BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 71 to 80 (The End)

Wai wa? Fahad? Baki ga zama cikin yan chaina ba shima tsayinsa da idannuwansa ne kawai basu koma irin nasu ba? Wata shegiyar kunya  dazu fa da muka hadu wajen cin abinci kinga yanda yake hade hannu yana gaishe ni?

Fatimata da haushi ya gama tirniketa ta dubi Gukunni dake kallonsu da sha.awa ta ce” Papou,  ka yiwa yarinyar nan magana, idan tana abu kamar itace Agaishat karamarmu, wai kawai dan yace da ita yana sonta abinda ta fara ce masa zai iya soyaya da shegiya? Wai ita bata da uba,

Gaba daya suka kai dubansu kanta, inda itama su take kallo,

Kanta ta girgiza kafin ta ce” menene? Karya na yi? Ni fa ban iya karya ba, kuma ganninsa na yi ya hade karshen haduwa, zan cuci kaina ne? Dan Nigeria ne, wai iyayensa suna zaune a abuja, shima nan ya yi karatun likitanci da ya gama ya yi zamansa nan yake kara koyon aiki tare da kwararu likitoci, gani na yi daga haduwa da shi ya bani cikenken ko waye shi, shine nima na bashi nawa asalin ko?

Anmi da suke kira da Mamou, ta girgiza kai kawai ta mike ta bar dakin, ita kam bata ga ta ibda za.a daidaita halayan Mariama ba, irin halayen Gukunni ne da ita, tamkar itace yar batuben, sam bata da dar ko shayi, magaifiyarta kawai take tsoron kallo cikin ido ta fadiwa magana, itama ta ci karfinta ta hanyar shareta da yi mata wa.azin girman darajar iyaye.

Gukunni kam sai da ya dan shafa habarsa yana dubanta kafin ya girgiza kansa shima ya ce” kin kyauta, kuma sai na hada ki da Annarki! (Ba ka ji ba, ba zai ga wani girman laifinta ba, domin shima halayarsa kennan????),

A wannan ranar da likita ya zo ya fada masu zasu iya kowani yama su fitar da ita ta dan rawata kadan kadan,  sannan a ci gaba da kwontar mata da hankali, a yawaita saka mata abinda zai sakawa ranta dangana, idan musulmai ne su yawaita kusantata da wa.azizika, da astaghfari, su nuna mata girman kadara, su nuna mata ba kowa Allah ke jarabta ba????????,

Idan har ta nutsu nan da satima zasu iya salamarsu…

Ai kuwa sun ji dadi sosai, inda Herde sai a lokacin ta tatara ta koma tare da Fatimata da dan gidan Gaishata wato Sultan wanda take jin yaron har bargonta, shima ya wani shaku da ita du motsinsa yana makale da ita.

Soyaya kuwa ta dinke da Mariama da Fahad, inda ya hadata da familynsa a vidio call suka gaisa da yar hausarta da bata taka kara ta karya ba, dan kuwa french dinma ba wani sosai take ji ba, buzanci ne shi kuwa ba yarensa ba, soyayar dai ana yinta ne karfi da yaji domin wani sa.in sai a rasa ta yanda za.a isar da sakon khalb.

                     Niger

Da gaske yake, ko nace da gaske suke,

Abu ne ake tamkar ba gobe,

Dukan bukatun Ayya kan lamarin tarewar yarta an cika mata, inda ake shan rigimar shi ba za.a yi wani taron diner ba, kawai a yi saukar alkur.ani, Ayya kuwa tace ai ko walima ne sai ta yi ta gayaci mutanenta an yi taro na kirki itama ta aurar da yarta,

Ido ya kawo ya zuba , yama maida hankalinsa kan aikinsa wanda kulun cikuluftu ke karuwa,

Ayya kam ba kama hannun yaro, wani irin shiri take yiwa yarta wanda siri ne, 

Ya kasance  ko masu aiki basa gannin Agaishat a dakin da ta kilaceta, daga ita sai ita, 

Du a tunanin Ayya y’artata ta saan aure, hakan ya sa take wani irin shiryata dan ko ba komai ta iya zama a gidanta, kar a rainata ta wannan fannin,

Sosai ta bata magannin infection, kafin ta shiga bata lakaninika ciki harda yusufa da kankanna, 

Kwata kwata ta haneta shan ruwan sanyi, inda take dumamata da masu dan dumi , 

Haka indai jikinta ya ji iska tofa wanka ta shiga, tana fitowa take maida lulubinta ta lulube, dalilin haka har yan kurajen zafi ta yi, suka mutu dan kansu jikinta ya saba ya kasance koda yaushe cikin dumi yake,

A kulun zai yi zuwa biyu gidan, yakan bi Ayya da kallo ne, tun lokacin da ta masa iyaka da tambayarta Agaishat, ya kawo ido ya zuba mata, wai tana gyarata, har sai da ya ce”Ayya, ni guaran na menene? Me kike gyarawa ne?

