BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 71 to 80 (The End)

Fitowa ya yi daga wanka daga shi sai tawul yana mai jinsa yana yawo a sama, sai dai me, turus ya ja ya tsaya yana hangen bayanta yanda ta dukufa take yaga bargon da ta yaye stilll tana ihun kuka,

Habarsa ya dafe da hannunsa yana bin dakin da kallo, kafin ya maida dubansa kanta, 

Ikon Allah, shi ne abinda ya fada a ransa, 

Zagayeta ya yi ya bude sif din yana bin inda akaiwa sabon zane da kallo , ya janyo boxer dinsa da wasu kayansa na kanfanin Gudd ya ciro yana ajiyewa nan jikin bed din,

Ai kuwa ta ankara da shi ta nufo kayan da ya ciro ta dauka ta saka wukar ta yaga,

Bakinsa ya rike ya ce” Walyn da tsada fa??

Bata bashi amsa ba sai harararsa da ta yi ta ce” walahi sai ka saketa, walahi ni na san dan ka rama abinda na yi maka ne, baka yafe mini zubar da cikin da na yi bane shi ne zaka hukunta ni ta hanyar yi mini kishiya, walahi sai ka saketa ko daga ni har kai mu bakunci lahira,

Murmushi ya yi kawai ya girgiza kansa ya kuma fitar da wasu, aman yanzu yana cirowa yana sakawa ne bai ajiye ba dan kar a maimaita abinda aka yi,

Juyawa ya yi bayan ya kile sif din dan akoy kayansa masu mahinmancin da ba zai so ta wulakanta ba ,

Da gudu ta biyo shi tana faman yi masa tijira inda ta nufe shi da wukar hannunta ta nufi cikinsa da ita ido rufe tana alwashin sai ta halaka shi tunda ya yi mata kishiya,

Da sauri ya goce ya tara hannunsa, nan ta yanki gefen hannunsa wajen kaurin hannun nasa da wukar ta yi masa baban yankan da jini ya bale ,

Idonsa ya rintse yana jin zuciyarsa na fara yaba gayatar balakin da take masa, 

Kara nufo shi ta yi tana ta balaki da tubanci wanda zagi ne kawai bata saka ba aman har Ayya sai da ta dorawa laifin da bata ji ba bata gani ba tana fadin daman idan sarakuwa ta tsane ka ai ba ta inda ba za.a biyo maka ba,

Hannun mai wukar ya rike inda ya matse shi da dan karfin da ya saka ta kwala kara ta saki wukar,

Janyota ya yi inda yake tsaye ya fala mata mari ya kara mata, 

Bai kuma yi mata magana ba sai janta da ya yi waje  kujerar da ta yiwa ta.asa ya kama rigar asibitin dake jikinta ya yagata , toh daman rigar ba wani kwari ba sannan botira ne jikinta,

Bata gama gane ina ya dosa ba sai da ta ga daga rigar bai zame ko.ina ba sai wajen da baya faduwa ya saka hannunsa shima ya yage shi ya…….

Tumurmusarta yake da dukan karfin da Allah ya bashi ta wannan fannin, 

Dukan da ya fi duka zafi ne yake bata ido rufe ko zai samu ta rufe masa bakinta ta daina magana kan mahaifiyarsa tamkar wata tsararta! 

Shin wacece ita? A darajar masu daraja da Allah ya halita a duniya musulmai wacece ita da ba za.a yi mata kishiya ta yi hakuri ba? 

Wacece ita da zata ringa budar baki tana jifan halitar da Allah ya halita ba tare da ya ce dan ya yi mata kalar fata haka laifi ta yi masa ba?

Wacece ita da zata ringa zagin kadararsa? Domin kuwa shi ya san Allah ne ya kama shi a kan Agaishat, ya ba zata bar shi ya ji da irin rigimar da yake hangowa kansa ba a tare da mahifiyarsa da kuma yarinyar da bai san meye a zuciyarta game da shi ba? Ya ba zata tarbe shi, ta kula shi, ta taya shi a wannan lokacin da yake cikin garari yana sakin magangannun da sai ya yi wata bai yi masu tsayi irin haka ba ? Ya bata lura da ya so su yi masalaha su fahimci juna, ya so ya rarasheta irin na kowace mace mai inci mai fada a wajen miji idan akai mata kishiya ba? Shin Walyn kwakwaluwarta a tabe take ko tsabar iskanci ne da samun guri? Shin ya fara sakin fuskar da har raini mai karfi ya kara yin tasiri tsakaninsa da Walyn da sauran mutanen?

