BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 71 to 80 (The End)

haka har ya karasa da ita asibiti, 

Sai da aka karbeta aka shiga da ita yana ta sintiri kafin ya tuna da Ayya, gashi ya fito ba waya ko daya a jikinsa, gashi mutane sun fara ankara da shi ne a wajen,

Waje ya samu ya zauna ya yi bakam yana kallon waje guda, adu.a kawai yake a zuciyarsa wace bai san bama me da me yake ja,

Yaren gidansa ne suka shaidawa Ayya abinda ke faruwa, dan haka bata tsaya wata wata ba ta je gidan ta dauki abinda zata dauka sannan ta bi bayansu asibitin da take awo dan ta san can za.a kaita haihuwa, asibitinsu ta sojoji

Zaune kawai ta tarar da shi, hakan ya sa ta zauna tana tambayarsa yaya dai??

Dago da kansa ya yi a raunane yana dubanta ya ce” Ayya, wai wai cewa ta yi mutuwa zata yi, Ayya idan ta mutu ni kuwa na yi yaya?

Ayya ta girgiza kanta tana dubansa ta ce” Allah baya barin wani dan wani ya ji dadi Wardugu, aman  kuma zafin ciwo ne ka ji? Mu yi mata adu.a in sha Allah zata sauka lafia,

Shiru ya yi yana gyada kansa, shi kam ko ciwon kai take sai ya jishi bashi da wani anfani, wollah dan ba makoki bane, da ko yatsarta ke ciwo sai ya yi kuka, dan sosai yake jin abin a ransa, bale yanzu,

Agaishat kam ta sha wahala ba laifi, nakudar awa shida ta yi, da kyar Allah ya sauketa lafia ta haifo baby boy dinta, bashi da girma sosai domin cikinta bai yi mugun girma ba,

Zo ka ga murna wajen Wardugu Ayya da duk wani sojan da kafarsa ke cikin asibitin,

Nan da nan wajen ke ta daukan harama duda dare ne sosai, haka aka yi kiran su Gukunni aka fada masu, inda Anna ta shiga murna a cikin ranta tana tausaya yar tata da adu.ar Allah ya raya,

Wardugu kam dariya yake hakoransa waje, mutane sai murna suke taya shi, inda ya yi kiran Walyn dake baci ya sanar mata yana mai farin ciki,

Bai tsaya ya ji amsarta ba ya kashe yana ta doka kira,

Walyn kam daga saman bed din ta doko kasa, idannuwanta du ta zazaro tana kallon dakin, me me ta haihu? Ciki ne da ita daman? Daman ciki ne da ita? Yaushe har cikin ya girma? Yaushema aka yi auren? Ni ina zaune ban yi cikin ba? To walahi sai na je indiar nan nima sai na haihu!

Haka ta yi ta sambatunta wanda sam bata san halin hasadar dake cin zuciyarta ba, a wajenta normal ne, itama muradinta take fada …..

Biki ne aka yi a tsare, bikin da ya hada dangin Tubawa da na Buzaye,

Du girman gidan nan sai da ya cika ya batse,

Walyn ta sha wata danyar shada wace takanas ta tada mutun aka je dubai aka kawo mata kala uku dan ta saka ta uagawa kishiya a bikinta,

Ta sha zinariya tun daga wuyanta, hannayanta, yatsutsanta, harda ta kafa,

An sha gyaran hashi an sha mak up an kawo mahaukatan jaka da takalmi an saka sai baza kamshi ake ana daga kai inda maroka ke ta waketa, sai dai abinda ya tsaye mata a rai gannin bata ga mai jegon da yaron ba,

Wajen karfe biyu ake walima, dan haka du aka taru ana gabatarwa, 

Nan Agaishat ta fito, cikin shirinta na doguwar rigar lesh mai ruwan golden,

Ta sha sarka da yan kunaye da awarwaraye sa agogo da abin hancinta kowane na zinare ,

Kwaliya yar daidai ce a fuskarta wace ta kara fitar da tsararen kuma nitsatsen kwaliyarta wace sai da Wardugu ya duba da kansa cewar babu kowa sannan ya yarda da ta fita a haka domin kuwa ta jima da aka yi mata tana son fita sai jaje yake wai ta yi kyau sai binta yake da kallo,

Ba kwaliyarta ta girgiza walyn ba, domin kwaliyarta nitsatsiya ce duda tsadar leshen da kuma su sarkar, ta san wardugu ne ya siya mata dan haka bata wani damu ba saima hura hanci da ta ringa yi ta biya marokiya na yi mata kirarin uwar gida,

A lokacin da aka fara rabon kyauta wa du wanda ya zo , a lokacin ta haukace da mamaki, kyautar daga kakar Agaishat, bata ifasa sarewa ba sai da ta ga wacece kakar ta agaishat, Matar GUKUNNI? ita ta haifi mahaifiyar Agaishat, 

Ambulop ce ake baiwa mutane dauke da kudi, sai ka buda ka ga adadin abi da aka baka, nan da nan wajen ya kara rikicewa da murna da shewa, kamar da wasa aka fasa zuzuta walyn din , kudi ya karbe hasken nata, nan da nan maroka sai suka gane bikin wanda suka zo suka juyar da akalar wasawar zuwa ga amarya shalele,

Basu kara sarewa ba sai da garar amarya ta shigo, wace iyayenta sukaiwa ango, 

Ba wai wani abinda ba.a taba gani bane aa, abin ne ba.a yi zaton za.a yi shi haka daga wajen amaryar ba, inda Ayya ta zagime itama ta bada kyauta wa  yaron da ya ci sunna *ABDALLAH* Bawon Allah, da kuma mahaifiyarsa,

Haka aka gabatar da kyautar da Wardugu ya dankara mata, aman bai yiwa yaronsa kyautar komai ba, ya dai yi dogon rubutu na saka albarka,

Kai bude bude ne ya cike gidan, inda ba wanda ya san fitar Walyn sai kofa…

Bayan wata bakwai…..

Rarafowa ya yi ya karaso kusan kafarsa, 

Ya kama kafar ya mike ya rike kafar da kyau sannan ya washkale da dariya yana duban Wardugu dake zaune yana kada kafa ya gama tashin hankalin ba zata je wajen sunnan matar Mu.azam ba, ita kuwa tace a na me? Ba.a zumunci su ke kai kawo hanya?

Ai kuwa ya hayayako yana fadin” Orronur ni ne sai me? Ni ne sai me? Bara na gwada maki sai me!

Da gudu ta afka dakinta ta dani kofar tana kilkila dariya ta kuga ta ce” Wardugu bana son duka

Shi kuwa daga zaunan da yake ya saki murmushi ya dauki yaronsa dake ta bangalar masa dariya ji yake wasa ne ake masa ya rungume a jikinsa kafin ya ce” ORRONUR, BA DAI NI NE WARDUGUN BA KO? KUMA NI NE SAI AN JE DIN KO? BA ZAN DAKE KI BA, AMAN WALAHI CIKI ZAN JARA MAKI!

IDO ta zaro kafin ta shiga kiciniyar bude kofarta dan zuwa ta baiwa mijinta, amininta, yayanta, ubanta, masoyinta, abokin wasanta hakuri ta rarashi abinta cikin hikima….

Tamat bi hamdika????????????????????????

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button