KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Hakuri suka bawa sabir Wanda ya kasa yin komai yayinda tayi tsaki tayi wucewar ta. Fadawa tayi a kujera, tayi ciro da takalman kafunta tare da cewa (ji wani mafari mara kyau)what a bad start! Aunty jalila kanwar wacce takeda shekaru 32 maman su tace gaskiya bushra kin bani mamaki menene haka? Ya zaki Mari sabir? Mutumin kirki ga gaskiya kuma…. datseta bushran tayi ta hanyar cewa aunty kuyi min uziri ku siyomin icecream keda feena, kaina ciwo yake zamuyi magana anjima. And please ku zaku siyo kar a bada sako ma driver ko wani kazamin.

Tabe baki aunty jalila tayi kamin ta shiga daki tana fadin aiki ya sameki sannan ta shirya suka fice tare da cewa yarta shameela wacce take sa’ar su zayya ta zauna ta sakawa bushra ido idan tayi wani Abu ta sanar Mata. Ita kuwa abin nema ya samu saboda rawar kai gareta.

Hakuri suka sake bawa sabir sanda ya bude musu gate yace ba komai sannan suka fita suna cikin tattauna halin da ta dawo musu dashi feena tace la aunty kinga wata baiwar Allah zaune da yarinya a hannu ga za’ayi ruwa kuma dai nan ba wajen bara bane. Haka kawai aunty jalila taji tanason ta tsaya dukda yadda zamaninnan ya baci.

Magana sula fara Mata amma taki ta dage kanta balle ta kulasu sai kuka take ana cikin hakane zayya ta dawo……

CIGABAN LABARI

Ajiyan zuciya minal ta sauke tana mamaki da akace akwai me kama da ita. Feena tace aunty zo kiji, cikin kunne ta fada Mata wani Abu sukayi yar shawara.

Tsugunawa tayi a gaban minal tace kinga yanzu ruwa za’ayi kuma da alamu bakida wajen zuwa me zai hana ki biyo mu. Girgiza kai tayi tare da cewa ni yanzu bazan yarda da kowa ba ku barmu ni da yara na kawai mu mutu.

Aunty jalila tace wannan wacce irin… kasa karashe wa tayi sanadiyyar ruwan daya tsinke zayya ne fara rokanta akan su bisu kawai kar ruwa ya halaka yar uwata. Badon ran minal yaso ba tabisu.

Yazeed kuwa suna cikin tafiya ruwa ya balle Abu na farko da ya fado a ransa shine boss ladynsa. Ganin hankalinsa bai kwanta yasa yace su juya koda ya koma yaga wayam haka yanaji yana gani ya hakura.

………..

Suna shigowa gida suka sassauko a motar da sauri suka shiga ciki saboda ruwa yayinda akabar? feena da zayya suna dauko ledan icecream. Shameela na ganinsu tace mummy wallahi kina fita aunty bushra ta sa ya sabir aiki wai ya goge Mata takalma….. aunty jalila tace yanzu tana ina? Tace tana dakin mama.

A waje kuwa daidai zayya ta juya ta hango wani kamar ta sanshi amma ta share batayi magana ba taci gaba da yiwa feena hira suna dariya suka shiga ciki.

Surutun da shameela keyi na ya tsaya lokacin da ta lura da minal dake bayan jalila. Kallon saman beni tayi ta kuma kallo minal sai ta bazama a guje tayi sama cikin haki ta bude dakin mama taga bushra a cikin dakin sai ta kallo minal, ta sake kallo Bushra ta kalli minal kawai sai ta fashe da kuka.

Waiyo umma(abinda take kiran mama dashi) na shiga uku na haukace. A tsorace mama da bushra sukayo kanta suna fadin lafiya ? Nuno minal tayi da yatsa aiko minal da bushra suka hada ido.

Kallo kurilla sukewa juna yayinda mama ke fadin ke jalila me nake gani haka? Murmushi tayi kamin ta fara fadawa mama yadda akayi. Mama tace no wonder sabir ya Kira bushra da yar uwa ya dauka itace ashe…. wani tunani ne ya fado Mata bata karasa zancen ba tace ke dakata hakan na nufin itace Wanda ta gudu yake neman ta. Ke shameela je ki Kira mana sabir, da gudu ta fita a bakin kofa sukayi karo ita da zayya. Tsaki taja kamin ta fice zayya ta bita da kallo. A lalle za’ayi cakwakiya bata sanni bane kar taga nan gidansu ne babu abinda ya dameni wallahi wulakanci zan Mata kar taga gidansune.

