BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 71 to 80 (The End)

Habarsa ya dafe kawai yana dubanta, sai da ta gama fadan ya mike ya shiga haurawa saman dakin Agaishat din inda Ayya ta mike da sauri ta bi bayansa,

Gannin tana biye da shi ya saka ya haye da sauri ya shige dakin ya rufe,

Zaune take tana cila yan kafafunta saman kujera, ita bata wani saka abin a ranta ba, sai tsagal ta ga mutun a gabanta,

Fuskarsa ce ta kayar mata da gaba, inda ya nemi waje ya rike a jikin hannunta , kausasa muryarsa ya yi ya ce” ba sai na rantse maki ba, ki yarda ko aa, daga yanzu du wani katon da ya ga fuskarki dukanta wanda ba muharaminki ba , sai na kwakwalo idannuwansa  na soya maki kin ci! 

Ya zaki ringa fita da irin wannan shigar kowani gaula na gannin ki? Ke kin san me zai raya a ransa a kanki? Ya yarinya karama da ke tun da kika shigo rayuwana zaki ringa zigani uwa shayi? *KE* ya fada yana nunota da dayan hannun nasa wato da yatsarsa manuniya sannan sai a lokacin ya hada idannuwansa da nata,

Gaba daya ya ji ana janye iskar tashin hankalin da ya zo a yi daga jikinsa, fuskarta ta marairaice ta zama tamkar ta jariri, dan bakinta ta dan bude shi inda hakoranta na gaba kwaya biyu da suke da dan tsayi kadan ruwan na zomo suka dan leko haka kuma ana gannin na kasan jere reras fari kal da su suna dan shekin abin yawun bakinta,

Idannuwanta tar cikin nasa, sun dan canza kala daga fari kar zuwa orang kadan alamun suna daf da cika da kwala, 

Dan girgizatan da ya yi ya saka gashin kanta dan hautsinewa suka bazo gaba kadan, 

Kallon cikin idon da take masa, tafe yake da sakon ka ji tausayina, kar ka ilata ni????????,

A hankali ya shiga sasauta mugun rikon da ya yi mata, tsayinsa ya rage kafin yake lumshe idannuwansa,

Abinda ke kara tarwatsa tunaninta ya yi mata, wato janyota ya yi a hankali ya rungumeta tsam a jikinsa inda idannuwansa ke lumshe yana daidaita bugun zuciyarsa tare da neman tayimakon Allah kan kar ta ci karfinsa????,

A hankali ya ce” *ki daina fita a haka, kin dai san yanzu mijinki ne ni ko? Walahi idan kika ki bin magana na, Allah zai toya ki, ni kuwa in dai kan fita ba lulubi ne ba zan iya yafe maki ba, dan ina iya aikata aikin dana sani ORRONUR*……

TO KU BANI KIDAN COMMENT A SAMA………..

NVL YA KUSA KAREWA, ALLAHU YA NUNA MANA KARSHENSA LAFIA

???????????????? *BAK’A CE* ????????????????

                            Na

                     *SAJIDA*

                          7️⃣9️⃣

*KUTKALE* (PRISON)

*AURE YAKIN MATA NE*

*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*

daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA*  in sha Allah,

……..kar ku bari a baku labari…..

Sowie yau kadan ne????????????????????????????????

*Mijinki ne ni ko?* shi ne kalmar da ta fi kara sakata wani yannayi na firgici da shiga wani irin hali,

Kennan ya ji, ya sani, harma ya kirayi kansa da kalmar *MIJI* a gareta, wannan gayen mai tsada? 

Idannuwanta ta lumshe ta kara shiga kirjinsa dan walahi kamshinsa daban ne, duda na yau ba irin na kulun bane aman na yau dinma wani silent kanshi ne,

A hankali take kara shigar da hancinta wajen botiran jalabiyar tana shakar kanshin, tana mai jin duniyarta ta kawata,

Shima dake rungume da ita caji kawai yake dauka, a hankali ya dora hancinsa saman gashin kanta, kamshin daban ne, kamshin mai ni.ima ne, mai sanyi ne, a hankali ya dora hannunsa wajen tsatsonta daga baya ya dan rike kadan kafin ya ce” *UM*? 

Agaishat da ta hadiyi yawu da kyar , ta dan cire hancinta daga wajen kirjin masa , idannuwanta ta dan dago ta ce” *Um?*

Wardugu ya tsura mata ido shima yana dubanta, a ransa kuwa fadi yake….yanzu haka ya je wajenta? Haka ya ratsa min ita? Haka ya taba min jikinta? Har fadi min yake ni.imarta? Ya Allah????,

A fili kuwa ya ce” baki ce komai ba, bayan na budi baki na yi ta maki zubar da bana yi!

