BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 71 to 80 (The End)

Agaishat ta lumshe idannuwanta ta bude ta ce” *INA SON KA* 

Bai bari ta karasa ba ya shigar da ita jikinsa, ajiyar zuciya kawai yake saukewa tamkar yau ya fara jin kalmar so a bakin mace, 

Sai da ya jima sannan ya sasauta mata rikon, aman kuma tana cikin jikinsa tamkar wani zai kwaceta,

A hankali ta ce” zan so gobe kiyama na yi alfahari da kai, zan so yayanmu idan Allah ya nufe mu da samu su yi koyi da halayanka, 

Ba zan iya budar ido na ga danka yana gaba da kai ba, zan iya samun arret cardiaque (heart attack) dalilin haka, domin kuwa d’a ko na wace mace ne, in dai naka ne toh bugun zuciyata ne,

Tsai ya yi yana kallonta, zuciyarsa fesss , inda ya  dago inda ta nufa da magangannunta,

Shirun da ta kuma yi tana mai daidaita bugun zuciyarta da tsoronta ya saka shi dan tapping din bayanta ya ce” Uhum?

Dan dago da idannuwanta ta yi ta ga ya tsareta da kallo, irin kallon nan na ya fara kausasa,

Takwaf takwaf ta yi da fuskarya ta samu ta mike tsaye inda ta yayumo abin shinfida tana kare jikinta da shi,

Hannunsa ya saka ya dangwarar da ita gabansa tamkar baby, ya daga girarsa duka biyu ya ce” karasa,

Da sauri ta girgiza kanta ta ce” shikenanma , abinda zan fadi kennan,

Wardugu ya girgiza mata kai shima ya ce” karya ne, fada min karshen maganar

Agaishat ta lumshe idannuwanta, a hankali ta fashe da kuka tana dubansa da yannayin yanda zai dauki kukan,

Ai kuwa ya nunan domin kansa ya dafe ya ce” meye na kukan kuma ? Me na miki?

Agaishat ta ce” to ai na san idan na fada kana iya dukana, ni kuwa bana son duka,

Wardugu ya sauke ajiyar zuciya ya ce” nima bana son taba lafiayarki, ki yafe min na dazu kin ji?

Agaishat ta gyada kanta ta ce” to, ka sani idan ka dake ni, ba komai, na yafe maka, aman dan Allah kar ka min mai zafi,

Shi dai kallon yannayinshagwabarta yake kafin ta ci gaba da fadin” yaya kake son haduwarka da Allah ta kasance? Ni mahaifina ya tsane ni, baya son ganina, aman ba Sofo yace na yi ta masa biyaya dan na samu rabauta gobe kiyama, ka ga ina son mahaifina komai mumunan halayan da yake aikata mana da mu da Anna,

Da sauri ya dubeta, wani tausayinta ne ya ji, tana son mahaifinta? Koda kuwa ta ji a irin hanyar da ya same su su duka? 

Katse shi ta yi ta hanyar fadin” kuma ka ga kaima zaka haihu, idan ka haihu yayanka suka yi maka haka fa? Mace? A kan mace? Ka dora muguwar gaba da mahaifinka haka? Dan Allah ka min rai, ka gyara tsakaninku da Aba, da kuma tsakaninsu da Ayya, na tabata idan yau ka yi niya sun gama shiryawa kennan, idan ya so ka barsu su gani da kansu, zasu koma rayuwa tare ne ko ba zasu koma ba? In dai an samu sulhu, zaka samu ladan hakan, kaima kuma Allah zai yafe maka, zaka ga daukaka sai dai ta yi ta kara zuwa, Allah zai kara kareka daga du wani shari, yayanka zasu mutuntaka su yi maka biyaya, matanka zamu ci gaba da mutuntaka mu yi maka biyaya,

Hannunsa kawai ya saka ya dafe yana dubanta,

Sai da ta gama sannan ta sake mikewa da sauri ta nufi bayi,

Tana shiga ta rufe tana sauke ajiyar zuciya, wai wai wai, bai kara tsinka min marin ba…..shi ne abinda ta fada kafin ta je ta shiga kiciniyar kimtsa kanta tana mai adu.ar Allah ya sa ta ci nasara,

Ya dan jima zaune kafin ya mike ya nufi bangarensa,

Shima wankan ya yi ya fito ya zauna bakin bed,

Shiru yana duban waje guda, wa ya koya mata? Dukan magangannun nan da ta yi, ba wanda ya taba yi masa su haka a dukan masu neman sulhunta shi da mahifinsa, ko kuwa ita dan yana jinta a ransa ne magangannun suka yi tasiri a zuciyarsa haka? To aman ai Walyn ya fara aura, hasalima bata taba tayar masa da maganar ba, tana tsoron ta yi ne ya mara fada ko me ya hanata yin? Ko bata damu da gobensa bane?

Wani abin yace…aaa, ba rashin damuwa da gobenka bane, just ita dai bata da kula a wasu abubuwan ne ai,

Ya jima zaune, kafin yake gannin haske a wayarsa,

Marahut ne ke maido masa da kira, 

A hankali ya daga, yana dagawa Marahut ya ce” Wardugu, walahi babu saka hanuna a sakin wannan yarinyar, hasalima ni tun da na gane irin mugun aikin da take yi, da bin maza da urena a kanta na saketa, ban san wa ya shige gaba wajen sakinta ba, yanzu nima Gukunni ke fada min sakinta za.a yi, Wardugu ka fahimc…..

