BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 71 to 80 (The End)

To albishirinki, walahi ni na fada maki, du abinda ya kasance shi kulun a fili a bude yake komai darajarsa a hankali take raguwa har ya kasance ta bace bat! 

Shigar kananun kaya, akoy lokaci, ba ina nufin kowani dare ba, no , aa, lala! 

Ki sayi masu tsari, masu ma.ana , masu kai,

Masu taushi! 

A cikin gidanki Agaishat, ki kasance cikin shiga ta kamala, ki ringa yawan yi masa rowar ganninki gaba dayanki arha, 

Agaishat, ki ringa saka riga da zani da dan kwalinki, ki yi sasaukar kwaliyarki sannan ki zauna cikin kanshi, 

Ki ringa saka sket da rigarki na atamfa, ki ringa saka doguwar rigarki au ta atamfa ko abayoyinki, ki ringa nada saharinki, ki ringa hawan lesh da shadarki kina zamanki, ke wani lokaci ki yi sasaukan shiri abinki,

Ki ringa daukan lokaci kafin ki yi masa shiri na kananun kayan, ya kasance a ranar yana kusa, ki saka abinki , ki juya a gabansa,….. Agaishat zaki baiwa wani labarin mahinmancin hakan, mijinki zai kasance yana mai jin zumudin riskar ranar da zaki hade masa cikin shirin nan, sannan koda lokacin da zai ziyarce ki ne, zaki ga zai warewa wannan lamari mahinmancin da za yana nuna maki, ( iyayen mu, na zaunar da mu ne, su yi mana huduba, fila fila, shin da wada take yarena ta tabatar? )

Sosai Ayya ta yiwa Agaishat nasiha, gargadi, ta ankarar da ita zaman duniya, dama hasashen na auren da take, kafin ta nanata mata maganar cewa *AGAISHAT* ,tabas kyau, fari, mulki, arziki, na jan soyaya, 

Sai dai ki sani *ZUCIYA NA SON MAI KYAUTATA MATA* , 

Wannan kalma kuwa , ta tsaye mata a rai kamar yanda sauran suka tsaye mata,

Haka aka wuni shagulgula kamar ba gobe, 

Sosai Ayya ta gayaci mata, mata kuwa sun amsa kira, inda aka wuni ana tafiar da taron yan gayu,

Kai amarya, ba.a tashi shirin amarya bama sai wajen karfe goma na dare, 

Ayya ce da kanta ke darwaye yarta, kafin ta mulketa da turaren Angel, 

Haka ta zaunar da ita ta saka mata kwali kadai a idannuwanta kafin ta damka mata shi a hannunta, 

Wata arniyar Lafaya ce ta nada mata saman lafiyayiyar doguwar rigarta ta atamfa mai ruwan ja da fari kar,

Ba.a saka mata dan kune ko awarwaro ba, takalmin kafarta kansa wani plat ne, 

Dirar motoci suke ji , tun suna hasashen za.a dakata abin gaba kawai yake,

Labule Alhinayet dake tsaye cikin shigar wata dakakiyar shada ta daga,

Gaba daya sai da tsigar jikinta ta tashi, 

Hasbunalahu wani.imal wakim,

Shi ne abinda ta furta a lokacin da ta hango motoci layi biyu, kowace tana kilyoten yan wutocin gaba, kowace da soja tsaye a kusa da ita, 

Sun layu gaba dayansu suna ta tafi ana shakiyanci irin na sojoji a cikin yannayin farin ciki,

Ta tsakiyarsu yake ratsowa a lokacin da Alhinayett ta hango shi ta saki wata buda tana kada harshenta ta shiga kwasar shoki, 

Wato wani irin shirya daukan amarya ne aka yi wanda sai wanda ya gani,

Haka Ayya ta kamo hannun Agaishat dake ta hawaye tana jin wani irin lamarin a jikinta wanda bata taba ji ba a aurenta na farko,

Ya Allah, ya Allah,

Ayya na fitowa da ita daga dakin nayake ainayin nata aka shiga guda ana zuba mata kudi,

Ayya ta riketa da kyau suka shiga saukowa daga matatakala inda ta shiga neman aminiyarta dan ta mika Agaishat dakin mijinta,

Tsakiya suka saka Agaishat suna tarairayota, 

Alhinayet kam har jikinta rawa yake , domin gaba daya wajen fa ba dama, muryar sojoji ne suna fadin”Hei Hei Hei Hei, 

Inda Wardugu ke takowa a kafarsa, jikinsa sanye da kakin soja marroon , wandon da kadan ya zarce kaurinsa sannan ya rike shi daga kasa, rigar kuwa baka ce jikinsa aman bai sakata cikin wandon ba , janta ya yi ya dorata saman yar karamar bindigar dake tsatsonsa, sai ranjes maroon waro takalmin sojoji, rigar mai karamin hannu ce , hakan ya sa damatsunansa du a waje,

