KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

CHAPTER 17

Abangaren yazeed kuwa suna dawowa daga masallati dakinshi ya koma ya kwanta domin zazzabine ya kamasa sallan ma daurewa yayi

Gawani tsananin tsanar minal dake taso masa

Wai yau shi mom ta Mara akan wannan kazamar bagidajiyar? Kuma har ta fidda masa jini?

Lallai sai ta gane kuranta a haka bacci yayi awon gaba dashi yana nazarin yadda zai yi maganinta minal.

Haka ta kasance Abangaren Jamal domin shima zaki ya nufa yayi d’are d’are a saman gado harda cire Riga sannan ya Lula duniyar bacci.

Abangaren su inna jikin baba Ba laifi ya Dan warware amma daka gansa kasan yana cikin damuwa.

Inna ce ta dinga yi masa nasiha tana kwatar masa da hankali har ya hakura ya fita domin zuwa gidan radio da jarida ayi sanarwa ko Allah zaisa a ganta

Aunty fauziyya ma ta daina kukan,mijinta yanajin labarin yayi gida haka zaliha ma ta tattara ya nata ya nata tayi gidansu.

Sanda mahaifiyar zalihan wato iyata sami labari kafafun ta kasa riketa sukayi.
Harga Allah minal yarinya ce mai Shiga rai dukda ko bata daukan raini ga tsiwa da tasha tayi tatul.

Hankula Kam dan banace hankali Ba sun tashi, yan anguwan su minal ma sunji tashin hankali,Yan matan nan ko da minal tayi musu saitin hamma da gyaran kafureto kwanaki sai Cewa suke Allah ya kara.
Wasu daga cikin Yan anguwan sun yi farin ciki,wasu na yada jita jitan ai iskanci ta tafi,mafi yawanci kuma na tausayawa baba saboda shidin tsoho ne mai dattako kuma ansan yadda yakeson minal shiyasa Idan tayi wasu abin ma ake boye masa.

AT NIGHT(after magrib)

Minal tana zaune a daki tayi zugum gashi bata Masan Inda wayanta yayi Ba abin duniya ya taru ya mata yawa.
Ko wani hali iyayenta ke ciki?me zata ce musu?

Kofan dakin aka turo laraba ce tace Wai hajiya tace kizo.
Amsawa tayi da Toh sannan ta dauki hijabin da aka bata tasa ta fita.

Da dingishi sannan ahankali take saukowa daga upstairs saboda tsoro da kuma rashin Sabo amma inka ganta zaka dauka damuwa ce.

Mom ce tace sauko kizo wajena kinji my daughter.
Karasa saukowa tayi taje wajen mom ta zauna a kasa. Mom tace zo zauna gefena kinji hira ta fara janta dashi itakuma sai nokewa take.
Mom tace ki saki jikinki babu abinda za’a miki kinji kai ta gyada Kamar Kadangaruwa sannan ta Dan saki jikin nata.

Suna fira kawai alarm din 8 ya buga da gudu minal ta tashi mom tace relax is time for dinner.

Batade gane me akace Ba amma ta zauna tana zazzare ido.

Maids dinne suka fara fitowa da abinci ana kaiwa dining table.
Mom ta kamo hannun minal tace muje ko Ba musu ta bita suka he wajen dinning table minal de mamaki take Wai Ashe a duniyannan akwai masu rayuwa Kamar a aljanna masha Allah dama nida su inna nane.

Sai kuma tayi chuckling to the sound of her calling inna innana.
Warmers din suka fara budewa one by one minal taga duk batasan abincin bama.

Mom tace wanne za’a sa miki minal tayi shiru domin bataso tacewa mom bazata ci Ba.

Mom ta fahimci batason abincin daga yanda tayi da fiska sai tace atine kuje kitchen tare Ku kama mata ta dafa duk abinda takeso.
Suka amsa da toh hajiya.

Mom tacewa minal tashi kije kinji kunya ne ma ya kamata taga ya akeyi Wai manya suke ramfo ka duk wayon ka ?

Tashi tayi suka Shiga kitchen din tace musu sunada dawa gyararre wanda zatayi tuwo su kace ah’ah semovita ne kawai pack daya shima ya Dade bari su Duba ko yayi expire dubawa sukayi sukaga beyi ba sai suka bata.

Tace akwai wani Abu da zata iyayin miya Kamar kuka,kubewa,ogbono,taushe sukace a’ah amma akwai ganye tace to subata nan dai ta dinga fada musu abubuwan da take so Suna dauko mata saide bata bari Susna mata hannun ba.

