BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 71 to 80 (The End)

Tsaye yake kikam yana dubanta,

A hankali ta mike ta karasa dan kusa da shi kadan kafin ta duka ta gaishe shi,

Mutanen kam a kusa suke yau, domin gaisuwarma da kai aka amsa mata, dan haka ta mike da niyar shiga kicin ta hado masa abin karyawa kafin ya fita,

Hannunta ya riko da hannunsa na dama ya dawo da ita gabansa,

Hannayenta ya kamo baki daya ya kai wajen botiran rigarsa dake bude ba.a bala ba,

A hankali ta shiga bala masa tana duban kasa ,

Sai da ta bala masa har daidai wanda yake tsayarwa sannan ya zauna saman kujera ,

Cikin nutsuwa ta juya ta shiga daki ta dauko kumb,

Dawowa ta yi ta caje masa sumar kansa da kyau ta juya ta mayar ta dawo da niyar shiga kicin din dai,

Rikota ya yi , ya juyo da ita suna kallon juna, 

Kansa ya girgiza mata a hankali sannan ya mike ya dauki ky dinsa ya juyo ya mika mata wata dankareriyar samsung bai mata bayanin komai ba ya fice a gidan,

Ta jima tsaye cikin yannayin damuwa, me ke damunsa? Me ya bata masa rai haka?  

A hankali ta zauna bakin kujera tana duban hanyar da ya bi ya fita,

Ya Allah, shi ne abinda ta fada a fili, azumi yake ko kuwa cin abincin ne ba zai yi ba? Yaushe ya shigo gidan ma ni ban ji ba? 

Idannuwanta ta lumshe tana tuna maganar Ayya cewar wani lokacin zaka rasa gane kansa, zai dulmiyar da kai cikin tunanin waye shi? Dan haka ki yi ta hakuri Agaishat!

Wardugu, ka taimaka, ka bani hanyar da zan fahimce ka, ka taimaka ka ringa fara.a tare da ni ba sai ranar da ka yi niya ba, ka taimaka na zama wace ke gane du wani motsinka!

Wayar da ya ajiye mata ne ta shiga kuka ta hanyar salama da muryar mace zazaka tana karawa,

Sai da ta zabura dan ta zurfafa a tunani, kukan ya ankarar da ita dan haka da sauri ta dauko wayar tana duba sunnan wanda ke kiran, Anmou, waye Anmou????

Dagawa ta yi da salama sannan ta yi shiru,

Daga can kuwa sai da aka daga ta mika mata wayar tana dubanta da murmushi inda ita kuwa ta karba ta dan yi tsai , bata san da me zata fara ba, bata san me zata ce da ita ba, marabinta da ita tun kanta na cikin duhu, 

Dan haka a hankali ta ce’ Agaishat!

Tsai Agaishat ta yi, lokaci guda zuciyarta ta buga, 

Wayar ta cire ta kali numbobin sannan ta mayar a kunnenta, 

Muryar matar ta kara cewa ” Agaishat, kina ji na kuwa? Da yaren buzanci, da irin yanda take rrrrrrrr dinta sak irin na Agaishat din,

Da sauri Agaishat ta kai zaune muryarta na rawa ta ce” Anna? ANNA ke ce?

Anna ta lumshe idannuwanta ta amsa da ” Eh Agaishat,

Ai kuwa Agaishat ta fashe da kuka tana sauraron limfashin mahaifiyarta, 

A hankali ta ce” Anna, ina kike? Kun dawo ne? Kin warke Anna? Anna ina yan uwana? Ayya ina Ba Sofona? Annata kin kama sunana sak Annata kin kama sunnana,

Anna ta lumshe idannuwanta tana mai jin nauyin yar da ta haifa da cikinta, tabas ta saki rayuwar Agaishat dandaja, Allah ne kawai ya zama gatanta, ita yanzu haka bata wani hadiye maganar wai dan amininsa na sonta ya saketa, ita fa tsoro take ko bai sameta daidai bane ya saketa? Sakin yaro karami na kutse kutse kofa kofa waje waje dan neman gurin da zai ji sanyin rayuwa , neman abinda zai saka a bakinsa, a haka har ta rago ta kawowa baba sofo da kuma Anna, a haka ta iya tatalin dan kudin da ta samu ta kawo masu, a haka take zuwa ta rabu tana tsoron wani abin ya faru ko mahaifinta ya zo ya karta mata abin wulakanci dan kawai kalar fatarta na da duhu? Tausayin yar ne ya saka Anna kasa yin magana, dan haka Mariama dake tsaye tana ta so a bata wayar ta yi dabara ta karbi wayar ta bushe da dariya ta ce” Agaishat, Agaishat din Ba Sofo, Agaishat an girma?

