KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Kabbara sukayi sannan yazeed ya fara rero karatu da zakin murya ga taushi ga tausasa zuciyan mai sauraro. Minal mamaki ya cikata sosai jin zakin murya yazeed,jikinta yayi sanyi sosai saboda yadda karatun ya tsuma ta.

Bayan sun idar sunyi addu’a sun shafa yazeed ya janyota yace my kazame ya akayi ne?turo baki tayi tace nifa banason kazamennan Dan dariya yayi yace zanyi tunani.

Tace ya yazeed wa kake ganin ya saka mana abin maye a abinci ko kunun mu?Sosa goshinsa yayi yana kara samawa minal mazauni a cinyarsa yace nuna abinda naketa nazari kenan. Minal tace ni gani nake so ake a hada tarzoma tsakanin mu kuma ko Waye meyin abunnan yasan abinda ke wakana a gidannan saboda kasan da bakacin abincina……

Pecking goshinta yayi yace kuskuren da na tabayi kuma kenan Ba. Murmushi tayi sannan taci gaba da Cewa Toh kaga kenan ni aka zubawa tunda ansan kai bakaci ko kasha Ba. Kenan Idan na bugu sai ka dauka ni yar shayshaye ce kuma Allah ne ya tons asiri na kaga kenan Daga lokacin kome akace ma akaina zaka yarda.

Zama ya gyara yana kara zurfafa tunanin akan abinda take fadan domin tana making sense. Taci gaba da Cewa kuma kenan zaka iya sakina at any moment saboda wannan.

Toshe mata baki yayi yace shhh bazan taba sakinki Ba! Inaso kiyimin alkawari ko me aka fada miki akaina bazaki rabu dani Ba kuma zaki tun tubeni kuma bazaki rabu dani Ba Komai zafi Komai wahala.

Tace Nayi yace nima na miki alkawari bazan tana zarginki Ba kuma bazan rabu dake Ba.
Rungumeta yayi ajikinsa sannan yace ya Allah ka karemu Daga Sharrin dukkan mai sharri.

Minal ne ta mike yace ina zaki?tace ina zuwa. Parlour taje aiko kalli wayar a Inda yazeed ya buya jiya. Murmushi tayi tunowa da irin haukar da suka dinga yi.

Wayan ta dauka ta dannan on button aiko yana kan contacts Inda yazeed yayi saving numbern shi Ba fita Ba.

Kokarin karanta sunane da yayi saving yayi tunda ta iya karatun Hausa na turancin ma Ba laifi zata rubuta zata karanta saide abinda ba’a rasa Ba matsala shine batasan ma’anan abinda take karantawa ko rubutawa Ba.

Karantawa tayi taga an rubuta yazzy baby tace Waye kuma yaz…..

Inazuwa!yazzy – yazeed , yazeed -yazzy.
Okayyy wato shiyasa jiya ya buya a gefen kujera saboda zaiyi saving number sa a wayana? Dariya tayi tace hmmm bari inje in hadu da yazzy baby a daki. Dariya ta kara fashewa dashi sannan ta nufi dakin koda taje kofa ya rufu gaba daya tunda batasan pin dinba sannan thumb print na yazeed ne zai bude sai tayi knocking yace ki shigo mana tace ai ya rufu bansan lambobin Ba. Tashi yayi ya bude meta sannan yayi wasu danne dannan shi yayce tasa thumb dinta. Sakawa tayi ya danna okay sannan yace ta kara sa’a for confirmation sawa tayi sannan ya danna green button din ma’ana OK.

A kunnan ta ya rada mata Daga yau in kinzo a kulle kawai ki daura wannan yatsan naki sai ki danna green dinnan ki kara daurawa kinji? Ta gyara kai sannan itama ta janyo kunnansa tace me yasa kake rada min kunnan ta ya kamo yace saboda kar muje akwai masu kallonmu ko jin mu. Tace ta yaya?

Yace ta na’urar camera zo muje muga abinda ya faru a kitchen a na’urar camera na.
Binsa tayi suka zauna tace yazzy baby dauko ka nunamin Toh. Kallonta yayi cikin abin tausayi yace Dan Allah ina kika sani wannan sunane ki rufamin asiri kar lukman yaji. Murmushi tayi ta hasko masa wayanta. Date kai yayi yace Allah ya tsinewa abin shaye shaye.

