KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Direct side din mom ya wuce a lokacin har ta fara bacci Kamar a mafarki takejin yadda ake buga mata kofa hakan yasa ta bude ido

Adan tsorace ta bude kofar ganin jamal fiskannan tayi jaa tace son lapiya?

Kamo hannunta yayi sai part din yazeed hankalinta a tashe Dan tadau wani abunne ya samu danta daya daya

A Abangaren su yazeed kuwa harara ya banka mata kamin yaje ya kwanta akan gadon yace tayi knee down
Tayi tsamo tsamo da ita a cikin fitsari duk ta zama abin tausayi kwalliyan duk ta cabe

Kinyin tayi illa ma turo baki da tayi alamun gardama saukowa yayi daga gadon ya daga hannunsa zai dalle bakin

Puuuuuumm aka bugo kofar dakin duk suka kalli wajen

Abangaren su inna kuwa hankalin kowa ya tashi aunty fauziyya sai kuka take acewarta laifin tane tunda a hanyarta na dawowa daga gidan tane ta bata

Baba kam ya ma kasa yin Komai Dan jinya ce ta kamasa rif daya Ba abinda yake furtawa sai Innalillahi wa inna ilaihi raji’un

Kowa hankalinsa ya tashi abin dai Ba dadi gashi ya Abubakar saura 3days ya dawo

Anan ne ink din bairo na ya kare bara insiyo wani domin rahoto muku labarin kuruciyar minal

Ku Muna Mani soyayya ta hanyar commenting

Sannan Ku nunawa kuruciyar minal soyaiya ta hanyar sharing.

Love u wujiga wujiga

10th July 2019

Karamarsu babbarsu ce fa

Mzz untichlobanty💕
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹🍀by @mzz_untichlobanty🌹

CHAPTER 16

Kallon wajen dukkansu biyu sukayi

Minal hawaye da majina duk sun chabe mata fiska

Jan majinan tayi kamin ta mitsitsika hanci sannan ta goge a hijabin daya hada launi daban daban kama daya kalarsa da kalar jini,da jurwayen fitsari tare da kanzon majina😂
Takowa tayi cikin dingisawa ta tsuguna tace ina kwana au ina yini hajiya

Dan Allah kicewa oga sir ya mayar dani gida wallahi yunwa nakeji gashi Nasan hankalin iyayena ya tashi.

Dagota mom tayi ta Shiga dakin tana takawa idon ta cikin na yazeed Wanda ya kasa fassara yanayin mahaifiyar tas

Bai ankare Ba yaji saukan mari
Wani tashin hankali ne ya saukar masa tunda ya mallaki hankalin kansa bai taba ganin bacin ran mahaifiyarsa akansa Ba balle ta dakesa.

Hakan yasa lokaci daya zazzabi ya rufe oga sir Dan baima lura da Cewa yana ha’bo ba

Zama yayi kan gadon jagab Ba tare da yace Komai Ba kuma bai motsa Ba kwakwalwarsa ce ta daina aiki

Baki mom ta bude ta fara magana dukda ko zuciyarta ta girgiza ganin ta fidda jini Daga jikin Dan nata amma abinda yayi ya wuce wannan.

Haba yazeed ban taba tunanin irin haka daga gareka Ba dukda Nasan irin zaman da kakeyi da matarka ban taba tunanin ko da wasa zaka Ra’bi zina Ba
Bama a zina ka tsaya Ba zinar ma fyade kayi?

Amina jin bata gano Inda mom ta dosa Ba kuma da alama mom ta saba layi Dan da alamu bata fahimceta Ba sai tayi saurin Cewa Hajiya dama oga sir da ya fita fyade yayiwa wata?

Juyowa mom tayi fiskanta da alamar tambaya domin kanta itama ya daure shima dai Jamal hakan ta kasance masa.

Domin duk Wanda yaga minal a yanayin da take kuma acikin side din yazeed to lalle Abu na farko da zaiyi tunani shine fyade yazeed yayi mata
Duba da yadda shi Jamal din ya samota a bandaki a sume sannan tana tashi abinda ta fara yi shine kuka to lallai abinda zaizo kanka kenan.

Mom tace yata dama Ba fyade yayi miki bah ?
Minal ta gyada kai kamar kadangaruwa atake nadama ya saukarwa mom kawai sai ta kama hannun minal tayi side din ta da ita domin jin Karin bayani.

Abangaren Jamal kuwa dakin yazeed yaje ya dauko cotton sannan ya dawo zauna a gefen yazeed,cotton din yasa ya goge masa jinin sannan ya tura wani a hancin ya ruko hannun yazeed din.

