BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 71 to 80 (The End)

Ku kennan haka zaku kare? Kulun kuna fama da rabiyar fadan cikin kasa bayan ga wanda ya adabi duniya? Ba so suke su kare ba? Zan kuwa karar da su!

Shiru ya yi kafin ya daga murya ya ce” commandan kana da ja ne?,

Amsa aka bashi kafin ya ce” ohk, ni na ce, a zartar!

Kit ya kashe kiran yana kokarin ajiye wayar sukai ido hudu,

Tsakaninsa da Allah sai da gabansa ya fadi, domin wani irin fayau ta yi masa, ga idannuwanta da yake gannin tamkar an kara masu girma, kawar da kansa ya yi, dan kuwa ya tabara fadansa ya sakata bude lulubinta harma ta tsura masa ido, 

Haushin kansa ya ji ya kama shi, ya aka yi bai yi hakuri ba har ya fita a inda take kafin ya dauki kiran?

Wata zuciyar ta ce” kai sai me? Hala tsoronta kake?

Harare ya wurga kafin ya ja tsaki, sai kuma ya kai dubansa wajen Mu.azam ya ga bai kula shi ba, baima dubansa tuki kawai yake, 

A yansa ya shiga mita, oh ni ga mahaukaci, ina fada ita ta tsareni da ido, kai kuwa ka mini halin ko.in kula ko? Ni ba mahaukaci bane, kuma ni ba mafadaci bane????,

Haka ya tamke fuska har suka karaso gidan, wanda du mutane ke fitowa baki wangale, a gaskiya, an tafka gini na zamani…fatan a mora lafia,

Fitowa ya sake yi ya zagaya ya fito da ita bayan ya ja mata rufarta ya mayar mata yanda yake da,

Hannunta ya ja inda mutane ke kallonsu ya nufi ciki da ita, 

Sai da suka shige cikin accenseur ya kara kusancinsa da nata ya ce” kukan bai isa haka ba?

Agaishat ta dan dago ta saci kallonsa, danme yake da fada, wai fa a kashe mutane yace, ita tsoro take a je ta yi wani abu ya harbe banza,

Kuma mamaki take shi ya je ya daukota, dama haka ake a birni ko me? Sannan wai ta bar kuka, yo ita idan bata yi kuka ba me zata yi? Allah ya ceceta da fushinsa.

Kira ne ke ta shigowa dan haka ya rike hannunta ya daga,

Kukan da take rusawa ya saka shi yin dan tsam kafin ya duba number, Walyn ce, dan haka ya mayar a kunnensa ya ce” hm,

Walyn ta ce” kar ka mini haka, na tuba ba zan kara ba, na bi Allah na bi ka, ka rufa mani asiri kar ka kadaice da wata macen bayana,

Wardugu ya girgiza kai a hankali ya ce” dan me?

Walyn ta ce” dan ni kadai kake so, dan ni kadai nake da hurumin ganninka ba……, Wardugu kar ka zubda mutuncina a idon yarinyarnan,

Wardugu ya dan fakaici kallon Agaishat dake biye da shi a hankali, murmushi ya saki ya ce” kai, bazan iya ba, canza wani abin Walyn, yarinyar a shekaru take karama, aman a zahiri ke kanki zaki yarda da baba ce, waima dan ban ga ainahin zahirin ba, da na fayace maki ko dan ki yarda,

Idan ka tabata kashe kaina zan yi, na rantse maka,

Wani wawan tsaki ya ja, kafin ya ce” sai me? Dan kin kashe kanki walahi ba zai hana ni zama da ita ba, ke harma na kara wasu su yi ta min go slow a gabana, ke kuwa kin mutu kafira! 

Wardugu…..ta fada murya shake,

Walyn ya fada yana mai ja ya tsaya,

Walyn ta ce” bani da lafia, sai da aka yi min dinki, ka zo ka duba ni ka ji? Wardugu ka zo ka min cikin na rantse ba zan zubar ba,

Kansa kawai ya girgiza ya kashe wayar yana tunanin bata dadara ba, shi kuwa zai yi watsi da ita har zuwa lokacin da zata yi hankali!

