BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 71 to 80 (The End)

Dubanta ta maida wajen Alhinayet ta ce” Alhi, bani wayarki na yi kiran Ayyana dan Allah, na fada mata halin da ake ciki na kuma fada mata ta biyo min da hijab dina kin ga dan kwalin ya fadi fa,

Da sauri Alhinayett ta dubi kanta, Lah kanta ba dan kwali, gaba daya kyan gyaran gashin ya fito sosai ta yi wata yar caras da ita,

Ai kuwa wayar ta mika mata tana ayyana Wardugu sai ya hada daga ni da a aurena ne kika fito a haka da ke din ya ci ubanmu

Number Ayya dake  kwakwaluwarta ta dora tana satar kallonsa, mamaki take wai kallon nan da ya same shi  na meye? Sai ya tsurawa mutun ido tamkar yana kallon tv ko waya, kuma ba abinda ya dame shi dan kun yi ido hudu ya kawar da dubansa? Aa sai dai kai ka kawar, wannan ai musulunci ya hana irin kallon nan tsakani da Allah

Shi kuwa duban da yake mata, yana so ne lale lale ta iya yarensa na kallo, yana so idan ya dubeta ta gane me yake nufi da dubansa ba wai ya tsaya yana ta haikar baki ba, yana so ta gane wannan shigar batai masa ba, baya so, hankalinsa, ransa, nutsuwarsa duka yana nema ya rasa a lokacin da ta fito a haka, ku ji fa hankali kwonce yltana danna waya ta kara tana zubawa mamanta shagwaba ba ruwanta da wa zai kala ko me mutun zai kiyasta a kanta a ransa?  Yana kallonta ta kashe wayar ta mikawa Alhinayet ta maida taguminta ,

Sai damun mutane take da tambayar me ya samu Walyn, ko meye damuwarta a ciki? Shi kadai ke fadansa a cikin  ransa kafin ya yi kwafa yana tunanin idan ta kai shi bango bai san irin jijigar da zai mata ba, 

Ba.a wani jima sosai ba mahaifiyar Walyn ta zo, tsakaninsu da Ayya kuwa bai fi minti biyar ba, sai gata itama an tukota a motarta 

Kamar ko yaushe cikin kanshinta da lafayarta har kasa da san saukakun awarwarayenta hannunta dauke da leda kamfanin Butique wace ta sako hijab din yarta,

Salama ta yi masu kafin ta tambayi mai jiki?

Nan suka shaida mata docter ne ciki , yace ya daidaita numfashinta aman cikin ruwan da ya jona mata da na baci wanda zai saka ta farka a hankali,

Ayya ta yi fatan Allah sawake, ta tambayi daman bata da lafia ne? 

Su kam basu da wannan amsar, hakan ya sa ta bude hijab din, maimakun ta bata ta saka sai ta budeshi da kyau ruwan shadar jikinta ne, ta juya Agaishat dake tsaye kusanta ta kama gashin kanta gaba dayansa ta hade shi ta yi masa dan tuntun madaidaici sannan ta zira mata hijab din mai hannu da wani dantel a jikinsa sannan zif ne da shi dan karami wajen wuya wanda mutun ke ja ya kama fuskarsa ,

Hijab din ya yi kata kyau das a jikinta sannan tsayinsa har kasa sosai,

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kawar da dubansa daga wajensu,

Docter ne ya fito da dan sauri yana tambayar ina wardugu?

Daidai nan su Mu.azam suka karaso , 

Wardugu ya nufi wajen docter, Inda Ayya ta je wajen su Alhinayett ta ce” ku kuwa me kuke har yanzu a nan ? Ku zo maza ku tafi gida haba dare ya yi,

Alhinayett zata yi magana wata nurse ta fito da gudu ta ce” Docter tafa tsoge allurar ruwan kuma du wanda ya je kusanta doke shi take,

Da sauri du suka nufi wajen hankali tashe, 

Wardugu ya saki wani murmushi yana kallon yanda suke rige rigen shiga dakin, 

Kansa ya girgiza ya bi bayansu, 

Mahaifiyarta ce ta karasa da sauri kusanta yanda take rusa kuka tana fadin” Walahi, sai na kashe su, daga shi har tsinaniyar bakar fatar nan! Da raina ba.a yi ba, ba za.a yi ba yarinyar da Wardugu zai kira da *ORRONUR* ba, ita ita Wardugu zai ciwa mutunci?

Daneta uwar ke faman yi karta mike, sannan ta tambayeta wai meye? Meye? Me aka yi?

