BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 71 to 80 (The End)

Zan so ki saurare ni, ki dauki dabi.u kyawawa, ki rungumi aurenki, zan so ki zowa rayuwarsa da sauyi, ina da kyakyawan zaton ke din zaki iya tankwasa shi kan wasu lamuran na yau da kulun, 

Agaishana , *ina rokar ki da ki tsaya ki yi tunani ki ganni, idan har ba zaki cutu ba, ki amshi auren nan, in sha Allah zaki ji dadinsa*

Agaishat da ta yi lamo tana sauraron Ayya ta dan dago da kanta , jikinta har rawa fa yake ta ce” Ayya, Ayya, matarsa, Ayya shi din kansa, ya ji wannan abin? Ayya zai sumar da ni ne, Ayya ni din me? Ni a wa? Ayya matarsa…..

Ayya ta saki murmushi tana kara shafa kanta ta ce” *MATARSA*  bani da wata damuwa da ita, du yanda ta ga zata kwaba tuwonta ta ci , tukunyarta ce, abinda na sani shi ne, Bama hada mata gida guda, komai talaucinka indai ka ce mace biyu zaka yi ko sama , to fa kowace gidanta daban,

Sai abu na gaba matarsa, ba ruwanki da ita, sannan koda wasa, ko da wasa kar na ji, kar na ga tsoronta a tare da ke, na me? Aa, ba zamanta zaki yi ba! 

*SHI KUWA* baki da damuwa da hakan,

Daga nan Ayya ta yi shiru, bata kara mata haske a abinda take nufi ba, 

Baiwar Allah ajiyar zuciya kawai take saukewa, bata da abin cewa , ta san zata je ne a kara sakota ta dawo, toh a sakota mana, an saketa a auren so ma bale na hadi? Nan baci ya aniya sandarta har ya dauketa, ita fa ta sakwa kanta dangana, abinda ta sani daya ne, bama zata ishe shi kallo ba bare har ya wani zauna da ita, ita fatantama kar ya karya mata kafa ko hannu dan haushin an aura masa ita ko ya jirkice mata kanta,

Jin ta dan kara nauyi ya saka Ayya dubata, 

Tausayinta ne ya kama ta, ta san dama da wuya ta yi mata wani diban albarka, aman bata yi tunanin ko kuka ba zata yi ba, yarinyar na da hakuri, sannan da alama zata bata hadin kai su baiwa marada kunya,

Gyara mata kanta ta yi da kyau kafin ta kuna mata ac ta dauki jakar kudin ta fice,

Mai aikinta ta kirawo ta aiketa kasuwa dan karo mata itacen magarya, bata ga ta zama ba, yarinya da kishiya gashi da alama tsoron kishiyar take dan haka dole ta zagine, ga irin yanda Wardugu ya yi kundumbala ya ce yana sonta ai sai ta dagewa yarta!

Walyn ta ga rana, Wardugu ya ware mata dukan karfinsa sai da ya kai bata koda iya daga hannunta kafin ya mike,

Bai koma dakin ba, ky din mita kawai ya dauka sai computern aikinsa ya fita,

Motarsa ya shiga yana mai jin kyankyamin kansa ya dauki hanyar gidan Ayya inda gabansa ke dokawa yana tunanin yanda zasu karke da ita,

A lokacin da hancin motarsa ta shiga gidan ya tatara du wani tunani ya watsar kawai ya nufi falon,

Tsaftsaftsaf kamar koda yaushe, 

Bai tsaya neman kowa ba ya shige dakin da mu.azam ke sauka ya cire kayansa ya shige bayin da ya tabata a tsaftace take ,

Tsarkake kansa ya yi kafin ya fito ya nufi wajen da kayan ke cikin dakin,

Tsaye ya yi yana duban kayan, anya kuwa zasu yi masa? Shi kuwa ba zai mayar da wadacen ba, da kyar ya lalubo wata jalabiya fara kar sabuwa ya saka ya caje kansa da kumb, ya dauki turare ya fesa sosai ya tsaya gaban mirror, 

Sakayau yake jinsa, ya rage nauyi dan haka ya fito da niyar kira da wayar Ayya kan a kawo masa waya, 

Dan dakatawa ya yi sakamakon hango Ayya da ya yi tana kallon wajen dakin, sai bayanta ita kuwa tana tsaye da alama wani abu ne a hannunta, 

A ransa ya ayana , ya Allah, tana son saka doguwar rigar da ta dan dara gwuiwarta ko dan ta san tanai mata kyau ne?,

Ayya ce ta ce” Wardugu? Yaushe ka shigo ?