Rumgumesa yazeed yayi ya fashe da kuka mai sauti Kamar maraya gaba da baya me karancin shekaru.

Jamal bai hanasa kukan Ba illa ma bubbuga bayansa da yake yi alamun lallashi

Saida yayi mai isarsa sannan ya tashi zai fita Jamal yayi saurin rikosa tare da mikewa tsaye Suna fiskantan juna yace lallai mudin abokai ne amma abokantakan ya ya karfafa Yan uwantakan mu lallai nidin na kasance mai kuskure d…………

Hannu yazeed yasa ya rufe masa baki tare da girgiza kai yace lallai nine me laifi da ban sanar dakai Ba kuma ai sanda kace zaka kawo mom saina mata bayani,na dauka wasa ne Kamar yanda ka saba Dan nima baizo kauna Cewa zakuyi min mummunar fahimta Ba saboda yanayin yarinyar. Lallai kaidin amini ne na Gaskiya saboda alkhairi kake sona dashi Dan haka karka bani hakuri.

Rungume juna suka kara yi kowannensu na hawayen farin ciki kamin kuma suka fashe da dariya suka tafi domin yin sallh Dan lokaci ya tafi.

Abangaren su mom kuwa wani daki ta kawo minal sannan taje dakin zakiyya wardrobe din ta ta bude Dan tasan pin din taga duk babu laces da atamfofin

Wani kofa acikin dakin  ta bude dakine girman sa Kamar store babu Komai aciki sai akwatina 5 wasu takalma masu kyau amma zakiyya tasa a store Wai sun tsufa alhalin Kamar saga kwalinsu aka cirosu ko kurar arziki basuyi ba

Akwatinan mom ta bude ta dauko wani lace mai kyau da takalmi da kuma hijabi sannan ta rurrufe wurin ta kawo dakin da tabar minal

Ajiye kayan tayi sannan ta kalli minal wacce ta zauna a kasa tace Yan mata tashi ki zauna akan kujera mana ayayin da take nuna mata sofan dake dakin

Girgiza kai tayi tace Ba Komai nan ma yayi
Mom ta kamo hannunta ta zaunar da ita sannan tace
ya sunanki?
Tace Amina
Mom tace ya akayi kikazo gidannan kuma me hadinki da Dana

Kallon mom minal tayi kamin ta fara kwararo mata bayani cikin nutsuwa,kamunkai da tarbiyya Kamar da gaske tun daga fitowarta daga gidan aunty fauziyya har izuwa yanxu

Not telling her that this is not the first time she met yazeed

Shiru mom tayi tana nazarta maganan

Da ta tambayi yazeed kamin ta mareshi amma ai kowaye yaga yanayin aminan abinda zai ce kenan kuma ko Ba Komai soyayya ta jawo hakan ai Dan masoyinka ke hukuntaka akan laifinka

Makiyinka ne zai ganka kana Abu Ba daidai Ba ya barka ko ya kara ma kwarin gwuiwa

Kayan ta mika mata sannan tace tayi sallah za’a kawo mata abinci kamin ta fita tana tunanin lallai yazeed bai kyautaba na azabtar da minal da yayi Ba tare da yaji mai ya kawota motansa Ba sannan taya za’ayi ta miyar da minal gida a wannen yanayin?

smiling tayi wadda ke nuna ta samo mafita

Masu aiki ta aiko da kayan abinci
Lokacin minal ta chakare tayi das da ita har taji wani fresh a jikin ta murmushi tayi tace tsabta dadi

Dakwalin ta dauko zata daura saita fasa kawai tasa hijab

Zama tayi a bakin gado tana kalon tsarin dakin

Ya mugun tafiya da imaninta

Abincin aka kawo duk babu Wanda zata iya ci sai shinkafa haka ta daure ta tuttura taci rabi Dan ita shinkafa Ba gwanarta bace

Doctor mom ta kira aka da mata su bandage a inda taciwo aka Duba kafarta targade tayi aka daure mata shima likita yace tanajin wani ciwo tace a ah Dan tasan da tace eh to tasan allura ne😂😂

(People like me and minal come and gather here lets know our selves)

Karamarsu babbarsu ce fa kai yau Nayi rubutu chapter har uku fa kuma ina tunanin kara wani

oya ku kirawo kawayenku da Yan uwanku masoya karatu suzo su yar da zango Anan.

Mzz untichlobanty💕

Au Ashe bansa date Ba

10 July 2019
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by @mzz_untichlobanty🌹

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button