BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 71 to 80 (The End)

Walyn dake zaune kanta kasa tana share hawaye cike da tsoronsa, kar ta yi abinda za.a maimaita wanda aka yi kafin ya bar gidan ta budi bakinta na rawa ta ce” War…..

Hararar da ya watsa mata ne ya saka ta hadiye sauran maganar, 

A hankali  ta taso ta dawo kusa da shi tana duban yannayinsa ta ce” …….

???????????????? *BAK’A CE* ????????????????

                            Na

                     *SAJIDA*

                          8️⃣3️⃣

*KUTKALE* (PRISON)

*AURE YAKIN MATA NE*

*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*

daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA*  in sha Allah,

……..kar ku bari a baku labari…..

Ta ce” Wardugu, har ka manta da ni? Tun ba.a je ko.ina ba har ka manta da ni? Wardugu ni ce fa matarka, uwar gidanka, danme maza bakwa yiwa kanku adalci bale ku yiwa wani? Wardugu saboda wata can bakar mace zaka yarda ni? Dan an cusa maka mace an baka shi ne ni zaka yi watsi da ni?

Wardugu ya dade kansa da hannayensa bibiyu kafin ya dago da dubansa, 

A hankali ya ce” me yasa ba zaki yiwa kanki adalci ba? Waye bai san irin yanda nake daga maki kafa ba? Walyn, kawai dan na yi aure sai karin tijara? Walyn yaushe iyayena zasu yi daraja a idannuwanki? A lokacin da na je wajenki na kasance mai matsanancin girmama iyayenki, a sanu kika koya mani halayen tafka rashin kunya a gabansu,

Walyn nima fa mutun ne, ina so na ga canji a rayuwana, 

Mahaifiyata da kika gani, ta fi min kowani halita a nan gidan duniya, da kina da hankali, kina da wayo, koda kin tsaneta ne sai ki boye tsanar nan ki kyautata mata, 

Aman ina, a gaban idona sha nawa zaki bita da wani kallo idan ta bada baya? Ina sane, ina gani , ina lure, kawar da kai ne nake dan a zauna lafia!

Da ace rashin hankalin ki iya ni kika tsaya, da zan ci gaba da jan kwababiyar rayuwar nan,

Aman walyn bayan ni, kika tsalake kika haura iyayena, sannan kika tashi kika je kika cire kwaina? Mahaukaci ne ni da ba zaki hada zuri.a da ni ba? Meye aibuna? Me na rage ki da shi?

Walyn dake sauraronsa sosai zuciyarta ke kuna, au fadama zai dora daga inda ya tsaya kennan? Du irin yanda ta zubar da ajinta take son su fuskanci juna shi ne zai rufeta da fada? Mahaifiyarsa, mahaifiyarsa,

Walyn ta dube shi, walahi ita tsoron haukansa take da ta fadi magana, dan haka ta ce” aman ai ba.a kyauta min ba ko?

Wardugu ya kausasa murya ya ce” waye bai kyauta makin ba?

Walyn ta so tace Ayya, aman gannin yana cikin yan maganan, kar ta kwabe komai ya sa ta ce” kai mana, ka kyauta min ne?

Da na yi me?,

Walyn ta kifta ido tana du dubansa ta ce” da ka yi aure kafin lokacin ka yin ya yi, da ka yi aure baka sanar mon ba kafin ka yi, da ka auri wannan yar yarinyar har ka juya min baya tsayin sati uku, da ka dauketa ka kaita gidanka na aeroport ni ka barni a nan ana ci min amana,

Wardugu ya sakar mata murmushi, ya kawar da kansa, can ya ce” adinina bai zo min da salon al.adata ba, dan na yi ban yi sabo ba,

Sannan da na yi ban sanar maki ba uwata ce ke? Nan ana daura aurena ban je na ga kowa ba sai ke, aman kika take ni! 

Dubanta ya yi cikin ido ya ce” Agaishat kuwa, Wollah sonta nake!

Kyam ta yi tana dubansa, 

Kanta ta kawar ta ce” ba zaka huce ba kennan?

Mikewa ya yi ya dauki ky dinsa ya juya da niyar tafiarsa,

Da sauri ta mike ta ce” Wardugu tafia zaka yi?

Juyowa ya yo yana dubanta kafin ya tako zuwa inda take tsaye ya dubeta da kyau ya ce” ban tsara saki wa mace ba, da na jima da rabuwa da ke bisa rashin hankalin da kike tafka min na yau da kulun Walyn,

Ban waiwaye ki yau ba dan isarki, kyanki, ko farin ki kamar yanda kike takama sai dan tsoron Allah da tunanin ko kin nutsu ne ? 

