin bata da abin cewa kansa ita kam,

Nan aka kuma shaida mata rashin lafiar Anna dalilin tonuwar asirin , 

Da da uwa, nan ta yi sokoko ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, du sai ta ji duniyar ba dadi, 

Kanta ta sada dan kar ta nuna mugun damuwarta har abin ya taba Ayya, domin zuwa yanzu ta gama yarda da soyayar Ayya a kanta tamkar ta uwa da d’a ne,

Dubanta ta kai wajen Wardugu idannuwansa a lumshe ko barci ma yake? 

Bai ci komai ba , shi ne ya fado mata a rai haka kawai, dan haka ta mike ta nufi kicin ba tare da ta kara bi ta kan wani ba,

Nan Ayya ta fara fada masa maganar auren Agaishat din da ya mutu, 

Sosai abin ya dake shi, har ya tambayi ba.asi?

Wardugu dake zaune ya ce” bashi da huja, 

Ayya ta kai dubanta kansa, ta girgiza kai ta ce” ya gabatar da hujarsa, wace sam bai dace dan wannan hujar a saki mace ba, batai masa laifin komai ba, shima bai mata ba, hasalima tun kafin a yi masa aikin ya yi sakin, bisa hujarsa na aminin nasa ya fi shi son ta! 

Dum gabansa ya fadi, da sauri ya kalli Ayya, la.ila ha ilala , shi ne abinda ya iya cewa, ya ake maganar yana magana kai tsaye bayan ga wada ke yi? Bai taba zaton, bai taba kawowa ransa cewar Ayya zata fadi maganar haka kai tsaye ba , 

Shiru ne wajen ya dauka, kafin Ayya ta ci gaba” na ji ba dadi, na yi fushi, Aure? Sai kace abin wasa? Ya tashi ya guntule igiyar auren yarinyar da bata san me ake ciki ba? Kan wani shirme? , shima Wardugun ya nuna masa ba dadi, maganar da nake maka har yanzu ba wani jituwa tsakaninsu, 

Nan ta kwashe du abinda ya faru ta sanarwa Gukunni da da farko ya dauki zafi har ya ga kamar an wulakanta yarinyar ne dan anai mata kallon marar gata, sai dai daga baya da ya ji komai ya yi tsam ya dubi Ayya, ya kuma dubi Wardugu da ya dafe kansa yana tunani, aa, du wannan jawabin na menene? Ya Allah????????‍♂️

A daidai lokacin da Agaishat ta fito dauke da farantin da ta soyawa Wardugu dankalin turawa da plantain ta nufo falon, 

Muryar Gukunni ta karade wajen da tambayar da ya saka ni ranaza har na saki biron hannuna,

Gukunni ya dubi Wardugu ya jefo tambayar da basu tsamaci zai yita ba, Gukunni ya ce” *SHIN DA GASKE KANA SON AGAISHAT NE? ZAKA IYA AURENTA KODA KUWA TABON DA RAYUWARTA KE DA?**************

                 MEMBERS BAK’A CE GRUP, WOLLAH INA JI DA KU TAMKAR NAMA DAYA A MIYA, 

WATO KUNA SAKANI NISHADI DA COMMENT DIN KU,

HAR KUKE SAKAWA NA JI NI YESSSSSS NI DIN TAKU CE????????????????????

???????????????? *BAK’A CE* ????????????????

                            Na

                     *SAJIDA*

                          7️⃣7️⃣

*KUTKALE* (PRISON)

*AURE YAKIN MATA NE*

*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*

daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA*  in sha Allah,

……..kar ku bari a baku labari…..

Da sauri Ayya ta ce” Aman ya Gukunni, ba shi ya dace a tambayi wannan abin ba, bana so a kuma yiwa y’ata abinda akai mata sai ta zaba! Kuma da ake maganar nan , bai jima da yin aure ba fa, ko cike shekara hudu bai yi, hasalima matarsa na kwonce asibiti dan ya dankara mata maganar cewa yarinyata *Orronur* dinsa ce! , dan Allah kar a tauye min yarinya,

Dubansa ya kai kan Agaishat da ta ja ta tsaya tana binsu da kallo, wai bata fahimci wa ake shirin hadata da shi kuma? Waye matarsa ba lafia? Wardugu ne, meye kalmar Orronur ke nufi? Ya Allah wani hadin za.a kuma yi mata ko me? Hadinma da Wardugu? Mutumen da ita ce shaidar irin yanda yake kwasa da matar so ma bale ita?, mutumen da ta yi imanin har abada ba macen da zata samu gurbi a zuciyarsa kamar yanda *AISATA* ta gama mamaye ko.ina? Domin a yi yawo da ganga ba zata hadiye cewar ba sonta da yake ne ya saka ya kasa yafewa mahaifinsa dan ya aureta ba! Mijin WALYN? ko ba wannan ba, ita ta yi imanin koda daura masa ita za.a yi a kafa zai ja banza a titi sannan ya take da ranjasss ya bale ya jefawa karnuka su cinye banza, ita a wa? Yar wa? Algabitt? Um, yayan manya, manyan kansu suna farauta ? Ita bata son mai kyau dan kar a ringa rububinsa, ita ita…. 

Tunaninta ne ya katse a lokacin da Ayya ta ce” kar mu yi haka da kai,

Tsai ta kai dubanta wajen Ayya a ranta tana fadin” ki yi wani abu, ni ban san wani kaka ba, yaushe ma ya zo gidan? Ki yi wani abu kar a kashe maki d’a, sannan a kashe maki y’a!

Wajen sai ya kasance Agaishat na kallon Ayya da wani yannayi, Wardugu kuwa tsai kawai ita yake kallo yana son sannin halin da ta shiga dan kuwa ya san ba kurma bace, kuma ba sakara bace, tabas ta fahimci maganar da ake, 

Ayya kuwa Na duban Gukunni, inda Gukunni ya gyara zama yana sakin murmushi yana duban Wardugu da yannayinsa, ya san waye shi, ba zai taba amsa shi a haka ba, ya kuma lura da yannayin Agaishat da irin duban da take yiwa uwar rikonta, wani sanyi ya ji a ransa domin ya ga shakuwa, kauna ta Allah tsakanin Agaishat da mahaifiyar Wardugu,

Mikewa ya yi ya yiwa su Ayya salama, inda Wardugu ya mike ya bi bayansa dan yi masa rakiya yana mai jin ba laka a jikinsa,

Sai da suka dangana da motarsa ya dakatar da shi, inda ya dauki katuwar wayarsa ya danna kira,

Dagawa ya yi tare da kara yin salama sannan ya ce” honorable ka samu ganninsa ne?

Gukunni ya yi murmushi ya ce” wato Alhaji, ka manta ni lauta ne kafin na zama alkali, ? Bayan wannan ka manta numberka na niger ne na kira ya shiga ba cod ba komai? Kana ina ne? Domin ina so in sha Allah mu hadu kafin lokacin sallar azahar, ina tare da Wardugu,

Jim ya yi yana jin ba dadi, ya Allah, kowa dai ya san halin da suke ciki da matarsa uwar dansa, koda yake shekara da shekaru its normal,

Fada masa ya yi su hadu a Wardugu Palas, wajen da ya dawo operation irin na da, 

Wardugu kam gum da baki, bai ce komai ba ya bi bayan Gukunni cikin motarsa da bodyguard dinsa biyu suka daga sai wajen da yake ainahin wajensa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button