BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 71 to 80 (The End)

Murmushi Marahut yake tunda ya gama magana, ya dubi Wardugu ya ce”  kana son ta kennan?

Wardugu ya hade fuskarsa ya kawar da kansa irin ba shi ya kawo maganar ba, 

Marahut ya girgiza kai yana murmushi ya ce” mai hali, baya daina halinsa!

Honorable, kana nufin, ba zaka juya chaina a gobe ba sai an daura auren nan? Baka gudun rigimar Ayyansu? Ita yarinyar shin tana so? 

Gukunni ya ce” ina tunanin su za.aiwa alfarma! 

Marahut ya sada kansa,

Agogon hannunsa ya duba, sannan ya mike ya ce” karfe 2 ka zo da sadaki saifa millions arba.in. ka same mu a masalacin Elhaj Murtala ,

Yana gama fada ya mike ya shige ciki inda Gukunni baki bude ya mike ya bi bayansa yana fadan wani irin Millions 40 sai kace wata yar gwal ko wata budurwa?

Wardugu kam wani tsadaden murmushi ne ya saki daga zaunen da yake, yau ranar Asabar, 5 ga watan Jun , rana ta raba tsaka zai malaketa,

Jama.ar da suka halarci sallar azahar suka shaidi daurin auren, Daurin auren *WARDUGU MARAHUT* da *AGAISHAT ALGABITTT* bisa sadaki Millions 40 cefa ladakan, ,

Zamanin whatsup, zamanin android , nan da nan mutane suka fara watsa wannan lamari, inda ake yayatun buzuwa ce, suna yi har fiye da haka, Buzuwa ce General ya santale,

Nan da nan yan jaridu suka fara neman Wardugu cikin birnin Niamey,

Yan mata suka fara doka waya suna neman jin karin bayani,

Gidan redio ta saki labari,

Walyn,

Walyn dake kwonce tana shating ta ga kanwar kawarta ta dora saman status cewa” kaka kara kaka, wai da gaske ne ko da wasa? General ya bada sadakin buzuwa million 40 arma ta zama tasa? General wardugu ya watsa kuraye, abin son jinma ana cewa Black ce!….?

Ta karanta ya fi a girga , kafin kamar hadin baki, kira ne, mesage ne whatsup ne, facebook ne? Abu ya zama a lokaci daya ya shiga shigowa,

Bata gama tantancewa ba mahaifiyarya ta shigo dakin asibitin a fujajan ta ce………….

Ayya hankalinta ne ya gama tashi a lokacin da ta ji wannan bayani ta bakin Marahut da ya yi kiranta da bakuwar number ya yi mata murna da fada mata ya daurawa dansa aure da yarta ga sadakin nan zai zo ya kawo da kansa idan tana so ta saka a hana shi shiga!

Wardugu, 

A lokacin da ya ji eh lale Allah ya damka masa igiyoyin jan ragamar rayuwarta ya mike ya shiga motarsa da kayan jikinsa na tun jiya da bai samu ya tsaya bama bale ya canza,

Zama ya yi ya jinginar da kansa, idannuwansa ya lumshe sai kuma Walyn ta fado masa a rai, 

Wani tausayinta ne ya ji ya dirar masa, dan ya sani ne Allah kawai zai tsayar da ita kan saka kanta a uku, 

Motarsa ya tayar da kansa ya harbata bakin titi da gudun balaki……

Bai zame ko.ina ba sai clinik din da Walyn take,

A nitse ya kashe motar ya zare kys din ya fice daga ciki,

Taku yake cikin nutsuwa da ingarma, ba zaka taba fahimtar halin da yake ciki ba har ya tura kofar ya bude,

Ido hudu suka yi shi da ita, tana zaune ta ziro kafafuwanta kasa, ta ja rigar clinik din can saman cinyoyinta, kanta bude gashin kanta ba ribom, ta tsurawa waje daya ido domin jinta da ganninta ne suka fauke na dan lokaci,

A hankali ya karasa kusan gadon da take zaune ya cire takalmin kafarsa ya dan saci duban mahaifiyarta ya ga tanai masa wani kallon da ba zai gane na kyama ne? Na tsana ne? Ko na deception bane! 

Hannunta ya kamo yana dubanta,

Murya cinkushe ya ce” Walyn,

Idannuwanta kawai binsa suke da kallo, Namiji? Bata taba sannin kalmar da zata yi ajalinta bane sai yau! Namiji Namijinma wanda ta fi aminta da shi, Kishiya? Kishiya Wardugu ya yi mata? Ita Walyn? Me ta rage shi? Menene? Ita ya wulakanta a idon duniya? Ita ya wulakanta a dangi? Yanzu uban wa zata yiwa daga kai da jiji da kai a gari? An taka dokar al.adunta ma, an tarwatsa takamarta ma, an ci amanarta, dan me? Me ya yi zafi? Me na rasa? Ban taba haihuwa ba….hasalima ban bar kwan ya zama gudaji ba na watsa shi, du domin ka???

