BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 71 to 80 (The End)

Wardugu ya amsa Ayya a takaice yana mai kunshe dariyarsa inda ya ce” eh,

Ayya ta dubi wayar ta mayar a kunnenta ta ce” sakon kuwa masha Allah, an gode , Allah ya saka da alkhairi,

Wardugu ya kara gimtse dariyarsa ya ce” amen, amen,

Ayya ta dane zuciyarta dai ta ce” harda su amale kai aman kosashe ne,

Wardugu ya ce” eh haka fa,

Ayya ta mike tsaye ta ce” Wardugu dan ubanka ina y’ata? Tana ina? Walahi maza maza a kawo min yarinya a yi mata kitso da kunshi a gabana, lahauli, Wardugu bana jin motsinta, tana ina me ka yi mata?

Ai kuwa wardugu ya saki murmushi kafin ya ce” haba yanzu na gane Ayyana, meye za.ana bin wani layi da ni kuma? Lafiarta kalau,

Ayya ta ce” aman wannan kyautar ai da manufarta ko? Gashi yaran da suka kawo ni basu ce min komai ba, ta yaya hakan zai faru?

Wardugu ya girgiza kai yana murmushi kafin ya ce” eh manufar dai da kike tunani Ayyana haka ne.

Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, ai Ayya ita ta datse kiran dan walahi kunya ce ta kamata, sintiri take tana zancen zuci, ba mai hanata wankawa Agaishat mari kan shiru da ta yi mata ta yi ta shiryata tamkar wace ta san hanyar, 

Ba mai rabata da Wardugu idan ya jiwa yar amanarta , 

Zama ta yi tana duban Alhinayett da ta rage, domin ta salami sauran mutanen, ta ce” kin san ai ba.ai mata kitso ma sai yau ko Alhi? 

Alhinayett ta amsa Ayya tana dubanta, kafin Ayya ta ci gaba da fadin” to bara ki ji, zuwa zaki yi ki dauki Melina daga saloon mun gama magana da ita ki kaita gidan Agaishat, idan kin je ki yi min vidio call na ganta, idan wani abu bai gamshe ni ba, zaku ganni a kanku, kun jima baku ce na dauko y’ata ba! 

Ai kuwa Alhinayett ta maida hankali, domin yannayin Ayya ba wasa,

Ita kanta sai da ta je ta gane ba kyautar tarin kauna bane ya yi kata, kyautar cika al.adunmu ne, kuma ya yi haka dan a san da eh ruf ta je,

Sosai ta tausaya mata, ita da kanta kunyarsa ta ringa ji dan a gabanta ya tsare Agaishat da abinci sai da ta ci ya shirya ya fice aiki bayan ya jadada a bar waya a kusa, inda ya wuni yana aikin kira ya ji ya take, me take,

Daga nan ma wajen Ayya ya fice inda suka sha daru, ta dage tana fada, aman ta ki fadin asalin fadan, ita dai fadi take du wanda ya takura yarinyarta zata je ta daukota ne!…..

Kwonci tashi, zaman Wardugu da Agaishat zama ne na amana, 

A hankali take binsa, shima a hankalin yake binta,

Ya kusanta kansa da ita, ya mayar da ita abokiyarsa, ya saka shakuwa ta kirki tsakaninsu, inda ta sakankance take afkawa cikin kogin soyayarsa aman har yau ba wanda ya fadawa dan uwansa kalmar so.

Sau daya ta yi masa maganar Walyn, maimakun ya fahimceta sai cewa ya yi” Walyn dai matata ce, kika san ko idan na fita daga inda kike wajenta nake tarewa? Ba ruwanki da rashin raba kwanakin ku, ko so kike ki nuna min na isheki dan bakya so na?

Shiru ta yi ta shiga goge masa zufar motsa jikin da ya yi, inda ta mika masa tea mai zafi ta shiga tatare wajen,

Kamar yau, ya kama wajen sati uku da aurensu, kuma har yau ya ki ya bata wayarta da ta gane tana hannunsa,

Zaune yake yana kallon France 24, ana ta hasko labarun duniya,

A nitse ta zauna kujerar dake facing din inda yake zaune, 

Kallon yake aman yana cirewa yana dubanta, sai kuma ya maida dubansa kan tvn,

Kafarta take dan karkadawa a hankali, ta hade cikin doguwar atamfa, rabonta da wardugu ya kai mata hari tun na daren farkonsu,

Ya kasance komai dare idan ta yi baci zai janye ya kwana daban daban da ita, ta sha kama shi yana dibgar lemun tsami, ta sani, ta sha azaba ya ba gobe, qman kuma ta fara shiga damuwa, ta dai san mijinta namiji ne lafiyaye, kuma ta san ba ita daya ne da shi ba, idan wajen matarsa yake zuwa ita hoto ce? Aa fa, ba zata so ta zama hoto a fadar Wardugu ba, 

Zaman kafar ta canza tana kadawa, dan haka a hankalce ya ce” menene?