Dawowa tayi ta gefensa ta zauna tare da sakala hannunsa a NASA tace yazzy baby nunamin Toh.
Saman study table dinshi ya nuna mata yace dauko laptop dina a saman can. Da fatan kinsan laptop tace na sani mana. Yace ki daiyi a hankali karki fasamin Dan akwai important abubuwa akai. Daukowa tayi ta kawo masa sannan ya kuna direct na kitchen ya Shiga suka fara kalla tun daga safiyar jiya. Yaga sanda su tala sukayi su shara,can minal ta dafa abincin safe tayi su kunun ayanta har izuwa sanda ta daura abincin rana.

Bayan ta fita can sai ga wani ya Shiga yana leke don tabbatar da Cewa Ba kowa.
Direct fridge ya nufa ya bude sannan ya balli wasu capsules guda 5 ya zuba acikin wani Abu dake fridge din Wanda babu shakka kunun ayan ne tunda basu sha Komai Daga fridge dinba banda kunun ayan.

Sansadawa mutumin yayi ya fita ta back door Kamar yadda ya shigo.
Caption din gate yazeed ya Duba amma baiga fitan mutumin Ba ya Duba na suka balbabalin gidan amma babu mutumin tunda ya fita Daga kitchen yayi kwana shikenan.

YAZEED yace shit! Toh ta ina ya shigo ko ya fita. Minal tace to kodai acikin gidannan yake ? YAZEED yace ko a cikin sojojina yake da zanga ya nufi side dinsu domin canja kaya amma wannan kwanan baya yayi shikenan.

Dukda haka yazeed baiyi kasa a guiwa Ba ya kira lukman……
Ringing uku ya dauka yace ya akayine? Yazeed yace kasa sojojinnan su Duba ko ina a gidannan a tabbatar babu kowa sannan biyu su dawo ta arean back door dina Suna monitoring.

Yanda zasu iya ganin mai Shiga da fita amma bazasu iya ganin na ciki ba. Lukman yace okay sir! Amma me ya faru an sake yin wani attempt ne? Yazeed yace Idan na fito zamu tattauna. Sannan ya kashe wayarsa, minal tace kai amma nature shege ne yanzu fa Mun kalli suka balbalin gidannan Muna dakinnan. Murmushi yazeed yayi yace hakane wannan shi ake kira CCTV. Jinjina kai minal tayi sannan tace yazzy baby amma dai babu acikin gidannan ko? Kallonta cikin idonta yayi sannan ya girgiza kai yace akwai a ko’ina amma handa dakuna.

Aranshi ko yace aike har ban dakinki akwai shi.
Minal Kam ajiyan zuciya ta sauke jin yace babu a dakuna Dan tsoranta kar ace yaga duk hakan da takeyi.

Kwantar da kanta tayi tace kadan sosamin kaina Dan Allah. Core human dake kanta yayi aiko a take gashin ya zubo babu ko ribbon.

Yace nifa banason kina Karin gashi ba dole kanji yayi kaikayi ba. Dago da kanta tayi ta kalleshi sannan tace Allah ya kiyaye in saka izgan doki ko gashin roba a kaina, wannan gashi nane.

Tabawa yazeed yayi yaji laushi ga kamshin sun flower shampoo dake tashi, lumshe ido yayi sannan yace kina kudin gashinki ne wannan? Ta gyada kai hancinshi yakai yana shinshinan gashin sannan yayi pecking yace kamshi. Murmushi tayi tace kanaso ne?yace sosai ma ki daina saka hula kinji ki barmin ina gani. Gyada kai tayi sannan ta kara kwanciya ya fara Sosa mata kan a hankali sai lullumshe ido takeyi.
Can yazeed yace ina rigannan na jiya tace yanakasan wannan yace tashi ki cire wannan din.
Mikewa tayi ta core dukda tanajin kunya amma tadan fara sabawa da nuna jikinta wa yazeed.

In ka ganta sai kace yar India irin model dinnan sanda yazeed ya kare mata kallo iya son ransa itako sai kokarin gyara Rican rake Dan ko guiwa bai karasa mata ba tashi ana ganin Komai.

Kwanciya ta sake yi yaci gaba da Sosa mata kai yana mai shara bayanta a hankali a haka har bacci ya dauketa bata sani ba.
Daukanta yazeed yayi yakaita kan gado sannan shima ya hau ya kwanta a gefenta sannan ya janyota ya rufe musu kafarsu da bargo bayan ya cire jallabiyarsa.

Shidai a Gaskiya akwai wani special Abu da yakeji a zuciyarsa game da minal kuma Idan dai abinda yakeyi wa zakiyya shine so to ba son minal ya keyi ba wani Abu ne na daban shima….

Irin wannan murmushi haka ai sai bakinki yayi ciwo. Ko duk jin dadin chaptern nanne?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button