Du taku da zai yi sai kura hei tun karfinsu murya irin ta garada, sannan su yi wata yar rawa da kafarsu ta dama baki dayansu a haka har ya karaso wajen yan matatakalar da zai taka ya hau kafin ya shige dakin Ayya , aman sai ya ja ya tsaya,

Daidai nan su Ayya aka bude masu suka fito da amarya,

Gaba daya wajen ya kwashi wani busa na sojoji kafin a karashe da fadin *GENERAL HEI GENERAL HEI* 

Tsura masu ido ya yi daga inda yake,

A hankali ya dora kafarsa ta hagu saman abin takawar na fari, kafin ya lankwashe kafar ya kasance gwuiwar kafar tasa ta hagun a kasa, sannan ya matso da ta damar saman na gaban ya dorata, ya yi irin taugunon nan da maza suke yi dan tambayar hannun budurwarsu (kasar larabawa da turawa),

Wani irin ihu wajen ya dauka a lokacin da ya mika hannayensa baki daya kan a bashi, ya zo a bashi………..

To fans saura kiris bilahi????????????????????

???????????????? *BAK’A CE* ????????????????

                            Na

                     *SAJIDA*

                          8️⃣1️⃣

*KUTKALE* (PRISON)

*AURE YAKIN MATA NE*

*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*

daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA*  in sha Allah,

……..kar ku bari a baku labari…..

Dakatawa Ayya ta yi, kafin ta dubi tarin jama.ar, 

Dubanta ta kai wajen mutanen da suka wunnin mata sannan ta kara duban yan matan dake wajen wato kannen Alhinayett da aka wuni da su,

A hankali ta yafito Alhinayett, ta karaso inda ta yi mata radar du rintsi a sada Agaishat dakinta da ita,

Ai kuwa Alhinayett ta amsa, kafin Ayya ta kama hannayen Alhinayett ta karasa kusa da Wardugu,

Hannunta na dama mai dauke da jan kunshi dan kadan ba mai yawa ba ta dora saman nasa na dama kafin a hankali ta ce” ka riketa mudin ranka War….,

Wardugu ya rike hannun da kyai inda ya kai dubansa da kyau domin jin wani laushi da hannun ya kara kan nasa na da, dubansa ya kai wajen mahaifiyarsa a hankali ya furta” Allah ya tabatar maki da shiga aljannah,

Aminiyarta da Alhinayett da Agaishat kawai suka ji, dan haka suka amsa kowane daga bangarensa, inda ya mike a hankali ya karasa hawa ya matsota jikinsa ,

A fakaice ya duba irin daurin lafayar da akai mata, aa yau sun yi abin kansu, an yi mata daurinnan na saman kirji wanda baya nuna surar mutun, dan haka ya sauke ajiyar zuciya ya sakali hannunta da kyau inda ya zame mata jagora yana takawa a hankali tana bin sahunsa ,

Sojojin gaba daya bindigoginsu suka daga sama kafin daya daga cikinsu da ya fi murya ya ce”REPOS! 

Gaba daya suka sauke

A hankali suke takawa, inda Alhinayett ke bayansu, sai yan matan suma suka rufa masu baya , sai iyayen da zasu rakata domin fir Ayya ta ki ta saketa haka kawai,,

Motar da zata kaisu ce ta karaso ta tsakiyar sojojin, nan Wardugu ya bude ya sakata gefen dama kafin ya zagaya ya shige gefen hagu,

Mu.azam, 

Shi ne abunfa Wardugu ya fada a lokacin da ya ga Mu.azam ne zai tuka su,

Mu.azam ya tsare shi da ido ta jikin madubin hakan ya sa ya yi shiru ya zauna da kyau yana duban yanda kowa ya je ya shiga mota suka dauki hanya,

Shiru ne ya ratsa motar, inda gabanta ke dukan tara tara, me? Mu.azam? Shi ne zai kaita dakin miji? Lale Mu.azam, kai itafa har yanzu bata san komai ba, kuma bata da niyar sani! 

Haka dai ta yi shiru har lokacin da Wayar Wardugu ta dauki tsuwa,

Dagawa ya yi ya kara a kunnensa,

Ai kuwa a dake ya ce” ka gane, abu daya za.a yi da su su dan daidaita halayensu, dangina ne na san meye zuciyarsa, du wanda ya kashe ka saka bakin bindiga ka harbe shi a tsakiyar ido! Du wanda ya jigata wani, ka jigata shi, hakan zai sa su daina fadan da zasu jiwa junansu har a kawo su asibiti,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button