KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Shin abinda mom tayi ya dace?

Ina jiran COMMENTS dinku.

Love you all😘

Miss untichlobanty💕

19th October, 2019.
[1/11, 2:22 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by @mzz_untichlobanty🌹

CHAPTER 34

Tafe suke babu mai magana can lukman yace ina zamu ne Wai?sanda yazeed ya dau Yan sakanni kamin yace muje makarfi plaza inason insiyo waya ne.

Gyada kai kawai lukman yayi alamun ok,Sannan ya kara speed din motar.
Chan yace inajinka. Yazeed sarai ya gane me lukman ke nufi da hakan amma saboda hali irin nasa yace kana jina name fa?

Side glance lukman yayi masa kamin yace zaka fadamin koko?yazeed yace me kenan?tsaki lukman yace sai ka rike matsalarka tunda bazaka iya fadamin Ba.

Shiru ne ya karade wajen kamin can yazeed yace ka tuna wannan yarinyar ?

Smiling lukman yayi domin plan dinsa yayi wato babu Wanda ya kaishi fahimtar abokin nasa idan  ka nuna masa baka damu da Abu Ba to Anan ne zai dauki abin serious.

Luku yace wace yarinya kenan?yazeed yace wannan yarinyar data Shiga booth?
Lukman yace wannan yarinyar daka gasawa aya a hannu kuma kaso ka gasa mata gyada a tsakiyar kai Allah ya taimaka brother Jamal ya kira mom?

Tsaki yazeed yaja yace matsalata dakai kenan ka fiya surutu yanxu waya tambaye ka duk wannan jawabin?

Lukman yace Nide Ba wannan Ba meye da yarinyar?

Yazeed yace ita…sai kuma yayi shiru lukman ya ehm ita me? Yazeed yace itace amaryar da mom ta aura min

Wani wawan birki lukman yana yana zare idanu ya kalli yazeed a tsora ce yace dude me kace ?
Harara yazeed ya aiko masa yace banson iskanci ai sarai ka jini.

‘Kefta idanu yayi alamun mamaki sannan yace kana nufin yarinyar nan daka gama shekawa rashin mutunci mom ta aura maka kuma ka zauna da ita ?
Kawai sai ya fashe da dariya harda rike ciki kai mutumina Gaskiya life dinka na birgeni,Wai ina self respect din naka da …….. Ya tafi ?

Wani kallo yazeed ke aika masa if looks could kill da an Dade dakai lukman kabari.
Yazeed yace banson wulakanci ya ina maka serious magana kanamin dariya?karka batamin mood fa. Dan wulakan ci bakasan in ina magana ba’a datseni Ba?’kwafa yayi yace dallah mallam  zaka ja mota mutafi ko zaka tsaya kana batamin time?

Kunna Moran lukman yayi yana mai danne dariyarsa sannan yace haba nawan, Allah ya huci zuciyarka.
Tabe baki yazeed yayi yace in bata huce bafa?lukman yace zama ta huce Insha Allah .

Tsaki yaja sannan ya ci gaba ni yanzu Ba wannan Ba matsalarka shine Allah ya gani bana sha’awar  kusantar yarinyar nan , mom kuma ta dage ita kawai a haifo mata jikoki.

Ajiyan zuciya ya sauke sannan yace zakiyya ko Kazan yadda muke ciki da ita
Gyada kai luku guy yayi alamun ya sani sanna yazeed ya kara da kuma inks lura amaryar tayi karama dayawa bana tunanin zata iya dani.

Wannan magana ta mugun bawa lukman dariya amma to avoid issues with his amini yasa ya shanye abarsa
Yace uhm sannunku manya manya su alharijunal auwaluna

Yazeed yace wallahi luk guy ka fita matsala na rantse da Allah zanma rashin mutunci inma harijancin ne aiba laifi na bane Allah ne yaso ya ganni haka wasu da kudi suke biya dan su zama harijan ?Toh Nina zamu a’bagas sai ince banaso?

Lukman yace chill man Daga wasa yazeed yaja tsaki kasa kasa yace aikin banza mutum matanshi biyu amma ya kare da azumi. Lukman yace karka damu wata rana sai labari.
Daidai lokacin suka iso plaza din, saukowa sukayi Daga Motan lukman ya latsa mukullin ya rufe sannan suka Shiga nan dai suka zabi latest Samsung Inda suka hau musu akan kalar wayan.