Agaishat ta mayar da kanta saman kirjinsa dan walahi ita bata so ya janyeta a yanzun kam, a hankali ta ce” ni tsoro nake ji,

Wardugu  ya yi jim tamkar ba zai tankata ba kafin ya ce” tsoro? Na me?

Agaishat ta yatsina fuska kafin ta ce” idan ranka ya bace, idan kana fada, tsoro nake ji, dan Allah idan na bata maka rai kar ka yi min duka ka ji? Ba zan kara fita a haka ba, dan Allah kar ka min mugun duka walahi ba laifina bane,

Ta karashe tana lumshe idannuwanta tana jin yanda zuciyarta ke dokawa,

Bai so ta yi shiru da magana ba, buzancinta na tafia da imaninsa, ta iya karya harshenta da fadin RRRRRRRRRRrrrrrrrr sannan tana magana tana lumshe idannuwanta ne, sannan lebenta na wani marmarmar gashi sam baya rabuwa da man lebe,  

Dan haka Wardugu ya ce” *Laifin me kika yi?*

ya tambayeta a hankali , 

Dan haka ta dago da kanta ta kure shi da kallo, yanda fuskarsa ke fitar da wani yannayi mai fuzga, idannuwansa kuwa a limshe suke, dan haka tana duban nasa bata san da shima ita yake kallo ba ta dan yatsina fuska ta ce” na aura maka ni da ya yi,,

Bude idannuwansa ya yi gaba daya bisanta, hakan ya sa ita ta kawar da dubanta a kansa, 

Janyeta ya yi kadan daga jikinsa dan lamarin ya fara karkata baya so ko daya ta gane shi, 

A hankali ya karasa da ita bakin bed dinta ya zaunar da ita ,

Wani tsadaden murmushi ya yi mata kafin ya daga kafadarsa ya ce” zan yi tunani…….

Tana zaune ya juya ua je ya bude dakin , burum Ayya ta shigo tana dubansa tana duban Agaishat,

Bata ga wani yannayi na firgici ko tsoro a tatare da ita ba, haka shima bata ga wani bacin rai a tatare da shi ba, hasalima rabawa ya yi gefenta ya fice a dakin,

Ayya ta karasa inda take zaune tana dubanta, 

Agaishat ta dago da murmushi mai sauti ta dubi Ayya ta ce” Ayyana, bai dakeni ba, Ayya wai menene ma.anar *ORRONUR* 

Ayya ta zaro idannuwanta da yanayin mamaki karara a fuskarta,

Kawar da kanta ta yi tana boye murnarta, da fushi ya shigo dakin, aman ya fita wasai….shi ne abinda ya fi tsaye mata a rai, Alhamdulilah… shi ne abinda ta fada, sai ga wayarta na kuka,

Kanta ta dan dafe ta dana ta mikawa Agaishat ta juya bata bata amsar tambayarta ba, yo ita me zata ce mata? Kai gaskiya da nauyi.

Agaishat ta kara wayar a kunnenta, nan Alhinayett t saka ihun murna daga zaune fadi take” Agaishat, ina yake? Yana ina? Tun da na ji labarin nake doka wayoyinsa aman gaba daya a kashe, takima a kashe, wayo Allahna dan Allah bani labari dala dala tawan, fada mini yanda aka yi lamarin, ya furta? Ya fada ne? 

Agaishat ta rafka tagumi tana sauraron Alhinayett kafin ta ce” wai an furta me? Waye zai furtan?

Alhinayett ta ce” wahala ne zaki bani dan kin san ba zan iya fitowa yau ba ko? Ki fada min ta yayane ya furta? Wayo ni baku tashi soyewar ba sai da aka shige daka da ni?

Agaishat kam du ta sakata cikin duhu, wai soyewa, wai ya furta? Murmushi kawai ta yi ta mata gum kan itama bata san da auren ba sai dazu Ayya ta shigo ta fada mata, 

Alhinayett ta jinjina lamarin, ta fada mata in sha Allah da ta fara zuwa aiki zata roli alfarmar ta zo gidan, tana da magama da ita, sannan ta buda wayarta….

Haka dai suka yi salama , inda Agaishat ta yi tsai da wayar a hannunta, magangannun take kara bita tamkar karatu, 

Guguwarsa bai hana shi zama special a wannan fannin ba,

Aa, ita da ba auren soyaya bane tana jin duniyarta sabuwa a cikin kirjinsa to ina ga matarsa? 

Ya Allah dole ta yi kishin abinta, dole ta ji ba dadi, 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button