KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Datse kiran tayi sannan ta kara dialling wani number ringing biyu aka dauka tare da fadin shedaniya uwar shedanu,muguwa uwar mugu,dakalin majina a hauki a zame kihau uban mutum ki zauna daidai. Tawa ni kadai har abada Umarninki shine farin cikina.

Murmushi tayi tace daina Sakai kenan duk yadda raina ya baci to Dana kiraka nake wartsakewa.

Ya ake ciki da batun boka cuku cukun? Yace masoyiya yanzu nabar wurinsa kuma yace an gama Jennifer ko za’a kashe kowa dake numfashi bazata iya tuna Cewa ke kika sata aikin Ba balle ta fada tace good to me yaje bukata.

Saurayin yace yana bukatar jinin bakinka Kare da raguna uku ma aljanunsa naman kuma a soye ta tayi yaji sosai sai ayi dambu da naman Karen wannan nashine tace okay zan turo maka 500k sai kayi duk abunda ake bukata. Yace an gama my love tace to sweetheart sai anjima.

Wani number ta kuma dialling sannan tace da fatan kaga balance dinka yace eh na gani tace yauwa Gaskiya aikin yayi kyau boutiques din sun none kurmus shiyasa ma na kara maka akai. Sai kayi kokari duk kayan da kuka kwashen Ku kukai min warehouse din.
Yace ai nakai tun jiya tace excellent shiyasa nakeson aiki dakai baka disappointing dina. Yace na gode ma. Datse kirar tayi tana murmushin rashin imani tace just wait and see daina rushed rayuwarku gaba daya especially yazeed da zakiyya Dan kune salsalan matsalata.

🌹…………

Koda yazeed ya Shiga mota domin su wuce su hadu da tawagar convoy dinsu,lukman yace mutumina karka dauka ban gani ba. Yazeed yace ni kuma Allah ya sakamin tsanan Dan sa ido ba. Lukman yace to ai ba saka ido bane tunda ina wajen abin ya faru karara a vaiyane yazeed yace kaika jiyota ai shiyslasa tunda ban yarda a Shigo min compound ko securities Suna can nesa.

Amma Gaskiya mutumi na gode domin kuwa shawar da ka bani ita na dauka kuma yanzu haka in nace babu Wanda ya kaini jin dadi banyi karya ba lukman ya sheke da dariya yace anyi abin kenan?yazeed yace kaji matsalata Sakai to babu abinda ya faru. Lukman yace zama faru ai.
Gidan da aka ajiye Jennifer suka shiga. Gaba daya fuskanta ya kukkumbura ba’a ma iya gane kamarta.

Thank you for supporting me!

Don’t forget to share and comment

GOOD NIGHT

Miss untichlobanty💕

4th December, 2019.

6 – CHAPTER 51-60
[1/11, 2:29 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by mzz_untichlobanty🌹

CHAPTER 51

Tana ganin YAZEED ta kara fashewa da kuka tana oga ka temakamin kayi min rai wani soja ne ya naushi bakinta. Atake hakori daya ya balle ya fado aiko jini ma yace baza’a barni a baya ba.

Yazeed ne yace let go of her if she is ready to talk. daya Daga cikin sojoji Biyar dinne ya falla mata wani lafiyaiyan mari yace zaki yi magana ? Ta Daga kai da Sauri tana Fiki Fiki da ido Kamar yar wuta Dan haka suka suncota.
Da gudu ta karaso gaban YAZEED ta rike kafarsa cikin hausanta Mara kyau tace sir Dan Allah kayimin rai karsu kasheni ka yafemin.
Hannunta yazeed ya yarbe Daga kafarsa sannan ya take ya murje ya muttsika har sanda jini ya fita yayinda Jenifer ke ihu tana fadin jusus!lord have Marcy !my hand!my hand!my hand ooo!

Alamu yazeed yayi da akawo masa kujera still kafarsa nakan hannunta amma baya murjewa.
Zama yayi sannan ya kamo bakinta ya matse hawaye ta somayi sai ka ganta abin tausayi yazeed yace wa ya sa ki zubamin poison a cikin cappuccino girgiza kai ta fara yazeed yadan kara danna kafarsa akan hannunsa hakan yasa tace waiyo zan fada!zan fada! Yazeed yace ina jinki tace madam………….
Wani abune taji yazo ya sari kanta a take ta rike kamin ta kwala ihu kaina!. Murmushi yazeed yayi ya table baki yace na hadu da criminals da suka Fiki so don’t fool around fada min!
Ya fadi haka da kakkausar murya.
Girgiza kai ta fara tace oga na manta na kasa tuna Waye I promise yanzu naji wani Abu ya sari kaina daganan kuma naji na manta wacece ita.
Yazeed yace macene kenan ?tace yes sir yace kai ayo kuyita dukanta harsai ta tuna.
Suko abinnema ya samu nan suka juya bayan bindiga suka dinga jibgar ta Kamar ba mutum bane.

