BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 71 to 80 (The End)

Ja ya yi ya goya hannunsa daya a bayansa yana dubansu har suka fice da motarsu,

Agaishat dake tsaye bakin window din dakinta ta sauke ajiyar zuciya kafin wani murmushi ya kubuce mata, 

Zama ta yi bakin bed dinta daga ita sai gajeran wandonta da yar riga karama na baci ta ce” Wai wai wai, rigimame yayana, kai aman gaskiya shi ne daidai da matar nan tasa , haba mace kamar wace aka haifa ana dambe? Ita kulun cikin fada da neman a gabzu take? 

Gashin kanta ta tatara ta daure kafin take yin bismillah ta bi lafiyar gadon,

Idannuwanta ta lumshe dan neman baci, sai dai me….idannuwansa ta ji sunna yawo a jikinta,

Wani irin tsammmmmmm ne ta ji tun daga kanta har yatsarta,

Da sauri ta mike zaune tana yatsina fuskarta, 

Mikewa ta yi ta koma bakin window din ko zata kara ganninsa? Kai wollah ita bata gajiya da kallonsa, tana tsoron rigimarsa , aman kuma tana girmama irin yanda yake girmama mahaifiyarsa, ba mahaifiyarsa kawai ba du wani abinda ya shafeta yana masa mugun girmamawa, zata so komai ya daidaita tsakaninsa da mahaifinsa, zata so gobe kiyama ya samu rabauta, domin aljanarsa tana karkashin kafar mahaifansa, tana so alkhairinsa ya same shi gobe kiyama ,

Yana tsaye dai, da waya a hannunsa yana danawa, ba zata iya gannin me yake dannawa ba, 

Bata shirya gannin ya dago da kansa ba sai gani ta yi ya kallo wajen windows dinta, da sauri ta duke kasa domin ba zata so ya kamata tsamo tsamo tanai masa kallon kurulah ba, me zai ce? Ina ai sai ya yi mata wata muguwar fasara,

Ajiyar zuciya ya sauke kafin yake sakin murmushi, ya ji idannunta a jikinsa, ya san ta tsaya a wajen can…..

Juyawa ya yi ya koma fallon yana kara kiran abokinsa kuma direbansa kan a gobe su bi jirgi su jufi timiya, zai daki abin da karfi ya ga mai tsayar da shi daga Walyn, da Ayyar, da uta Agaishat din! Idan tana so idan ta ji ya aureta ta hadiyi shinkafar bera ????

???????????????? *BAK’A CE* ????????????????

                            Na

                     *SAJIDA*

                          7️⃣6️⃣

*KUTKALE* (PRISON)

*AURE YAKIN MATA NE*

*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*

daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA*  in sha Allah,

……..kar ku bari a baku labari…..

A nan falo ya kwana , ko nace ya yi rabin kwana , domin bai shigo falon ba sai da ya dauro alwallah ya zo ya tayar da sallah ,

Ya jima yana sallah kafin ya zauna ya yi ta adu.a, 

Ya roki Allah, ya kaskantar da kansa wajen ubangijinsa, ya roki zabin Allah, ya sani bai isa ya baiwa kansa ba, ya roki Allah ya sa alkhairi ce a gare shi da kowama,

Nan saman salayar dake falon ya jingina da kujera ya dan rintsa, 

Asuba na yi ya farka ya fice a falon inda ya je ya sake daura alwallah ya fice a gidan dan zuwa masalaci,

Yana dawowa wajen karfe shida da yan mintuna ya zauna nan saman kujera idannuwansa suka kai kan wayarsa dake ta vibration,

Ikon Allah, shi ne abinda ya fada kafin ya ja dan tsaki kasa kasa yana mai jin haushin masu saukon kiran nan! Ko me zai masu?

Wayar ya janyo yana duba sunnan,

Mamaki ne ya kama shi, aa *GUKUNNI* kuma?,

Da sauri ya mike ya daga kiran, domin abu daya ya fado masa a rai ko wani mai laifi ne ya gudu daga cikin prison? 

Salama ya yi masa , suka gaisa da kyau kafin wardugu ya yi shiru yana saurarronsa,

Gukunni ya ce” gani a kofar gidanka Wardugu,

Wardugu ya kara kamuwa da mamaki aman sai ya boye ya ce” ai ina gidan Ayya ne Honorable,.

Gukunni ya shafa sankon kansa ya ce” ka kwatanta min in sha Allah zan karaso, ina tafe da muhimiyar magana ne , wada na jima ina nemanka Allah bai yi ba sai yau na samu wayarsa

Wardugu ya dan tsurawa waje daya ido, anya kuwa zai kwatanta gidan mahaifiyarsa haka kai tsaye? 