Ya ga Alama ba Walyn ba, harta da ita Agaishat din idan ya yi wasa za.a samu matsala……

Ya Walyn zata manta ainahin Waye Shi a doron kasa? Ya zata manta shi ne asalin batube gaba da baya cikake mai jininsu dake yawo a jikinsa har ta nuna masa wuka?

Shin ta manta yaya suke da wuka ne?

Shi zata tarba da balaki hauka , da tashin hankali batan ta san adireshinsa ne complet??????

           Morning

            Idona ya fara ciwo, ni kam sai na huta????????????

???????????????? *BAK’A CE* ????????????????

                            Na

                     *SAJIDA*

                          7️⃣8️⃣

*KUTKALE* (PRISON)

*AURE YAKIN MATA NE*

*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*

daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA*  in sha Allah,

……..kar ku bari a baku labari…..

Ups sauran kadan dai????????????????????????????????????????????????????????

Dakinta ta tura ta shiga , jiki ba karfi ko kadan,

Wajen salaya ta hangota inda itama ta dago da kanta tana dubanta, salar la.asar ta gabatar kennan, ta zauna tana adu.a,

A hankali ta karasa inda ita kuwa take faman mikewa tana duban Yannayinta, tamkar tana cike da damuwa,

Mayar da ita ta yi saman salayar ta zaunar da ita sannan itama ta zauna ta rakubu da bangon dakin ,

Kanta ta daga sama tana kallon shilling, 

A nitse Agaishat ta ce” Ayyana , lafia??

Shiru Ayya ta yi tana tunanin ta inda zata fara, can ta ce” ina jin kinyar Allah, ina jin kunyar amana , ina jin kunyar soyayar da kike min tamkar uwa,

Da sauri Agaishat ta dubeta da kyau kafin ta matsa kusa da ita sosai ta ce” Subahannalah, 

Ayya ta dawo da dubanta wajen Agaishat ta ce” na yi wasa da ke sosai, a yanzu ban san wani hali nake ciki ba,

Agaishat ta dora kanta gefen kafadar Ayya tana fan girgiza kanta, dan ita bata san me zata ce ba, a hankali ta ce” Ayyana, baki yi min komai ba, ba abinda kikai min, me ke damun ki?

Ayya ta ce” Agaishat, na farko haka ya zo ya shige tamkar wasan yara, yanzuma gashi an kara maki wani mai hargitsi, 

 Agaisha, ni na haife shi da cikina, da aurwn soyaya, aman ni zan fadi dole matarsa ta yi hakurin zama da shi , shi din  mai rigima ne, shi din mai taryan rigima ne,

Tun yana yaro nake fama da hakan, gashi abu guda dai shi din bai iya son abu ba,

Agaishana, basu saurare ni ba, basu ysaya sun ji me nake da shi na cewa ba, ko ke abinda ke cikin ranki mahaifinsa ya yi jagorar daurin aurensa da ke, 

Da sauri ta dago ta dubi Ayya, idannuwanta du ta ruko da mamaki da tsoro, aure? Da da Wardugu? 

Ayya ta kawar da kanta daga dubanta ta ci gaba da fadin” Marahut, jira yake, hanyar da zamu raba abin kallo yake nema, bai jima da fita a gidannan ba, a gadarance ya kawo min jakarnan ta sadakinki ce, tabas gaskiya ne an daura aurenki da Wardugu bisa sadaki Cefa Millions Arba.in,

Kanta sai da ya sara dan dukan da maganar ta yi mata, a hankali ta silale ta dora kanta saman cinyar Ayya kafin take kawo hannunta na dama ta rukunkume cinyoyin Ayya,

Ji take zuciyarya zata balli gangar jikinta ta fito dan tsoro , shikenan, ta faru ta kare, 

A hankali Ayya ke shafa kanta ta ci gaba da magana kamar haka” ba zan maki tilas ba Agaishat, duda a yarena namiji nada cikenken iko da matarsa, domin ko ni mahaifiyarsa ban isa na takura masa da lamarin matarsa ba, kin ga a yau a yanzu idan wardugu ya yi niyar wulakanci sai ya zo ya dauke ki ya tafi da ke tafia ta har abada ba wanda ya isa ya tanka shi, musuluncima ya bashi iko a kanki a yanzu, sai dai na sani ne, yana da dar a kaina, ko a al.adunmu na tubawa yana daga abubuwa da yawa idan dai ya shafe ni, idan kika ce ba zaki zauna da shi, in sha Allah zan ci karfinsa,

Sai dai zan so ki nutsu, ki fara duba na rayuwarki kanta, yarinya ce ke karama, idan ba muguwar kadara ba , ba zan so a ce an kama yi maki saki saki kina shiga hannun maza kina fita tamkar kwalo,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button