Muryarta na rawa ta ce” Wardugu, dandan me? Sex ne ko? Dan wannan ka tozarta ni? Nawa bai isheka ba???

Wardugu ya dane , ya ki nuna komai ya rikota jikinsa ya ce” aa, ba wulakanta ki na yi ba, kuma ba ramuwae gaya na yi maki ba Walyn, ba dan sex na kara aure ba, ina so ki kwontar da hankalinki, ki kwontar min da nawa, idan har kika yi haka Walyn, ina mai tabatar maki da zan canza, zan dawo maki yanda kike so Walyn, idan har kika yi hakuri da wannan jarabawa…zaki ci ribarta, ki yi hakuri, ina baki hakuri ne ba dan na aikata haramun ba, aa , sai dan kema matata ce, ina son ki, ba cusa min ke aka yi ba, Walyn haka itama ba wanda ya yi min dole, ki sani aure lokaci ne, kuma rai ne da shi, ki dauka lokacin yin ne ya yi na yi, kar ki yarda zugar mutane ko na shedan ya yi tasiri a kanki, dan Allah matata ki jure wannan karon, bana so mu raba hali, ki jure walyna……

Ya karashe yana mai shafa gashin kanta,

Wani irin kuka ne ta fashe da shi mai karfi da rudu,

Gaba daya ta saka hannunta saman kanta tana ihu,

Da sauri ya hade bakinsa da nata dan rufe bali ihun da take ……… aman ina cizo ta gantsara masa kafin take kokarin kwacewa daga rikon da ya yi mata tana jifansa da wani kallo irin na bakon halita mayaudari ko wani azalumi,

Aniya wartar du abinda ya zo hanyarta ta yi tana dokawa da kasa, ihu take wanda ya fara tsoratar da dakunnan kusa da ita sannan likitoci suka fara yowa dakin da gudu dan ko tunanin mutuwa aka yi wani marar imanin yake kuka irin haka!

Hannunsa na dama ya saka ya tokare habarsa yana kallon yanda mamanta ke binta tana kiran sunnanta aman cikin ikon Allah dan karamin frij din dake dakin kansa sai da tajanyo ta kifar tana ihun yau sai dai a yi daya, ko ita ko Agaishat!

Mikewa ya yi ya damki hannunta ya jata,

Kiiiiiiiiiiii inda du aka rufa masu baya wasu na tambayar lafia ? Cike da tsoro wasu na kallon ikon Allah da yiwa Walyn kallon wayo Mahaukaciya ce da alama?

Motar ya bude gidan baya ya turata ciki sannan ya koma gaba ya shiga ya rufe ya yiwa motar ky sannan ya tayar ya harba ba tare da ya tsaya daukan mamanta ba, dan ya sani ne, ba zata taba tausarta kan lamarin ba, dan shi kadai ya san abubuwan da ya tsinta uwar na fada a lokacin da ya karaso asibitin,

Hauka fa tuburam, Walyn fa ta zauce, magangannu take saki tare da fadin Warsugu macuci ne, ya cuceta a haka har suka karasa gidan su,

Wannan karron daukanta ya yi cimak ya nufi falonsa da ita, yana budewa ya direta cikin falon ya rufe fallon ya barta nan ya nufi cikin dakinsa ya shige bayi,

Wasa sabon girki, wato dabi.un wasu tubawan idan akaiwa kishiya , shi Walyn ta aro, inda ta aniya dira tana fasa du wani abin fasawa na falon Wardugu, ciki harda katuwar plasma din dake mamaye da bango, ta tarwatsa table din diner da na tsakiyar falon, ta dauko wuka ta yayaga wannan tanfatsetsiyar kujera ta alfarma, ta kawo ruwa ta makawa moket din ta aniya dira tana yagawa,

Ta kama labulayen bangon du ta yaga shegu, ta dira dakin bakinsa ta aniya yaye jibgegen bargon dake malale saman katifar dake kan bed din, ta saka wukar ta yayaga katifar, ta kama kyarta jikin gadon da sif din da komai na dakin, ta fasa madubin dake kawaye a dakin, ta dauki iphone dinsa kwara uku ta tanfatsa da kasa, 

Aiki take na gangan, aiki na motsa mutun domin koda Wardugu mai kudi ne an masa asara ta kirki, gashi bai jima da canza komai na gidan ba,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button