Agaishat ta zumburo bakinta ta ce” wai me sunana ne?

Wardugu ya tsura mata ido, a ransa ya ayanna yau kuma fitina take ji,

Murmushi ya yi ya tashi ya koma kusa da ita ya zauna, habarsa ya dafe yana duban kwayar idannunta,

A hankali ya ce  sunnanki…Orronur,

Agaishat ta zumburo bakinta ta dube shi da kyau ta ce” menene ma.anar Orronur,

Tsareta ya yi da ido, zai bata amsa kira ya shigo wayarsa dan haka ya daga yana dubanta, 

Walyn…ya fadi sunnan a sanyaye,

Walyn ta amsa shi da Wardugu, dan Allah ka lamuncen ganninka, ka bani damar ganninka, na tuba, ka tuna fa, hakina dake kanka idan har ka tauye min Allah ba zai barka ba, ba sakar min kudi bane kawai hakina dake kanka,

Wardugu ya lumshe idannuwansa kafin ya bude yana kallon yannayin Agaishat ya ce” kina ina ne?

Walyn ta amsa shi da tana gidansu na da,

Wardugu ya saki murmushi a zuciyarsa dan kuwa zai so ya ga yannayin da Agaishat zata nuna, dan haka ya ce” ki shirya min tarba, zan so shinfidarki ta yi kamshi, gani nan zuwa,

Kamar an doka mata ice a kanta ta ji, a zaunen da take ta lumshe idannuwanta tana kiran sunnan Allah, domin kuwa juwa ce take ji daga zaune,

Bata tashi jin kamar an gaura mata mari ba sai da ya mana mata kiss, ya mike yana gyara belt din wandonsa ya yi mata wani murmushin shegantaka sannan ya juya ba tare da ya ce da ita zai fita ba , ko zai je wani gurin ba, ya fice a gidan inda ta gane haka ta tvn bangon dake nuna mai shigowa ko mai fita daga gidan dan ba.a jin dirar motoci in dai dakunnan a rufe,

A hankali ta silale saman kujerar ta rushe da kuka dan zuciyarta take ji zata balo kirjinta ta fito, 

Dan me ba zan zama mace mai inci irin na kowa ba?

Zaman kwana ashirin da daya da na yi da kai, zaka yi min wasa tamkar wata baby, na san bana yawan neman zama inda kake ba suturar kirki a jikina, aman irin idan ta kama ka shigo na fito a wanka zaka yi gagawar juyawa ka bara min dakin, wari nake? Ko kaima kana kyamar *BAK’A CE?*, ni na san kana zaune da ni ne dan girman kaunar da kake yiwa mahaifiyarka, aman kuma kaunar ba zata sa ka nunan nima mace bace? Ko na zurmi da yawa ta hanyar bin nasihohi ta hanyar kyautata maka? Na san matarka ce, ta fi ni fada a wajenka, aman idan ka yi niyar raba mana kwana ne ka hada mu mana ka yi kamar yanda kowace mace ke samu? Ba ko salama ko? Ni ko? Ba komai Wardugu, nima zan kama kaina, na farka daga yaudarar kaina da nake cewar so ne, aa *Kyautatawa ce*, 

Nima zan kyautata maka!

Wardugu kam na fita sai da ya gama shawaginsa a gari kafin ya je gidan,

A bangarensa ya sameta, an gyagyara dakin ba laifi, sannan dai cikin shigarta ta kananun kaya,

Ga mamakinsa bai yi wani zumudin shigarta ba kamar kulun, saima zama da ya yi yana son kwadaitawa kansa ita dan fita haki, da kuma samun nutsuwar kansa, dan ba karamin takure yake ba dagawa Agaishat kafa da yake, yana matukar tausaya mata , yana so ta karasa yarda da shi, ta idasa sakewa da shi, kafin a hankali ya kara dirmiyar da ita ruwa ta hanyar da ya dace, so yake ta fada soyayarsa komai kankantarta, yana so ta so shi koda da wasa ne, shi dai  ya samu soyayarta kamar yanda yake ciki, 

Sai dai yarinyar ya lura tana zaune da shi ne kawai dan biyaya, domin sha nawa zai samu kiran yan mata a gabanta, maimakun ta nuna bacin ranta irin na Walyn, saima ta shiga sabgar gabanta, kennan dai bata son sa bale ra yi kishinsa ko? Dan me? Dan me jarabawarsa ta diro ta nan? Ya Allah……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button