KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

????

Koda su lado suka karaso layin su godiya sabi’u yayi masa tare da cewa ya tafi gida shima zai wuce haka suka rabu suna shirya yadda zasuyi mugun sabawa minal idan suka sameta.

Yana raba hanya haka ya shigo har ya wuce sai yaga kamar akwai wani Abu da bai Saba gani ba a gefen itacen mahaifiyar sa. Rakani kashin sa (Nokia) ya ciro ya haska sai ya tuna ashe gari ma ya waye kalla yayi dakyau yaga minal kwance tana bacci hankali kwance. Yace daidai kenan wato kin tagaiyara ni? shine ke kuma zaki kwanta kiyi bacci ko? Toh gashinan Allah ya kawomin ke har gida. Dariya ya fashe dashi Wanda yayi sanadiyyar farkawar ta babu shiri ta fada cikin gidan daidai lokacin ummu amina ta sauke kunun sayarwar ta tana kokarin dauko su mukubur din ta na tuyar kosai taga mutum ya fadi Mata gida salati ta rafka yayinda minal ta buya a bayanta. Daidai lokacin sabi ya fado cikin gidan yana fadin ina take ? Ina ta shiga? Ummu amina tace lafiya zaka biyo yar mutane ku fadomin cikin gida da sanyin safiya? Yace kalli, ummu kalli goshina. Wannan yar iskar ce taji min.

Kallon ta ummu amina tayi tace a ah yar nan Dama kece? Sabi yace kin Santa ne? Tace ai jiya da muka fita nemanku ni da uwani, sai aka fara ruwa anan muka hadu da ita.
Kai miko min kujerar can ta zauna, yace? tashin hankali ai indai ni zan dauko kujera ta zauna saide ta mutu a tsaye. Ba rantse da wallahi idan na shiga na fito bata bar gidan nan ba, zan muku hauka. Yana fadin haka ya banka dakin sa ya shiga. Ummu amina tace dadin abun nice uwar ba kai ba, daga nan ta shigar da minal daki ta zaunar da ita ta bata kunun sannan tace Mata ta shirya su tafi kasuwar gwanjo ta siyo Mata kaya, ta daga kai alamun toh nan dai ummu amina ta gane cewa minal bata iya magana.

Haka suka tafi kasuwa ta zabo Mata kala 5 masu arha da rahusa sannan suka dawo gida. Koda suka dawo sabi bayanan dan haka ummu amina tace ma minal tayi wanka ta shirya sai tazo ta karbi kosai a kofan gida.

??

Yazeed yana zaune a dakin sa, ayush tana hada masa shayi yace little sis banida Mata ne? Ajiyan zuciya ta sauke tace Allah tayi Mata rasuwa bayan ta haifi safwan. Shiru yazeed yayi kamin yace safwan din ?ana ne? Ayush tace eh shi da yayan sa safwan. Murmushi yazeed yayi yace no wonder nakeji kamar ina missing wata ashe marigayiyar Mata ta ce. Ina yaran suke? Tace sun tafi school is already 8am fah. Yace kikace nine president na jeedmar group ko? Tace ofcourse bro Yace toh gobe zan cigaba da fita aiki. Tace okay but bro kasan ban Dade da dawowa daga karatu ba and you said zaka bani GM kace zaka shirya papers din kuma sai wannan abin ya faru. Yace no problem tomorrow zaki iya fara fita kece general manager na advertisement department. Tsalle ta daka tare da rungume shi tace thank you brother, ya shafa kanta yace you are welcome sweetheart.? Kanshi ne ya Sara jin kalmar sweetheart hakan yasa ya rike kansa. Tace bro lafiya yace nothing ki turomin sahir da safwan din idan sun sawo in gansu. Dariya tayi tace kaji ka fa bro wai ka gansu. Sai kace irin an siyosunnan yace toh ai na manta shiyasa. Dariya kawai tayi ta fice, tana fita daga side dinsa ta daka tsalle tare da fadin yes! Komai yana tafiya yadda nake so.

…….

Ummu amina tana cikin tuya minal ta fito ta zauna a gefen ta, Murmushi ta Mata tace har kin fito kenan? Minal ta daga kai kosai ta zuba Mata ta fara ci tana Mata hiran yadda takeson Allah ya bata diya mace. Tace sai gashi Allah ya bani ke, kinason ki zama diyata? Minal ta daka kanta.