Dubansa ya kai wajen Agaishat, gani ya yi ta dan ja rufar ta bude fuskarta, ta yi wani shar da ita, 

Da hannunsa ya nuna mata inda zasu yi kafin yake dora hannunsa wajen ya bude,

Shi ya fara shiga kafin ta yi adu.a a ranta ta saka kafarta ta dama,

Waouh  shi ne take fada a zuciyarta, masha Allah, a hankali ta taka ta karasa tsakiyar dakin tana bi da kallo, 

Ta shagalta da kallon sai da ya kama hannunta ne ta ankara da ita yake jira ,

A hankali ya yi mata jagora dakin baci, 

Suna shiga ya ja ya jingina jikin garun dakin yana dubanta,

Kafafuwanta dake dauke da jan lale take takawa cikin nutsuwa , a hankali ta juyo tana dubansa, tsaye ya yi kawai yana kallonta dan haka wata kunya ta darsun mata,

Juyar da kanta ta yi, hakan ya sa bata ga zuwansa ba , sai hannunsa da ta ji kusan fuskarta,

Bayan yatsarsa ta tsakiya ya dora gefen fuskarta tun daga wajen girarta ya shafo har zuwa wajen habarta kafin a hankali ya kai wajen lebenta dake zagaye da dan lips kadan ba dayawa ba yana dan sheki,

Idannuwansa ya lumshe sannan a hankali ya saka hannayen nasa ya janye rufar lafayar, 

A hakama an saka mata bakar hula marar ado daga ciki an rufe mata gashinta dake wanke tas ba.ai mata kitso ba, sai gobe!

Hannunsa ya kai wajen kulin da akaiwa lafayar wajen kirjinta, hakan ya sa gabanta dokawa har ta dan daga kanta ta saci kallonsa, sai dai ta ga shi yana yi ne tamkar aikin da zai yi ya gama ne, dan haka ta sada kanta duda ba wani mahalukin namijin da hannunsa ya taba zuwar mata nan, idan ka cire Ayya dake daura mata lafaya ba wanda ya taba samun kusanci haka da ita sai wannan bawan Allah,

Kwoncewa ya yi kafin ya zagaya ta bayanta ya yaye shi ya sake shi nan kasa,

A hankali ya sako hannayensa ta bayan nata ya rungumota jikinsa daga baya ya dora habarsa kan dokin wuyanta,

Muryarsa kasa kasa ya ce” Menene?

Agaishat da jikinta ke rawa rawa ta dan girgiza kai bata iya amsawa ba,

Wardugu ya dan kara goga mata sajen fuskarsa a dokin wuyan nata yana lumshe ido sannan a hankali yana lura da yannayinta yanda du ta firgice da bakon lamarin da bata taba gani ko ji a tare da ita ba, sai ya dauki hakan a wata fasara daban, ganninsa ta saba ne, har ta fara daukan caji… dan haka ya sasauta rikon da ya yi mata ya ja hannunta ya kaita kusan bayin dakin ya nuna mata da hannunsa, sannan ya nuna mata salaya ya juya ya fice,

Wata wawiyar ajiyar zuciya ta sauke kafin take dora hannunta daidai zuciyarta, wai Allahna, shine abinda ta fada….menene wannan? Me yasa idan na ganka nake jin irin wannan faduwar gaba da tsoron ka gusa daga inda nake? Me ya sa ka zama mai zafin taba fatar jikina aman maimakun na hana sai na bige da lafewa a fafadan kirjinka, Sadaukina….bakon mijina, zan kwatanta yi maka biyaya mudin raina, Allah ya bani ikon cin nasara

..

Haka ta shiga bayin da ta so zama yar kauye, du kuwa da irin wajajen gayun da ta rayu,

Da kyar ta samu ta daura alwallah ta fito ta yi sallah,

Ba wani wanka da zata yi, bata zo da wannan rawar kan ba, sannan kafin a kawota sai da Ayyanta ta cika mata ciki dan haka tana gama sallah mikewa ta yi ta nemi wajen kwonciya ta nade saman lalausan lafiyayen bed din da bashi da wani tsayi sosai sai dai fadi,

Bata wani jira gannin ya zo inda take ba, domin kuwa koda Ayya ke mata jawabi ta cika da tambayar kanta daman miji zai tardota inda take ko me? Ita dai a aurenta na fari, bai taba zama saman bed dinta ba, bale a kai ga kwonciya, dan haka bata cire doguwar rigarta ba ta yi kwonciyarta da abinta, (kar ku manta, budurwa take, du wani rawar kai wani a cire kaya a sake wanka , a wani canza kaya sai kace uwar mata ko wata wace ta jima a lamarin , walahi a kiyaye, zaki iya sakawa mijin dar a zuciyarsa, koda kuwa a bazawara ya aureta idan ya tardo cas cas malan ka8 nake jira ba wani aji ba wani dan kunya ina dalili? Dan Allah ku mu dauki al.adunmu na malan bahaushe, amarya amarya ce, ta bari a tardota, kai koda ta san lamarin ta bari ya ja daren farkon nan, aman ba wai daga an tabaki ba kema har kin koya! Yin farin? Zuwan farin? Yan mata yaya dai?????????????????????????????????????),

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button