Baki nutsu ba, har yanzu baki sauka daga inda kika hau ba, 

Allah kawai nake tsoro, ina jin tsoron haduwata da shi da laifin wani a kaina, idan kika cire wannan, ki je du abinda zaki yi ki yi! 

Yana gama fadar haka ya juya ya fice tana kugin kiran sunnansa ya yi mata banza,

Tsaki ta ja kafin ta wurgawa hanyar da ya bi harara ta yi kwafa ta ce” in dai rawar kan amarci ne, zaka yi ka kare, ba wani ka waiwaye ni dan wani abin face kana so na, ba zaka iya ba sai da ni! Wannan bakar ba zata girgiza ni ba!

Barci Agaishat take saman kujera a takure, da alama tsoro take ita daya, 

Haka ya shigo dakin ya kai dubansa inda take,

Bai tasheta ba, bai yi mata magana ba ya fice ciki ya duba wajen abinci ya ga bata ci ba,

Bai tasheta ba ya fito ya nufi bangarensa ya kwonta domin ransa a bace yake, indai zai tasheta ne dalilin bata ci abinci ta kwonta ba yana iya bata mata rai,

Kamar yanda ta saba kiraye kirayen sallah suka farkar da ita, da kyar ta iya mikewa domin kwoncib da ta yi du jikinta ya yi tsami,

Dakinta ta zarce ta je ta kimtsa dan yin sallah,

Koda ta gama sallah zama ta yi ta tsurawa waje guda ido, zuciyarta ke mata fada, ba na komai ba sai na ta yi sabko, ya zata damu haka da son ganninsa bayan ta san ba ita daya gareshi ba? 

Ita fa zuwa ta yi ta tarar da wata, idan ta tsiri damuwa da jinsa a kusa bata so kanta da yawa ba kuwa?

To aman ai sai ya min bankwana ko? Wayar da ya yi ita kawai ta shaidan inda zai je, daga shi bai ce min komai ba,

To meye dan wannan a halayan wardugu? Ke dai ki kiyaye,

Wata zuciyar ta bata amsa,

Dan haka a hankali ta mike ta ninke salayar, yau kam sai ta ga masu gyara gidan nan, a kulun kafin ta fito daga sallah an yi komai an gama, har kulun mamaki take, danma ita ke shiga kicin abinta, aman tana kyautata zaton da masu aiki a gidan, dan kuwa har yanzu tunda ta shigo bangaren nan nata kafarta bata fita ba, du sati Ayya ke turo mai kitso ta zo ko ta yi mata kitso ko ta mata gyaran kai, kunshin kafarta da hannayenta kuwa da sun fita ake dora wasu domin wannan lanlan ne na zamani mai saurin fita,

Labule ta dage ta leka sosai,

Ai kuwa sai shige da fice suke kowa da abubuwan aikinsa, hakan ya tabatar mata da har cikin ma da masu gyarawar kennan, ita dai abinda take yi da kanta saka turaran wuta, wanda take yin garwashin a kicin ta saka da toka mai zafi ta saka dan turaranta ya game dakunan da kamshi,

Murmushi ta yi ta je ta salo wankanta,

Tana gama shiryawa cikin doguwar atamparta an yi mata dinki simple, sai hannayen ne kawai akaiwa ado , ta daura dan kwalin atampar ta tsaya gaban madubi tana kallo,

A hankali ta sauke ajiyar zuciya a fili ta ce” Ba sofona, ina yawan mafarkinka, Allah ya sa lafiarka kalau ka ji? Zan so ka ganni Ba, tabas maganarka haka ne, birni ga girma ga abubuwan girma, birni mai dauke da wardugu da Ayya da kuma Walyn, 

Birni mai mota mai jirgi,

Birni mai kalolin fata ba biyu kawai ba,

Sai da ta gama kalon kanta kafin ta yafa mayafi saman shigarta ta fito a hankali ta nufi wajen abin turaran wutarta ta dauka ta nufi kicin,

Sai da ta hada shayi ta zuba a dan cofi ta dauko biredi mai beurre sannan ta kuna garwashin ta hado turaran wutar ta fito da su a hannunta ta dorashi wajen da yake gana dakin sannan ta je saman cafet ta zauna ta yaye mayafin ta ajiye ta zauna ta fara karyawa,

Tana tsaka da ci ta ji kanshin turaransa hakan ya sa ta yi dan tsai kafin ta dago da dubanta,

Cikin shirin zuwa aiki yake, yannayin fuskarsa ba fara.a hakan ya sa ya shaida mata da ransa a bace yake,

A hankali ta kawar da dubanta daga fuskar tasa ta ajiye kofin glass dun dake hannunta ta mike daga zaman da ta yi tana goge hannunta da tissu duda ba abinda ya yi, ta kai dubanta wajensa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button