BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 71 to 80 (The End)

A hankali ta dago dubanta kamar shi ne kofar ta dubi kofar kafin a sanyaye ta ce” Me yake nufi??

Wardugu ya saki murmushi mai dan sauti, ya ce” ki yarda da amon kuryana, ki yarda da yannayina, ki bude min , ki zo gareni, ki sauke min fushina, ki ririta ni, ki bani na tsotsa (????????????‍♀️), ki bani na samu nutsuwa, Agaishat , ki karanci menene Orronur a tare da ni, ki bani amsa da kanki,

Wani irin yamyamyam ta ji tun daga yatsar kafarta har tsakiyar kanta, idannuwanta ta lumshe da karfin gaske dan kuwa har jikinta sai da ya amsa sannan ya dauka,

Wayo Allah, shi ne abinda ta fada a kasan makoshinta, domin kuwa a yanda ya yi maganar, ya karashe tamkar yaron dake neman mamansa ido rufe,

Hannunta na dan rawa rawa ta mike ta kai hannunta wajen budewar ta dana inda ta yi kundumbala da tsoron haduwar da shi, ta tataro jarumta ta bude kofar (Agaishat????, idanfa ya yi haka ne dan ya damke ki? Baki dadara da marin ba ko? Wayo Agaishat????)

Budewa ta yi baki daya kofar ta bude, sai gata bayane gabansa, gaba dayanta yar ficik a gabansa, 

Taku daya ya yi ya karasa gabanta, hannunsa ya mika ya……………..

???????????????? *BAK’A CE* ????????????????

                            Na

                     *SAJIDA*

                          8️⃣5️⃣

*KUTKALE* (PRISON)

*AURE YAKIN MATA NE*

*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*

daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA*  in sha Allah,

……..kar ku bari a baku labari…..

*ASALAMU ALAIKUM FANS, BAK’A DAI BA NA SIYARWA BANE, DU WANDA YA KARBI KUDINKU DAN YA SIYAR MAKU YA CUCE KU NE, NI BAN RUBUTA BAK’A CE DAN NA SIYAR DA SHI BA*

A hankali ya mika hannunsa ya janyota jikinsa,

Bata ki ba ta kwonta a jikinsa luf,

Cikin nutsuwa ya lalubi lebenta , bai tsaya dogon turanci ba ya shiga aika mata kis cikin sauri sauri dan kuwa a matukar matse yake da ita,

Kokarin kaita kasa yake nan, ta samu a hankali ta kai bakinta daidai kunnensa ta ce” Dati jikina Yah, ka bari na yi wanka daga kicin na fito, karnin nama nake,

Idannuwansa ya lumshe domin ji yayi tamkar tana yi masa susa a kunnen dan kuwa a hankali ta yi maganar ga kuma lebunanta dake gugar kunnen nasa,

Tsai ya yi, kafin ya lumshe idannuwansa, 

A hankali ya samu ya janyota jikinsa sosai,

Hannunsa yake bi dukan jikinta yana neman hanyar cire rigar kafin ya iya fuzgo maganar bakinsa ta hanyar cewa” kin fi armashi a haka………

Da gudu na baro dakin, domin kuwa Agaishat ta zagine tana baiwa mijinta goyon baya dan raya sunna ,

Sun jima suna maida numfashi bayan komai ya lafa, a hankali yake shafa gashin kanta, kafin ya ce” kin san me?

Agaishat ta girgiza kanta tana lumshe idannuwanta, dan kuwa ya yi kokarin binta a laluma , sai tarin gajiyar da take ji dai na rashin sabo a jikinta,

Wardugu ya ce”  Oroonur, na nufin *RAINA* 

Da sauri ta dago da dubanta daga kwoncen da ta yi lamo a jikinsa, 

Ido ta tsura masa tana dubansa, 

Hakan ya sa ya hade fuska shima yana dubanta,

Murmushi ta saki kafin ta mike ta shige jikinsa gaba dayanta, a hankali ta ce” ni? Ni ce Ranka?

Wardugu ya rungumeta da dan karfi a jikinsa, hakan ya sa ta yi lamo, still ta kuma cewa” *KANA SO NA?*

Wardugu ya yi murmushi bai bata amsa ba, 

Can har ta cire rai da jin amsarsa ya ce” me kike so na maki a duniya na kare min mutuncin kanki da kika yi? 

Agaishat ta dago da kanta tana dubansa, ita kuwa me ya rageta da shi? In mutunci ne ya siya mata, in kaunar ce ya kilaceta a gidansa, ba yunwa, ba kishirwa, ba rashin mutunci, ba ruwansa da kauyancinta, kuma yanzu ya gama shaida mata ita din Ransa ce, ita kuwa me zata nema bayan shi nashi jin dadin? Kai walahi ta dauki aniyar faranta masa mudin ranta! 