Abinda basu sani ba yan anguwa duk sun taru, labari ya ratsa ko ina akwai sabuwar budurwa kyakkyawa a gidan ummu Amina kuma tana da ciki. Saurayi dake siyan kosan ne yace ummu amina wai a ina kika samo wannan kyakkyawar budurwar? Ummu amina tace kai banason maganar banza diyar nan tawa ce da na Dade ina rokon Allah ya bani ya kawo minaita har gida, kuma harma ina sa ran samun jikoki. Sunan ta Amina.
Kallon minal yayi yace wow nide minal baby zan dinga kiranta sannan yayi kokarin riko hannun minal din. Wani irin kallo ta banka masa tare da Jan dogon tsaki tana mai yin kicin kicin da idanu.
Yace tofah, ummu ai baki sanar dani cewa amina taki batada kunya ba ashe uwar tsiwa ce. Wani kallo minal ta aika masa ta ajiye kosan a gefe ta dafa kasa ta Mike. Wato za’ayi cakwakiya kenan, daidata tsayuwarta tayi ta dun?ule hannu wata Mata dake keken abinda ke faruwa ta window tace tooo, ashe aminar ba ta arziki bace wannan aminatun yar jagwal ce.
Take kan minal ya Sara ‘aminatu yar jagwal’ ke Mata yawo akai kamin ta yanki jiki ta fadi.

Nan fa…nan fa…nan fah. Au ashe ruwan biro na ya kare shiyasa na kasa ci gaba da labarin?

Karku manta kuyi SHARING sannan kuyi COMMENTING hakan ne zai nuna min tsananin kaunar da kuke wa littafin nan da ma mai littafin da kanta.

One love ? from your KARAMARSU? BABBARSU

Miss Untichlobanty ?

30th March,2020.

??KURUCIYAR MINAL??

?by miss Untichlobanty ?

INSTAGRAM : miss_untichlobanty
WATTPAD : miss_untichlobanty
TWITTER :miss_untichlobanty
TIKTOK: Untichlobanty

?CHAPTER 80?

RECAP

Yace tofah, ummu ai baki sanar dani cewa amina taki batada kunya ba ashe uwar tsiwa ce. Wani kallo minal ta aika masa ta ajiye kosan a gefe ta dafa kasa ta Mike. Wato za’ayi cakwakiya kenan, daidata tsayuwarta tayi ta dun?ule hannu wata Mata dake keken abinda ke faruwa ta window tace tooo, ashe aminar ba ta arziki bace wannan aminatun yar jagwal ce.
Atake kan minal ya Sara ‘aminatu yar jagwal’ ke Mata yawo akai kamin ta yanki jiki ta fadi.

CONTINUATION

Mikewa ummu amina tayi tana rafka salati tace na shiga uku aminatu lafiya? Fallawa saurayin Mari tayi tace kai ilu me kayi Mata? Uwani ta Kira ta taimaka Mata suka shiga da minal cikin gida.

Sabi yana karyo kwana yaga taron mutane, baya baya suka fara ja lokacin da suka lura yana tunkaro su. Ashar ga danna yace kai me kukeyi anan wajen? Yaran ne suka ruga da gudu yayinda samarin suka watse suna gunguni? su kuwa Mata yan tasha yan gulma suka dinga Watso magana ta batanci. Matar nan dake leke ta window tace kai sabi’u bamason iskancin banza, kai da uwarja bakuda aiki sai hada tarzoma. Yatsa ya nuna Mata yace ke talatu billahillazi la ilaha illa huwa idan kika kuma kirana sabi’u zanci… tam.

Kofar gidan su ya bankade da kafa har sanda ta karye ya shiga tun daga zaure yake dannawa mahaifiyar sa kira. Ummu! Ummu! Ummu! Tace kai wai lafiya kake Kira na haka sai kace kana bina bashi dalla ka fice kaje ka tuya mini kosai banson shirman banza.
Yace ummu ba nace kar na dawo na samu yarinyar nan a cikin gidannan ba? Tace tunda kai ka haiho ba. Wallahi sabi idan baka fice ka toya kosan nan ba zan fito daga dakinnan in ci maka mutunci. Uwani tace waikai sabi bakada tarbiyya ne? Mahaifiyar ka tana magana kana mayar Mata yace ke uwani babu ruwanki, kuma idan rashin tarbiyyar ne ai gara akan danki.

Juyawa yayi ya fice yana fadin mutane sai shisshigin masifa ko uban me ya kawota gidan oho. Kuma wallahi idan ba’a cire wannan yarinyar a gidannan ba zan muku hauka zan muku bari.

Koda ya fito zama yayi a kujeran yana suya yana banbami wai tsabar an rainashi za’a hadashi da suya. Wallahi babu abinda zai hanashi ketawa minal rashin mutunci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button