Yazeed yace lallai saide a siyi fari domin yafison farin kala ko shudi (blue or ruwan bula) yayinda lukman yace ai golden zaifi tunda itadin zata hau da kowa ni kaya kamar dai sarkar gold kuma ai mata nason kyale kyale ……..

Haka suka cigaba da arguing Daga karshe mai Saida waya yace wannan abu mai sauke ne su siyi fari inyaso sai asa mata cover golden.
Nan suka yarda yayin da suke hada baki wajen Cewa that’s it!

Bayan sun dawo Motan ne yazeed ya kalli luku yace guy bakace Komai ba.
Shima lukman domin ya rama abinda YAZEED ya masa sai yayi acting Kamar bai gane ba yace akan me fa ?yazeed yace abinda na fada maka mana
Lukman yace kawo kunnanka,yazeed yace ni in zakayi magana kayi lukman yace dadinta ni lamin lafiya nake kuma dadinta ba matsalata bace. Kanaso kaji koko? Yazeed yayi ajiyan zuciyar in defeat sannan ya matso na ya sanar masa da yadda zaiyi aiko yazeed ya zabura yace luku amma kasan if the plan backfired zai iya jawomin raini ko?lukman yace ‘in order to succeed, you must take the risk’ ko ba haka kake Fadawa mutane ba?gyada kai yayi alamar haka ne amma wannan din is it worth it?

Haka dai suka dawo gida lukman na kara karfafawa yazeed din guiwa sai wajen 10 tukunna suka rabu.
Koda ya shigo dakinshi wanka ya fada.
Ji yayi Kamar an Shiga dakinnasa amma ya basar Dan yasan bazai wuce zakiyya ba. Koda ya fito samunta yayi tana kwance tana chatting da sabuwar kawarta sumayya ,ko kallon inda yake batayiba,shima bai kulata Ba yayi hayewarsa ya kwanta.
Wajajen 3 yazeed gaji Kamar ana tabashi
Bude idanunsa yayi yaga zakiyya zaune tana kallonsa tace baby inason magana dakai dan daura fiska yayi yace magana bai iya jiran safiya bane ? Haba zakiyya fisabilillahi ace ki tashi mijinki tsakar dare Daga bacci lokacin da Allah yasa Dan bayi su huta Wai zakiyi magana dashi?to ina jinki
Tace baby wani urgent business trip ne ya taso min ana you know  that next week fa za’a fara bikin cousin sissy kaga we have to arrive early so I think  de I will not be around for 2 weeks.

YAZEED kam da mamaki ya cika shi danshi yanzu lamarin zakiyya ya daina bashi haushi ya fara bashi tsoro.
Tabe baki yayi alamun takaici yace OK jeki sannan ya Koma ya kwanta.
Tace baby Ba zancen tafiyan nawa bane ai.
Yace ok tunda dama Ba izini kikazo nema Ba to miye na fadamin?

Tace to katashi ka zauna magana is serious fa yace a haka ma inaji sannan ya rude idanunsa. Tace dama so nake na dauki white Prado dinka Ba.

Yace kinsan dai ko sweetheart bata tana hawa wannan Ba kuma kinsman ko tukani ba’ayi Dan kar ashiga min cikin Abuna.

Tace to jawabin na menene kuma aini Ba mom bace,kawai kaban motan.
Yace abinda jawabin ke nufi shine bazan bayar ba. Kuma zancen keba sweetheart bace kina nufin kin fita ne ? Ince mota 6 ne dake ko duk babu Wanda zaki iya tafiyar dashi ne?tace baby 4matic dina kullum shi make using its out of the picture,Prado na kuma paint dinshi ya tsufa kuma………..

Yazeed ne ya datseta ta hanyar Cewa ince paint ne kawai ya tsufa tace eh yace fine then use it mana.
Tace baby mutanefa zan Shiga yace anso gara ke,mutane nawa ne zasuzo da irin motan naki?the only help dazan baki shine ki dauki bakin not the golden one! Tace baby amma…… Hannu ya Daga mata hannu yayi sannan yace zaki iya barmin motata.

Tashi tayi tana gunguni bajar bajar tabar dakin shiko yazeed tabe baki yayi ya Koma tsakiyar gadonsa yayi d’ane D’ane.

Sarai yasan dalilin da yasa takeson tafiya da farin, saboda shidin customised ne. Hmm wato mai hali baya fasa halinsa,itadai burinta ko ina taje asan matar manya ta iso.
Baccinsa ya cigaba da narka kamar Ba gobe.

Miss untichlobanty💕

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button