A hankali ta dora kanta saman kirjinsa, hannunta dake kusan keyarsa ta dan karawa tsayi ta duko da kansa wajen fuskarta,

Kanta ta daga ta kai lebenta kusan bakinsa,

Yana tsaye tamkar ya kurma ihu dan dadi yana jiran ya ga ikon Allah me zata yi,? 

Ba zato ba tsamani ya ga ta ciro harshenta a hankali, kuma idonta cikin nasa ta kawo harshen daidai lebensa, idannuwanta ta lumshe kafin ta lashi lebensa na kasa,

Tana lashewar ta bude idannuwanta sanadiyar kara matseta da ya yi a jikinsa, idannuwansa ta gani a lumshe, 

Murmushi ta saki sannan a hankali ta ce” burina shi ne, ka yi hakuri, ka zama mai hakuri, ka zama mai yafiya, Yayana da ciwo, da mugun ciwo, aman a yau idan ka dubi wani abinda ya gani a rayuwa naka mai sauki ne, ka duba ka ga yanda kake cikin rufin asirin Allah,  ALlah ya baka rai kyauta, ya baka lafia kyauta, ya baka iyaye kyauta, ya bata yan uwa kyauta, ya baka mata masu kaunarka domin Allah kyauta, ya baka arziki ta hanyar halal kyauta, ga kyau, 

Ta yi tsai ta dago tana duban idannuwansa, ta yi wal da idannuwanta ta ce” Mijina ga jarumta, ga farin jini , ga karfi, duka ba dan karfinka ko dan dabararka ba,

Shiru ta yi ta kuma dagowa tana duban yannayinsa, gani ta yi kawai ya tsura mata ido yana sauraronta,

A hankali ta dan zame kadan tana dubansa ta ce” duka bai tambayeka komai ba sai ka yi masa bauta, ka yiwa iyayenka biyaya, sannan ya ce *ALJANARKA TANA KARKASHIN KAFAR IYAYENKA* , 

Ka san me?

Dubanta yake bai amsata ba, bai kuma nuna bacin ransa ba, kai hasalima ba zaka fahimci wani yannayi yake ciki ba, yana dai kallonta ne,

Ji ta yi ta fara jin tsoron yannayinsa, dan haka a hankali ta yi shiru ta mike dan daukar rigarta zata saka,

Hannunta ya riko, ya kawota bakin bed din,

Maimakun su hau bed sin sai ta ga ya zauna da ita nan kasa ya sakata tsakankannin kafafuwansa ya dora bayanta saman jirginsa sanna ya saka hannayenta cikin nasa, a hankali ya ce” *sai kin fada*

Gabanta sai da ya wulwula ya fadi, anya kuwa zata iya ci gaba da magana a haka ? A hannunsa fa take dumu dumu, idan ta yi garaje daga haka yana iya juyar da kanta zuwa dubansa wato ya karya kan, 

Yawu ta hadiye ta ci gaba da fadin” ni ba zan yi wasa da aljanata ba, du rintsi, du wuya, zan bi aljanata da gudu, a kanka sujada ne kawai ba zan maka ba shima dan haramun ne, zan tarbi mai tarbanka, zan banki mai yi maka mugun kallo, zan harbi mai zundenka, somin kai din uban gidana ne, mijina ne, mai take da aljanata ne,

Wani irin gingirigin kansa ya yi, wollah jinsa ya yo ya cika dakin dan girma, wani yuuuu ya ji gaba daya jikinsa, mace bata taba fada masa haka ba, macen ma Orronur, yarinya karama, yarinyar da ta yi girman daji, dama ta iya dadadan zance haka? Yaushe ta koya? Yaushe ta san tace da shi mijinta, yana jin dadi da gannin girman kalmar bale da ta fito daga bakinta, wai wai dadi, a hankali ya lumshe idannuwansa sannan ya kara rike hannayenta, muryarsa kasa kasa ya ce” Orronur, 

Kina so na?

Shiru ta yi, tana mai kara tunanin hikinkimun da zata bi da shi, 

Sai da ta kwontar da kanta saman kirjinsa ta yi lamo, sannan ta ce” *ARREKI DI IMANINE DU IDINETTE* (U.R TH MAN OF MY LIFE……TU EST LHOMME DE MA VIE),

sannan ta rike hannunsa ta kawo daidai zuciyarta ta dora, a hankali ta ci gaba da fadin” sun ce, daga na fara so, idan na ga abin son zuciyata zata fara bugawa, za.ina son gannin abin, za.ina son kasancewa da shi koda yaushe, 

Tabas a kanka na san wannan abubuwan, 

Gaba daya ya juyota tana facing dinsa, hannayensa dake rawa rawa ya saka ya dago fuskar tata daidai tasa yana kallonta, A hankali ya ce” fada, fada min , na roke ki,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button