Tea din da ta sirba ne ya so sarketa inda ta samu da kyar ta hadiye shi tana zaro ido tana duban Ayya, ta kasa waiwayawa ta kasa zaune ta kasa tsaye sai rike cofin da ta yi da kyau tana jin zufa na neman karyo mata,

Ayya ta dubeta ta yi murmushi, ta ce” ehem, me ma kika ce? Ke dai ina wayarki ina wayarki? Mu ci gaba…. ta fada tanai mata murmushi, domin tun da ta farka bayan magariba ta shiga rigimar ita ina wayarta ne wai? Ina aka kai mata wayarta ? Wa ya ga wayarta? 

Salama ya yi kafin ya shiga yana duban yannayin Ayya,

Fuska sake ta amsa shi tana fadin” War, baci ba ka yi ?

Shi kam wata kunyarta ce ya ji ta lulube shi, dan haka ya zauna  saman kujera inda yake ta kokowa da idannuwansa kan su yi hakuri kar su dubeta,

Ayya ta kaleta ta ce” Agaishar kawowa yayanki ruwa,

Kamar jira take a kunnata ta juya da dan sauri ta shige kicin,

Sai da ta bacewa ganninsa kafin ya tataro dukan jarumtarsa ya gitse ya hade rai tamkar ba shi bane ya kare mata yaren Wayo Allah zuciyarsa,

Ayya ta dubi yannayinsa kafin take sakin murmushi, wato ita zai rufewa tabarmar kunya da hauka ko? Kunya ta ishe shi shine ya aro jarumtar wawa ya afkawa kansa,

Cikin wayewa ta datijuwar da ta san kanta ta ce” Wardugu zo nan, 

Ta nuna kusa da ita sosai,

Wajen ya bi da ido, kafin ya mike ya koma ya zauna yana kakawar da kai,

Ayya ta ce” Wardugu, barkan mu ko?

Kunya ya ji ta kara dirar masa dan haka sai ya sada kansa, kafin ya dago a hankali ya ce” Ayyana, hakuri????????

Ayya ta sakar masa murmushi kafin taa ce” me na ce ni? Ina cikin farin cikin hakan, sai dai me ka tanadarwa zaman y’ata a gidanka? Sannan wani gida zaka kaita? Ka san dai ba.a hada mata ko?

Wardugu ya yi tsai yana dubanta, shi kam yaya zai yi ya raba Ayya da maganar al.adun nan ne? Shi ya so ya hada su, a hankali yau da gobe wata rana zasu yi zumunci, aman yanzu an ce ya raba su,  yaushe Walyn zata yi hankali?

Ajiyar zuciya ya sauke bai ce komai kan lamarin ba, Ayya ta ci gaba” za.a yi biki kamar yanda ake yiwa kowace yar gata, za.a kai amarya kamar yanda ake kai kowace amarya, za.ai mata gyara , zaka yi bajinta irin namu domin da namu da nasun du kusan iri guda ne, Wardugu harta da garar namiji ban cire maka ba , sai ka yiwa y’ata, 

Ta karashe tana gimtse fuska , daidai Agaishat ta dawo da ruwa cikin goran Awa da kofi na kwalba , abinda wardugu ya fada ne ya sakata jin ba dadi, duda ta san zata fuskanci hakan,

Warsugu yana duban Ayya ya ce” aman Ayya , sai nake gannin kamar ranki a bace kuma kina dariya, Ayyana, Marahut ya daura auren nan, kin ga kuwa tilas na yi masa biyaya,…..

A hankali ta karasa ta ajiye ruwan ba tare da ta tsiyaya ba ta juya zata fice a dakin ta je tsakar gida ko zata ji iskar Allah ta ratsa hancinta yanda ya dace,

           *KE*, shi ne abinda ya daki kunnenta da kakausar murya,

Wa zai cewa ke a wajen da daga ita sai Ayya sai shi? 

Dakatawa ta yi, a kasan zuciyarya kuwa fadi take, walahi da wani gaulan ne sai na bala masa harara wai wani ke, aman ba komai ba komai????,

*Ki je dakin ki* , ya fada yana kawar da kansa daga dubanta inda ya ji ransa ya baci a tsakar ransa,

A hankali ta juya ta haye sama ta nufi dakinta,

Dubansa ya maido wajen Ayya ya ce” Ayya, ya zaki bari yarinyar nan tana yawo haka ne tsakani da Allah? Idan da kin ce igiyar wa ke kanta yanzu fa? Ayya, gidannan da maza fa, ga masu gadi, ga sojoji, ga direba, Haba Ayya,

Ayya ta hade fuska ta ce” toh ubanna, nace toh ubanna kawo min duka, 

Dan yatsanta ta nuna masa ta ce” Wardugu ka kiyaye ni, bilahilazi na fika ciyayi, kai ku ji kin yaro da rainin hankali, ka je ka gindaya mata dokar mana dan raini ka sakani gaba bayan ka gama raina min wayo da maganar wai ka yiwa Marahut biyaya ka korar min y’a, sannan ka rufe ni da fada? Sauran duka sai na gane ba za.a iya taroka ba! 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button