Sai dai wata zuciyar ke fada masa da ba komai bane sai alkhairi, dan haka ya yi masa kwatance suka katse kiran,

Rigarsa ta saman kakinsa ya nema ya dora saman bakar rigar dake jikinsa, 

Kansa ya daga sama ya ga basu fito ba, bai ji motsinsu ba, dan haka ya zauna nan yana jiran karasowar Gukunni Bayan ya baiwa masu gadi damar idan ya zo ya shigo,

Ya kai minti arba.in kafin ya karaso, domin dai ba sannin gidan ya yi ba bale ya kai kansa kai tsaye, 

Sai dai a lokacin da ya ga kofar gidan ya gane ko gidan waye, wato Elhaji Marahut, tabas sunnan Wardugu , Wardugu Marahut, 

Murmushi ya yi ya lalubo wayarsa ya dannawa Marahut kira , da yannayin barkwonci yake sanar masa komai da fadin ai yana kofar gidansa,

Nan marahut ya yi jim kafin yace da shi baya kasar fa, aman zai shigo da wuri wuri, shima ya yi murna sosai sosai, sukai salama,

A tsakar gidan aka dakatar da shi, kafin Wardugu ya fito,

Tunda ya fito yake dubansa da yannayin farin ciki, kai shi dai yana son yaron nan ko dan kwazonsa da rashin tsoronsa,

Wardugu na zuwa ya bashi hannu suka gaisa sosai, sannan Marahut ya ce” Wardugu, tafe nake da magana mai mahinmanci, fatan zan samu lokacinka,

Wardugu ya amsa shi tare da yi masa jagora zuwa falon Ayya, domin ko ba komai yana kaunar datijon yana gannin mutuncinsa, dan kuwa su shara.ar da ya je ya gani da idonsa wace ya yanke hukunci na manyan kasa masu laifi, yana gani da idonsa yana yankewa ne da zuciya daya ba tare da wani dar ba, hakan ya sa ake bashi tsaro domin ya kasance yana samun hare haren mutanen da suka ji haushin irin hukuncin da ya yanke masu ko wani nasu!

Suna shiga suka tarar da Ayya na saukowa daga sama, sai naza kanshi take, zuwa lokacin duka duka karfe takwas ce, inda Wardugu ke duba lokaci dan kar karfe tara ta yi lokacin tashin jirginsu zuwa agadez,

Gaisawa suka yi, nan Ayya ta mike zata bar masu wajen aman ya nemi da ta zauna,

Cikin nutsuwa ya shiga warware masu abinda ke tafe dasa shi,  ya dora da fadin” lamarin ne a cakule, lamarin ne a hargitse, kadara ce ta afka mana, sai dai mu ce Alhamdulilah, autata Allatchi ita ce mahaifiyar yarinyar, ta fuskanci rayuwa sai hamdallah, yanzu haka tana Chaina, tana karbar magani, nima nakan zo sati sati dan na kara duba tsohon da muka zo da shi duda akoy masu kula da shi, nakan zo na ga komai na tafia daidai kafin na koma wajensu,

Al.ajabi, tausayi, ne suka kashe Ayya a zaune, inda wardugu ya sada kansa yana jin wani lamarin da bai san menene ba,

Ayya cikin mamaki ta ce” ta yaya? Waye ya daura masu aure? Waye ya yi gigin daura masa macen da bai ga alwalinta ba???

Gukunni ya yi shiru, jikinsa ya kara mutuwa, hankalinsa ya rashi, ransa ya kara baci da lamarin, dubansu yake yana tunanin sun cancanta su ji haka kuwa? 

Eh kwarai sun cancanta, idan ya so, idan mijin da ya aureta ya ce ba zai zauna da ita a haka ba ba laifi, Allah ne gatan bawa, dan haka ya dago fuskarsa da ta nuna yannayin da ya shiga lokaci guda ya ce” *BAI AURETA BA, BA AURE YA ZAUNA DA ITA , BA AURE SUKA SAMU ALBARKAR HAIHUWA*

Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une,

Shi ne abinda Ayya ta fada tana mai dora hannunta saman kanta, 

Wardugu ya dago da kansa da mugun sauri tare da bugawar zuciya,

Bin innalilahin da Ayya ke maimaitawa ya yi, 

Tausayi? Mugun tausayin matar ne ya dirar masa, sai tausayin Yaren, ya Allah, kowa da kalar kadarar rayuwarsa, Agaishana….shi ne abinda zuciyarsa ta ambata,

Ayya? 

Muryar Agaishat ya katse masu halin da suka shiga,

Da sauri Ayya ta sauke hannunta daga saman kanta, domin hakan da Agaishat ta hango ne ya sakata saukowa da gudu daga sama dan jin ba.asi, sam bata lura da Gukunni ba, sai da ta ji an riko hannunta an juyota,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button