Itako sai ihu take tana fadin I promise you sir na manta I swear on my life na manta!tun tana iya magana har kaji shiru can shu’aibu yaga Kamar ta dena motsi yace Gaskiya sir wannan matar tanada taurin kai Dan koda namiji ne da yanzu yayi magana Idan ba haka ba kuma to ta manta Dan gani nake Kamar Suma tayi.
YAZEED yace lukman! Lukman yace yes sir! Dauko ruwa a mota yace angama sir!

Koda lukman ya kawo ruwa aka zuba mata shiru kakeji Dan haka yazeed yace su sata a bayan hilux dinsu a kaita asibiti Dan karta mutu bata fada ba.

Aiko haka akayi koda akaje asibiti take aka karbeta bayan 2 hours doctor Muhammad ya fito yace Mr yazeed muje office ko.
Bayan sun Shiga office din doctor yace what’s your relationship da patient din? Wai hatsari tayine ?Dan mun karbeta ne Duba da Cewa you are an authority as well amma this is a police case.

Daure fuska yazeed yayi yace ba hatsari tayiba kuma she is my house made and she is the one that poisoned me.
Dr Muhammad yace do you mean ita tayi poisoning cappuccinon ka? Yazeed yace yes. Doctorn yace this is serious because that poison is strong Gaskiya. Toh amma yanzu dai Gaskiya tanada karaya 2 a Hannu  da kafa sannan dole sai an yanke mata idon hannunta na hagu Dan ya back Gaskiya before ya rube yayi affecting sauran and also she is in a coma.

Yazeed kam Dage kafada yayi yace she deserves it!any way do what you think is right and help me check her mental situation. Doctorn yace we can’t do that because her brain is not functioning anymore and that’s why she is in a coma remember? Yazeed yace oh yeah.

So yanzu zanbar 2 men dina zasuyi gadinta Doctorn yace no problem. Shaking hands su kayi sannan yazeed ya dawo gida lokacin har magrib tayi Dan haka shida lukman suka Shiga masallati direct har sanda akayi isha’i sannan suka fito.

Bayan sun fito yazeed ke cewa lukman saura week daya fa amaryarka tazo. Lukman yace matarda ka auramin dai. YAZEED yace naji aide kanasonta. Lukman yace lie lie zuciyata na ayush ne ita kadai,bakaga yadda ta dinga kuka ba sanda na fada mata yazeed yace don’t mind her zata saba sannan munanan Sakai duk ranan da kazo kacemin kanason yarinyarnan saina ma duka, suka fashe da dariya lukman yace never.
Daganan hiran ta kara saboda sun iso.

Koda yazeed ya shigo kitchen ya nufa ya zamu minal tana jute abinci ta bayanta ya rungumota tadan tsorata saura kadan miya ya zubo mata kukan shagwaba tasa tace da yanzu na kone fa? Yace sorry my yar kazame kawai Nayi missing Fiki ne amma ke da alamu bakiyi kewana ba.

Tace wa yace maka yace alamu na gani mana tunda ko welcome hug baki bani ba.

Juyowa tayi ta rungumeshi sannan tace to sakeni inkai wannan dinning table yace ina ai yau ni zankai tace ka barshi yace Idan baki kaeoba munyi fada bashi tayi shiko ya nufi side dinsa direct Wanda ke nuna acan zasuci abin cin.

Binsa tayi a baya tunda dama tayi wanka ta saka doguwar rigarta navy blue simple but elegant.
Koda suka Shiga side dinsa Inda sukaci dazu nan ya a jiye musu, mika masa wayarta tayi sannan taje fridge dinsa da ta ajiye kunun ayansu ta dauko ajiyewa shima tayi sannan ta bude food flask din ta zuba musu tuwo Mara uku biyu nata daya na yazeed tunda yace ta dena cin abinci dayawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button