Ganin kallo yayi yawa yasa feena tambayarta ko ta Santa ne? Tace a ah.
Haka dai sabir ya shigo ya roki afuwar su sannan aka duba sahla inda aka tabbatar tanada rai saide a halittarta bata juran wahala.

Minal da bushra dai basu cewa wa juna komai ba har dare yayi sukaci abinci. Ba ciki na ciki, minal ta kasa gaskata akwai me kama da ita yayinda bushra kejin haushi ya za’ayi ita da take ganin tanada kyau ace wata banziya gayyar talauci tana kama da ita har ma ta fita kyau.

Wasa wasa lokacin na tafiya safina hargutsa gidan yazeed baki daya. Yayinda sahir ya tafi cambridge university karatu safwan kuwa yace a kasarsa zai makale babu inda zashi danshi Dan baba ne.

Bayan shekaru 6

Da baya baya yake ja idonsa cike fal da tsoro kamar kulya a lungu kafarsa na mazari Dan yasan kashinsa ya bushe tunda ya sake ya jefi zayya da ball.

Gefe kuwa yan team dinsu ne tsaya suna cika suna batsewa. Kirbashi ko ta soma tun yana ihu har ya daina da alamu ya suma yarda shi tayi ta juya zata tafi ogan team din cikin harshen turanci yace ke kina tunanin kin daki banza ne ? juyowa tayi suka hada ido.

Ido cikin ido suka fara nufo juna gaba daya daliban da suka taru suna kallo baya baya suka fara yi Dan sunsan yau za’ayi world war na 3…..

Don’t forget to vote, comment and follow me. I repeat vote and comment ooo.

DEDICATED TO: aysherahmaddanlami

Love you all??

Miss Untichlobanty ?

14th April, 2020.

?? KURUCIYAR MINAL??

? By miss Untichlobanty ?

? CHAPTER 84?

RECAP

Ido cikin ido suka fara nufo juna gaba daya daliban da suka taru suna kallo baya baya suka fara yi Dan sunsan yau za’ayi world war na 3…..

CONTINUATION

Naushi ya kawo Mata ta kauce, caraf tayi ta riko shi tare da basa one blow seven die. Haka dai ta hadesu duka su goman ta basu kashi.

Principal ne yazo kanshi ya bata sammacinta lokacin da aka dawo daga wasa.
Cikin takunta na maza ta shigo dakin taron Dan malamai gaba daya sun taru, cikin harshen turanci tace malamai sannunku sannan ta dauke kai.

Ajiyan zuciya principal Solomon ya sauke tare dacewa zayyana meyasa? Meyasa bakyajin magana ko kadan? Ke wace irin matamaza(tomboy) ce? Mun baki hutun hukunci (suspension) yadi Akirga,hukuncin Karin lokacin tashi (detention) kuwa yana cikin jadawalinki. Kinsani a Bisa ka’idar makarantan nan ba’a duka tunda international school ne Dan haka mun yanke shawara zamu mayar dake dayan branch dinmu Wanda babu musulmai,babu hausawa, babu yan kasarnan saide yan wata kasa.

Tunda principal din ya fara magana ta saka earpiece a kunnenta dan haka koda ya gama godiya tayi ta karbi paper da ya bata sannan tayi ficewarta aji ta koma ta zauna a kujerarta Wanda ke karshen aji sannan ta fara shirgar baccinta. Girgiza kai malamin yayi kamin yaci gaba da bada darasi.

Koda aka tashi sanda sukayi fada da shameela akan ta bata musu lokaci zayya bata ce kala ba sanda shameela ta gama zayya tace bana taba Mata saboda ragwaye ne sannan ta wuce abinta.

Suna dawowa suka samu kowa da kowa a parlour barka da zuwa aka musu mama na zaune a gefen daddy wato Alhaji mansur mainasara, yayinda aunty jalila ke hararan kanwar shameela wato nana saboda tayi roko.

Bushra aka tisa a gaba akewa fada akan yadda ta rufe ido Sam wai ita sai mai kudi zata aura. Ga yadda take wulakanta talakawa kuma hakan matsala ke haifar musu ita da minal.

Ko ina idan minal taje neman aiki sai ace ba ita bace tayi wulakanci a waje kaza ? Sai a koreta komin rantsuwar da zatayi, yayinda ita kuma bushra ake cewa an ganta a waje kaza da shiga ta mutanen arziki. Shiyasa kullum sai sunyi fada.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button