Haka ta fara aikinta cikin kwarewa Inda ta dafa tuwo miyan ganye ya sha kayan hadi yaji kaza tun kafin ta gama yawunta ke tsinkewa Dan mugun yunwa takeji ga kamshi daya mamaye ko ina.

Mom tana kallo a parlour ta jiyo kamshi smiling aranta tace yarinyannan ta iya data shinkafa Dan tasan yamatan yanxu akwai maitar shinkafa(Nide ahalin tuwone😉)

Koda ta gama warmers
(foodflask) suka kawo mata madaidai ta.

Tuwonta Mara(malmala) 3 ta saka a ciki sannan tace su bata wani flask din Malmala 5 tasa a ciki sannan ta basu tace suci nasu ne ladan tayata aiki.

Godiya suka rinka mata yayin da suke satar kallon junansu me ma’ana ‘tanada mutunci ko me yasa oga sir ya mata abinda ya mata oho?” Sai kuma sukayi murmushi. Tray suka dauko suka daura flask din nata akai sannan suka kai dinning
Fitowa tayi daga kitchen din ta nufi palour wajen mom cike da kunya tana nazarin me zata ce?

Sai kuma ta tsaya “in banda hauka irin nawa taya za’ayi Maman oga sir taci tuwo?ehm kawai bara inyi mata godiya “

Parlourn ta karasa sannan taje kusa da mom ta zauna kanta kasa tana wasa da yatsu mom cikin wasa da accent din ta na Larabawa shigen na Jamal tace daughter har kin gama mana abincin ne? Murmushi tayi kamin ta gyada kai sannan tace Nagode hajiya da irin kyautatawan ki gare…..

Bata karashe maganan ba sakamakon riko hannuta da mom tayi tace”ni ba godiya nace kiyimin ba Dan Allah nayi sannan karki kirani da hajiya kinji?zaki iya kirana da mom”

murmushi minal tayi kamin tayi subutan baki wajen Cewa inkawomiki abincinne?

Smiling mom tayi Allah ya gani bata da niyyar cin abincin amma kar minal taga Kamar kyamanta mom take sai tace ki zuba mana tare.

Zare ido tayi tace tare kuma mom tace ehm.
Girgiza kai minal tayi tana wiki wiki da ido aiko karen haukane ya cijeta bazata taba cin abinci plate daya da mom ba taje wannan oga sir din ya ganta yaci ubanta tabe baki tayi tace ko ina yayi oho.

Muryan mom ne ya datse mata tunani ta hanyar cewa wasa nake miki kinji ki dibi naki kawai zanci anjima

Gyada kai kawai minal tayi sannan ta wuce ta dibi tuwonta Mara biyu tayi sama domin kunsanta ba wasa.

Aiko ta gyara wa tuwonnan zama sosai Dan ya mata dadi.
Abangaren mom ma haka ta kasance Dan tana diban Rabin marannan tayi dakinta ta gyara masa zama tare da yaba iya girkin minal sannan ta kara samin kwarin gwuiwa kan aniyarta.

Nikam side din masu aiki Nayi domin kar ayi bani Dan nima fa tuwonnan ya biya raina

Bazakusha mamaki ba sai sanda naci tuwo Nayi nak ai bansani yadda akayi medical yet fashion looking glasses dina ya fita ba niqabi na kam ba’a maganarsa Anan bacci yayi awon gaba dani 😴ko wanke hannu banyi ba😂

Gaskiya na gode sosai da addu’an Ku domin Alhamdulillah result ya fito kuma Nayi passing harma andawo second semester Muna shirin tafiya hutun mid semester daga nan sai test Dan haka ina bukatar wani addu’an Allah ya saka muku da alkhairi da fatan ina nisha dantar daku masoya na

Eid mubarak in advance

Nice de the one and only karamarsu babbarsu wato

Miss untichlobanty💕

5th August, 2019

Wait oooo don’t forget to vote ehee……….
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYA MINAL🏆🏆

🍀by mzz_untichlobanty🍀

CHAPTER 18

Da asuba bayan mom tayi sallah taje dakin minal domin ta tasheta sallahn asuba
Sallama tayi ta sameta Zaune abakin gado
Saukowa minal tayi ta tsuguna tace ina kwana haji.. Au mom
Murmushi mom tayi tace lafiya kalau ya kwanan bakunta

Murmushi minal tayi domin yadda mom din tace bakunta da kaji kasan ba bahaushiya Bace kamin tace Alhmdllh

Mom tace Ashe har kin tashi? minal tace ai tun dazu ma na tashi
Smiling kawai mom tayi tace to bara in barki ko

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button