KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Mom kam batace kala ba kallonsu kawai take tana ganin ikon Allah na yadda zakiyya ke Abu Kamar Mara lafiya sannan kuma me yazeed zaiyi.
Yazeed bai nuna alamun ransa ya baci ba illa gyara tsayuwa da yayi hankali kwance yace kika ce ban isaba Toh ke a suwa? Ko ince why bazanyi aure ba😕?
Babu abinda zakiyya ta tsana Kamar tayi banbami taga be batawa mutum raiba
Sai tace tabdi jam eehh lallai why ma zaka ce?….to because I said so kanaji na ko yazeed? au Wai dama dagaske auren zakayi ? Wallahi za’a yi tashin hankali.
Kallonta yayi with an expression of I thought u don’t care about me,all u care about is your boutique,boutique, boutique.
With a less concern yace eh aure zanyi jibi ma kuwa thank goodness kinzo a dai dai so no need to stress my self.
Tsalle ta daka tace wallahi ni zakkiya nafi karfin ayimin kishiya god forbid ai ba haka mukayi zaka kara aure ba….na haramta maka yin aure a gidannan yazeed da fatan kana jina?ta fadi haka tana zazzare ido tare da huhhura hanci Kamar maiya
Mom ne tayi carab tace
Hey…hey…hey kikace kin haramta masa?and who the hell do u think u are ?ke asuwa kunun bayan ludayi….just a zero behind a decimal point….ran mom yayi mugun baci
Iyee, its all my fault da bansani Anyi wajen dake Ba kamin a Shiga da ita, shiyasa kika sani bakin magana. Listen to me very attentively! Idan kika sake kikayi mana tashin hankali a gida ki tabbata zaman ki ya Kare. Banason in zama sanadin daba aure amma abin naki ya isa. Kin fara wuce gona da iri.
Yazeed ne ya riko mom yace calm down sweetheart bade aure bane Anyi angama karki damu kinsan I love u ko?muje dakikinki. Haka ya tisa mom a gaba har dakin ta. Tanaji Kamar ta yarfawa zakiyya tafi amma batason ta zubda girmanta.
Zaunar da ita yayi ya bata ruwa sannan yayi assuring dinta Cewa ba mai hanasa aure sai Allah daganan ya fita…
Zakiyya kuwa tasan ta tabo Dan yadda taga ran mom ya baci babu abinda zaihana tasa a saketa she must calm herself down. Taso tayi musu hauka amma bazata iyaba saboda tanason igiyan aurenta
Haka taje dakinta aguje tahau watsarda abubuwa tana fasawa hannunta na jini kamin ta fada kan gado ta fashe da wani matsanancin kuka…..
Yazeed ne ya turo kofan dakin ya shigo
Tasowa tayi attachment dinnan duk ya wargaje tana sending masa murderous glare ahankali yazo ya zauna akusa da ita being conscious with the glasses kar ya taka.
Hannunta ya riko ta warce ya kara rikowa zata warta ya rike gam yace haba my zakky uhm….yanxu shine kikaje kikayi fada da mum kinsan mahaifiyata ne tanada hakki akaina ya kikeson Nayi kinaso na haukace ne?
Rungumeta yayi kamin yaci gaba da fadin na dawo ko kiss ban damu sai kihau yima mahaifiyata fitsara kin kyauta kenan?a hankali ta girgiza kanta yace ai kinsan ko Nayi auren ke nakeso waccan zabin mom ne ko?ta gyada kai yace promise me zaki bawa mom hakuri tace on one condition idan kayi auren bazaka hada gado da matar ba yace ai wannan ko baki fadaba kinsan haka yake Insha Allah.
Tace to nima zan bada hakurin yace good daganan aka Shirya kuma akayi wani duniyar.
Jamal kam sune kirjin biki bai samu haduwa da yazeed ba sai Washe gari Inda za’akai lefe
Your one and only karamarsu babbarsu
Miss untichlobanty💕
8 SEPTEMBER, 2019.
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty💞: ðŸ†ðŸ†KURUCIYAR MINALðŸ†ðŸ†
🌹by @mzz_untichlobanty🌹
CHAPTER 24
Kamar yadda kuka sani yau za’a kawo lefen minal
gidansu ya cika taf da dangi,Yan uwa da abokan arziki kai har makiya ma sunzo domin asamu abin fadi acikin gari
Ana zazzaune akaji sallaman kawayen mom da aunties din yazeed sun iso firfitowa akayi ana musu maraba tare da shinfida musu dardumai
Gaggaisawa akayi da fara’a da mutunci Yan gulma da tsurku tundaga ganin masu kawo lefen sunsan minal ta cafka tayi sa’a zata Shiga gidan da akwai gida mai maiko
(Wannan yana daya daga cikin kuskuren da mutane keyi Suna ganin idan har ka auri me kudi ko me kyau Toh kayi sa’a saide abin Ba haka essential qualities da ake bukatan mutum ya lura dasu shine:
1.shin wannan mutumin ya kwantamin ?