Kafin ta amsawa Mariama Fatimata ta sabce wayar ta tsere kusa da Gaishata ta ce” Agaishat, Agaishat din Ayya Agaishat kina ina, ina ne gidanki?

Ai kuwa ta kwalalo ido cike da murna ta mike ra budi baki ta ce” Fatimata, Fatimata….

Sai kuma ta ji muryar Gaishata,

Ita kam bata taratsinsu, cikin nutsuwa ta ce” Agaishana,

Agaishat ta zauna tama rasa ina zata saka kanta dan dadi, muryarta nitse ta ce” Gaishata, Gaishata ina kuke ne? Gaishata Anna da sauki jikin nata? Kuna Timiya ne?

Gaishata ta girgiza kai tamkar tana gabanta ta ce” aa, muna garin da kike, mijinki ne ma ya kira jiya, Gukunni ya bashi number Anmou,

Agaishat ta sauke ajiyar zuciya ta ce” Gaishata kin haihu? Me kika samu?

Gaishata ta yi murmushi ta ce” du wannan tambayoyin adana abinki abinda zamu zo? Dama muma zumudin mu ji muryanki ne, aman Anna da sauki sosai alhamdulilah, nima kuma na haihu, Agaishat, lafiarki kalau dai ko? Ba abinda ke damunki gidanki ko? Agaishat amarya, yar Ayyanta aure sai da hakuri kin ji?

Agaishat ta yi murmushi tana ta sauraron muryar yayarsu ta fari, wani dadi take ji na ratsata har suka kashe kiran bayan sun tabatar mata da suna gari da zama , da sun huta zasu zo inda take,

Suna kashewa ta ji wani karfin gwuiwa ya zo mata, hakan ya sa ta zauna ta shiga game d wayar hankalinta kwonce,

Ta so kiran number Ayya, sai dai tunanin kar ta huce gona da iri ya saka ta bari idan ya zo sai ya kira mata kamar yanda ya saba , ta bata albishir,

Fararan hakoranta kawai take yawan washewa, 

Ta jima nan kafin ta mike ta nufi kicin dan shi ne kawai aikinta a gidan, 

Da yama bayan ta gama salar la.asar ta zauna da wayar da ta wuni game tana jujuya abinda ta rubuta da yarenta, inda ta samu da kyar ta gama message din kamar haka

                   *Salam*

          Ina yini Ya, ya aiki?

Zan kira ayya ne………………….na gode

           Agaishat

Numbersa da ta shanye tun tana gidan Ayya saboda tarin zero din dake ciki irin number nan mai shige da juna ne ta rubuta ta tura dan ita ta kagauta ta ji muryar Ayya ta fada mata sun yi waya da yan uwanta da Annarta, 

Wardugu dake tuki daga justice ya fito ransa a mugun bace sakamakon kiransa da Gukunni ya yi kan case din AISATA  matar Marahut, za.a salameta nan da wata biyu domin a lokacin da ake binciken asalin masu shigo da kwayar Niger ta bada hadin kai wajen fadin sunnayen wa.inda ke siyar mata baki daya, ta bada sunnayen wa.inda ta san suna siya a wajensu, sannan ta yarda bata baiwa sharia wahala ba ta hanyar gardana ko kin hada kai, hakan ya sa ta samu sasauci bayan kason da take yi an dankara mata tara ta millioyin kudi sannan wai za.a salameta! 

Hakan ne ya kunno shi, ido rufe ya fito ya dauki hanyar neman Marahut, nemansa yake ido rufe, shi ya san koda da haka, to fa da saka hannun Marahut ta hanyar gannin masu Niger din dan a salamo masa matarsa marar mutunci,

Wayar ce a hannunsa yake dannawa yana neman layin Marahut, aman amsar daya ce, number a kashe, layin ba zai shiga ba,

A haka message ya shigo, da yake orange ne yake kiran da shi sai ya yi tunanin ko zasu shaida masa number ta bude ne? 

Yana budewa ya ga message din,

Kallon number ya yi ya ga number wayarta ce da ya saka mata layinta cikin wayar nan,

Wai wardugu gatsal tamkar wani sa.anta? Sannn shi zata turowa message da umarni? Me take tunani? A me ta dauki kanta? Ba damuwarta bane da damuwarsa itama ko? Bata damu ba da halin da yake ciki ko?

Wani kuuuuu ya taka birkin motar kafin ya samu ya yi riboss da matsiyacin gudu ya dauki hanyar Aeroport din, ba zai hadiyi cewar, shi yana hana kansa komai idan ya ga koda yannayin fuskarta ya canza ne aman ita bata damu ba, da damuwarta kawai ta damu, zai warware mata rashin mutunci ne ta san cewa bafa shayinta ko taoronta yake ji ba! Zai je gidan ya…….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button