Wata kunya ce ta lulube shi, innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, mahaifinsa? Mahaifinsa ne ke rawar murya dan ya wanke kansa a wajensa? Wata irin masifa ce wannan? Dama haka suke rayuwa? Dama haka Marahut ke masa magana ko yau ne haka ta faru? 

Muryarsa ya ji tana rawa, a hankali ya ce” ABIH,.

Marahut dake ta faman kare kansa ya yi dif, 

Kunnensa ne ke jiyo masa abinda yake son ji daga bakindan nasa ko kuwa gaske ne,?

Dan haka sai ya ci gaba da maganar a darare,

Wardugu cikin yaren tubanci ya ce” Abih, dan Allah ka bari, ya isa haka, ka bar mini rantsuwa, 

Da sauri ya dubi wayar, number Wardugu ne, dan haka hankalinsa ya tashi, mikewa ya yo ya ce” me ke damunka? Baka da lafia ne? Me akai maka? Kana ina ne? Wani abu ya sami Ayyanka? Ko wani abu ya samu iyalinka? Menene War?

Wardugu ya ce” ina gidana , dake aeroport, kai kana ina Abih????

Marahut kashe wayar ya yi, daga inda yake sai cikin motarsa ya tayar cikin tashin hankai ya nufi gidan Wardugu,

Wardugu kam kansa ya dora gefen gado yana jin wani irin tausayin mahaifin nasa, yanzu da shi ne haka ke faruwa da shi , da dansa ina zai saka kansa? Ya zai rayu da haka?

Bai san adadin lokacin da ya dauka a haka ba, sai kiran masu tsaron kofar suka shaida masa Marahut ne,

Cikin tsawa tsawa ya bada umarnin a barshi ya shigo ko.ina, babansa ne fa!

Ai kuwa suka bar Marahut shiga ,

Yana parking din motar ya fito yana neman ta inda zai fara dan samun gannin Wardugun,

Sai dai hango shi ya yi tsaye yana kallonsa,

Takawa ya shiga yi yana duban yannayinsa har ya isa gabansa,

Ya budi baki zai yi magana kennan ya ga Wardugu ya duka….. ya duka har kasa, kansa na kallon kasa, 

Jijiyoyin jikinsa du sun daga dan yannayin da yake ciki, muryarsa wani irin ya ce” dan Allah ka yafe mini, ka yi hakuri ka yafe mini,

Marahut da ya ji wani iri zuciyarsa ta buga da karfi ya saka hannunsa ya dago wardugu yana dubansa, hannunsa ya saka yana taba lafiar jikinsa sannan ya ce” me ke damunka? Baka da lafia ne?

Wardugu ya girgiza kansa yana mai jin haushin kansa, wai ace dan ka yi dadan magana wa mahaifinka sai ya shiga rudu? Lale ya jima yana tafka barna,

Kansa ya dafe da hannun nasa kafin ya ce” lafiyata kalau, ina neman yafiyar irin abubuwan da na yi maka  Abih, tabas matar mutun kabarinsa, tun ran gini tun ran zane, ka yafe min ,

Ai kuwa Marahut ya saki murmushi ya rungume Wardugu a jikinsa, bai iya cewa komai ba sai jan hannunsa da ya yi suka nufi motarsa suka shiga, Wardugu ke ja, Marahut kuwa sai sakin murmushi hamdallah ga ubangiji yake, baima san me yake ji ba, fatansa ya shawo kan Ayya cikin sauki

(Mace ta gari kennan, masha Allah)

Bayan kwana biyu da faruwar wannan , Walyn ta zo gidan, 

Sun sha daru da masu tsaro , inda suka hanata shiga fir, 

Ta kusan wuni a kofar kafin Wardugu ya dawo, ganninta a zaune a waje ya saka  ya barta shiga cikin gidan, inda ta ringa bin ginnin da kallo, tana mamakin nan ya kawo bakar mace dan zubar aji?

(Ku gane, shi fa gyaruwar halayan mutun abu ne mai matukar wahala ba kamar yanda muke zano mugayan halayan mutane sannan mu nuna lokaci daya sun gyara a cikin novel ba ko an sake su ba, kowa kuma na zaune da ra.ayinsa ne, shi shiryuwama sai Allah ya nufa, sannan ba lale mutun ya daina dukan halayansa ba, sai dai a rage a samu sasauci, sannan idan ya hadu da daidai kugunsa sai a yi ta buga game din wardugu dai ba zai saki mace ba, domin wani irin mutun ne shi mai kishin balaki, ku gane ba wai wani so ko wani abin ya hana shi sakinta ba, sai kishin ya saki macen da ya malaka wani ya malaketa, shi fa izgili yake yiwa al.adu da canfe canfe inda yace rabon ya jima bai.kashe shi ba! Idan abu ya yi kamari ne sai ya watsar da ke, ranar da kikai hankali kya nemesa ) ,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button