2.shin yanada addini?
3.zai iya ciyaddani da halal?
4.shin ‘ya’yana zasuyi alfari dashi amatsayin ubansu?
5.shin zasu gode min na zabanshi amatsayin baban su?
6.shin yanada akida mai karfi
7.is he loving and caring?
8.will always support me?
9.am I ready to live my whole life with him?
10.Does he respect my family
if those questions are satisfied then you are good to go,bawai idan ka auri mai kudi,handsome shine kayi sa’a Ba pls and pls Yan mata take note Ku core San duniya aranku Ku sank duk mijin da kika zaba Ba kanku kadai kika zabawa ba har da yaranku.Ku guji ranan da ‘ya’yanku zasu kalleku suce muku kun cucesu kun zaba masu mafi munin uba.
Suma mazan idan kun aurensu zasusan Dan me kuka auresu Dan kudi ko Dan allah.
Shiyasa yanxu rate of zaurawa ke karuwa soboda tun kafin adaura aure an rusa ta an kasheta auren a mace tazo. AKIYAYE)
Abokan ya abubakar ne suka fara shigowa da akwatuna har aka Shiga da 6 akwai nasu Kate ba,7,8,9,10………18 set uku kenan Wanda Duke da kalar fari,baki sai sky blue ga stones farare masu kyau ajikin ko wanne
Wasu set shida aka shigo dasu Wanda suke kalar brown guda 3 na inna,2 na baba sai 1 na kawayen Amarya
Kaya aka fara budewa hmm abin ba magana atamfofi 50,laces 30,material 25,an dinka goma goma atamfofi kuma ashirin ,English wears 25,Arabian gowns 30,sleeping dress 20,pants da bras dozen uku uku,takalma da jaka set 20,cosmetic traveling bag daya,gold jewellery 5 sets
Inna tace kayan sunyi yawa a rage Rabi sukace ah ah ai kaya sunzo in zasu koma to saide in ankawo amarya
Haka inna ma ta nasu tukuicin ban girma ;cin-cin,bakilawa,cake,doughnut, alkali,meat pie da samosa buckets buckets Wanda aunty fauzy ta bayar amatsayin gudun muwa sannan tahada musuda turaren wuta
Haka aka watse kowa yana farin ciki da annashuwa
THE WEDDING DAY
yazeed ne tsaye abakin mirrorn dakinshi zakiyya makale dashi tana wani shashshafa fuskanshi zuwa wuyanshi baby Wai da gaske auren zakayi,yace Toh zaky ba maganannan an gamata ba meye na dago da ita,zakiyya tace Toh naji amma kar ka manta kace bakasonta kuma bazaka hada gado da ita ba yace ina sane da wannan,happy now?tace yes
Fesa turare yayi kamin yayi mata peck a kumatu ya wuce
Zama tayi abakin gado tace koma wacece ke to kisani zaki kawo kanji cikin masifa ne Dan kishi dani sai an Shirya yanda ba’ayiwa uwata kishiyaba nima bazan zauna da ita ba😈
(Wannan banziyar akida ce mutum yace Wai Dan ba’ayiwa mahaifiyarsa kishiya ba shims ba’a masa ba karku manta Allah madaukakin sarki yace acikin suratun nisa’i
“Wa in kiftum allâ tuksidû fil yatamâ fan kihu ma d’aba lakum minannisa’i masna wa sulâsa war ba’a,fa’inkiftum allâ ta’adilû fa wahidatan au ma malakat aimanukum zalika adnâ allâ ta’ulû” 3:3
Allah madaukakin sarki ya umurci maza da su auri mata biyu,ko uku,ko hudu,idan bazasuyi adalci ba to su auri daya
Kinga da auren biyu ma aka fara kamin uku kamin 4 shikuma daya karshe
Kisani idan mijinki yace zaiyi aure kikayi adawa to kisani badashi kikeyi ba da Allah ne tunda Allah shi ya umarci ayi hakan
Dan Allah mata mu tashi munemi ilimi kuma muyi aiki dashi kodan gudun ranan da yayan mu zasu tambayemu Abu akan addini mutsaya muna zare ido mu Shiga kunya.