Ta yi masa shiru ta kawar da kanta, dan ba za.a ja maganar da ita ba, idan shi bashi da kunya ita kam tana da ita

Shi kuwa daga shi ya yi shiru ya daina tambayarta ita, kuma abinda ke bashi mamaki ko wulginta da baya gani, ya dai san lokaci ta deba, kuma saura kwana uku, hakan ya saka ya kawo ido ya zuba mata,

Yau sauran kwana daya kacal tarewar Agaishat, 

Kowa ya dauka kan tarewa ne, dan ta taba aure, 

Jama.a da yawa na mamakin wannan aure , General ya auri bazawara? Ayar tambaya, wa.inda suka san matar da amininsa Mu.azam ya saka ce kuwa suna yayata maganar daidai da mandan bakinsu,

Wardugu, bai san irin halin da zai kwatanta yake ciki ba, ga aiki da ya sako shi gaba domin ana yawan kawo hare hare yankin Diffa, tsaye kan kafafunsa , dan haka ya kara neman alfarmar kar a yi maganar diner, gannin halin da ake ciki ya saka Ayya amincewa , aman hakan ba zai hanata yin nata taron ba, 

An kawo garar amarya da akwatuna, 

Zama zanowa bata lokaci ne, Wardugu ya kashe kudi sosai, kaya kuwa an zuma na yar gata,

Agaishat kan fashewa da kuka wani lokacin , kukan murna, kukan godiya ga Allah, tana jin Ayya har kasan zuciyarta, girman Ayya daban ne, tana sonta so irin na da da uwa, 

Saima idan ta zauna tana tuna hirarsu ta yau bayan salar asuba, yau da ya kasance za.a mikata dakinta, gidan mijinta, wanda take fatan sai dai a fitar da gawarta, Ayya ta dubeta ta ce” zan so biyayarki, tsoron Allahnki, ya kasance bayan zuciyarsa da kika shiga, ki shiga kowani motsi nasa,

Agaishat, ban hore ki da rashin kunya ba, ban hore ki da tsayaya ga miji ba,

Agaishat, shin wanda aljanarki take karkashin kafarsa wani irin motsi zaki yi dan gannin ya dage kafar nan tasa ya baki damar shigewa? 

Ki yi masa biyaya, 

Ki barshi ya fada, 

Idan ya daga murya ki kaskantar da kanki, 

Kar ki yarda yana fada kina fada Agaishat, da haka gwara ki yi nesa da shi! Ban ce ki zauna ya wulakanta ki ba fa, ko daya, ina dai doraki kan hanyar da zata kai ki ga ci ne, 

Kin ga kar ki yarda daga saman salayarki ki sauka da asuba ba tare da kin furta kwali a kwayar idannuwanki ba, ki adana kwalin ki kusa da abin salar ki!

Kar ki haye gadon da kika gyara dominsa kafin shi ya hau (ina kuke ne mutanenmu , iyayen mu????, gafa wajen????),

Idan ya yo dare, ki kasance mai jiransa , kar ki je ki jibge saman gado, har ya zo ya gama abinda zai yi kina minshari (???? kin ji ko maniu????????),

A duk lokacin da kika ga da hali, akoy robar wankin kafa, akoy dutsi, ki zauna a yar kujera ki saka kafarsa ki wanke, ba dan ta yi dati ba, sai dan kara shakuwa tsakaninku koda kuwa bai saba gani ba, kar ki wani damu ke dai ki koya masa irin zamanki da kike so ku yi,

Akoy wahala fa, domin kuwa ba ke ya fara aura ba, ba ke kika fara rainonsa ba, zaki ga abubuwa da yawa wanda haka matarsa ta hore shi da su, wasun zasu canzu cikin hikima da juriya da hakuri, wasun kuwa Agaishat sai dai ki rayu da shi a haka!

Sai maganar kananun kaya,

Ina mamakin zamani, ina mamakin yayi, 

Wai idan za.aiwa yarinya aure da budurwar da bazawarar da datijuwar sai ki ga ta kama kwasar kananun kaya , kananun kaya ita dai, 

Uhum, kuskure baba, 

Ke Agaishat shin sex din ne kawai ya kai ki gidan auren? Tabas shi ne jigo, shi ne farkon gini, aman shi din an gaya maki zama kusan tsirara a kulun ne zai saka shi armashi?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button