Walyn ta daga jajayen idannuwanta ta sauke saman mahaifiyarta ta ce” a wajen partyn banzan nan da suka tsara ne ya rakata wajen zama bayan ni ya barni nan zaune ni da nake matarshi, shi ne na tambaye shi wacece ita? Wani matsayi ke gareta da har zai lakaba mata wannan sunnan? Yar gidan waye ita?

Shi ne yace da ni wai *RANSA CE!* 

dif dakin ya yi Agaishat dake bayan Ayya tana dan lekowa idannuwansu suka hade da na Walyn,

Wani kukan kura ta yi ta ture mahaifiyarta ta taso da gudu da karfin balaki ta nufi wajen Ayya tana furta” Walahi sai na ga ubanda ya tsaya maki, ko wani irin boka ko malan ya ci…….shi! Ya dura ashar mai yaji????, shegiya bakar fata mai bakar aniya, mijina ya fi karfin buzuwa banza jahila! 

Kafin take isawa ta ganshi tsaye, tsaye tsakaninta da Ayya da kuma Agaishat, kikam ya tsaya ya tsura mata ido 

Zagaye shi ta so yi ta karasa wajensu, sai dai ya riko hannunta ya yi mata turawa daya da ta saka ta je can ta fadi,

Daga kafarsa ya yi ya tunkareta da wani irin sauri da niyar kasara wata gaba ta jikinta

Sai dai muryar Ayya ce ta dawo da shi daga wannan niya tashi wace du mazan wajen suka yi gagawar tarar shi, rike shi sukai suna faman bashi baki kan kar ya yi, ko ba komai mahaifiyarta a wajen a zaune, idan ita ta saki baki tana abubuwa irin haka shi ya ci girma,

Wani irin huci yake saukewa inda ya bi umarnin Ayya da ta nuna masa hanyar fita,

Shi ya fara fita sannan suka mara masa baya inda ta fashe da kuka da wani ihu ihu tana munana mangangannun kan ba dole ya tafi ba, ita ga mabaukaciya ai dole a bar mata waje, daman ita ta san Ayya bata taba kaunarta ba, gashi ta kawo masa karuwa har gida ana cin amanarta, ita kuwa zata ga yanda za.a yi soyayar nan!

Mahaifiyarya ce ta daka mata wata gigitaciyar tsawa kafin ta ce” dan ubanki ta yaya kikai masa tambaya kan wacece itan??

Kwashe du magangannun rashin da.ar da ta yi masa ta fadawa mamanta, inda ta shiga bata karfin gwuiwar cewa” ya fada maki haka ne dan ya tunzura ki ke kuwa kika hau banza, ko ni kika yiwa rashin kunyar nan ai sai na baki haushi bale Wardugu, me zai yi da wannan mumunar halitar in ba shirmen kishi da ya rufe maki ido ba? Ya fada ne dan ki zubda haukan, kin kuwa zubda hankalinki ya kwonta! …..haka ta yi ta dorata kan yayi haka ne dan ya bata mata itama aman me zai yi da Agaishat?

Tunda suka kama hanyar gidan ayya kansa ke jingine jikin madubin motar yana sauraron ajiyar zuciyarta , domin ta tsorata da gannin kamar ita walyn ke farauta, 

Shiru motar ba mai kwakwaran motsi har suka karasa gidan Ayya,

Shi ya fara fita ya nufi falon ayya, kafin ya shiga ya iya sabule takalman kafarsa sannan ya ciro rigar dake cikin zanzaron jikinsa ya yi tsaya yana mai jin kansa tamkar zai rabe gida biyu!

*BAKA KYAUTA MINI BA!* 

Ayya ta fada a lokacin da suka shigo da Agaishat, tana kallo Agaishat ta nufi dakinta,

Kanta ta juyi wajensa , ya dafe kai yana jijiga kafarsa, balaki na cinsa, da wanda zasu yi kawai yake nema, ta ce” Baka kyauta min ba, ka san sarai halin matarka dan me zaka sako min yarinya cikin shirmen ku? Me ya hadaka da fadin wannan maganar a kan yarinyata a wajen matarka?

*DAN INA SON TA* 

Maganar ta fito daga bakinsa da amo mai karfi karfi,

Da sauri ya juyo wajen Ayya ya taka har zuwa inda take zaune ya duka ya dora kansa saman cinyarta,

Zuciyarsa ce ke wani irin dokawa ya ce” *Ayya, Wayo Allahna Ayya zan mutu, Ayya mutuwa zan yi, Ayya zafi nake ci a nan*

                         ????

???????????????? *BAK’A CE* ????????????????

                            Na

                     *SAJIDA*

                          7️⃣5️⃣

*KUTKALE* (PRISON)

*AURE YAKIN MATA NE*

*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button