KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Zaliha dai inba kuskure take Ba to lallai muryan minal taji may be depression na batan minal din yasan ta fara imagining things

Juyowa tayi aiki karaf suka hada ido murza idonta tayi yayinda bakinta ya budu mamaki da tambayoyi fal ranta

Da sauri ta karaso tana mai saka hannu domin taba fiskan minal Dan ta tabbatar da kokontonta
Aiko minal dince Ba gizo gizo Ba

Cikin dashasshiyar murya tace minal

Smiling minal tayi tana gyada kai

Zaliha tace Kece ?minal tace nice
Bude kofan motan tayi ta sauko kamin suka daka tsalle atare suka rungume juna suna ihu tare da juyi

Smiling kawai baba bala keyi

Nanfa minal ta juya tacewa baba bala zai iya tafiya

Yace hajiya kin tabbata Ba matsala? murmushi ta masa alaman eh kamin sukayi jikin gida aguje sai dakin iya bakinnan nasu har kunne

Aiko iya taji dadin ganinta sosai bayan ta mata jaje ne suka fito suka koma dakin zaliha

Zaliha tace kawas wayar dani, Wai yankan kai kika fara ne?ko sata?ko kidnapping?

Minal ta kyalkyale da dariya tace Kamar kinsan yanxu haka kanki nazo cira kuwa

Ai bashiri zaliha ta rufe kanta

Wannan karan minal dariya take harda buga cinya tace ke dallah wasa nikeyi matsoraciya

Zaliha tace anji ai tsoran ma da dalili nakeyi nidai yi mini bayanin yadda akayi kika samu mota irin wannan kuma harda driver

Minal tace “jiya……..

Nan ta labarta mata abinda ya faru Kamar yadda mom ta tsara har izuwa yanzu zaliha ko sai gyada kai take Kamar kadangaruwa alamar gamsuwa

Minal ko taki fada mata Gaskiya ne saboda tasanta da karadi yanxu sai tayi subul da baka ta fada Ba tare da tasani Ba

Aiko hira suka kafa minal na bata labarin yadda gidan su yazeed din yake wani abin ma Zaliha sai tace “kai minal arage na tomorrow”
minal tayita rantsewa amma zaliha bata yadda ba

Wayan zalihanne yayi ringing ta Duba Suleiman ne dauka tayi yace mata ya iso tace to gatanan zuwa kamin suka fito ita da minal

Jingine yake ajikin motarsa kin 406 Yace lallai ma swthrt dama kawai so kike kiga fiskana shine kika wani cemin minal ta bata minal tace eh hakane na bata amma yanxu na dawo

nan zaliha ta labarta masa abinda ya faru yace Allah dai ya kiyaye na gaba tace Ameen

Hira suka ci gaba dayi abinsu sai wajen azahar tukunna minal tace zata tafi Suleiman yace bari ya rage mata hanya

🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹
………agaskiya hajiya Duba da irin mutunci da karamci da kika nuna mana dukda Cewa kin fimu arziki zamuso kuma zamuyi farin ciki ace Mun hada jini dake saide wani hanzari Ba gudu ita yarinyan bamusan ra’ayinta Ba

Dan! Dan!! Dan!!!

Gaban mom ne ya fara lugude lallai dakyar minal zata yarda da wannan batu Duba da irin abinda yazeed din ya mata saide ikon Allah

Tace to shikenan ga card dina duk shawaran da kukayi sai kusanar dani ko?sukace Insha Allah

Sannan ya Abubakar ya amsa card din

Yayi waje shida baba yayinda inna ta bisu da Karin kumallo sannan ta dawo ta sami mom bata fara Ciba

Tace hajiya kick mana mom tace aike make jira muci tare sannan ki dena ce min hajiya kicemin yar uwa

Toh kawai inna tace sannan ta zauna suka fara ci tana mai kara jin mom har cikin ranta

Wajajen azahar saiga minal ta Shigo alokacin mom ta Dade da tafiya

Baba da ya Abubakar ta gani zaune suna dan hiransu yayin da inna ke dafa abinci

Tsalle minal ta daka taje ta fada jikin sa
Baba yace yi ahankali kada ki karya Mani d’a

/\/\inal tace ai Nayi kewansa ne nan ta jona aka ci gaba da labari da ita can inna ta leko tace a ah har kin dawo kenan? Tace eh
Inna tace ya kika tadda kawar taki minal tace lahiyatta lau kawai de tayi kuka ne baba yace Allah sarki

Inna ce tayi ma baba Alama da ido Cewa ya fada mata

Gyara zama yayi yace AMINATU

Tace na’am baba yace ki saurareni da kyau sannan Kiyi tunani

Tace Toh

Yace nasama maki miji sunansa YAZEED……..

Tofa fans kuna ganin minal zata amince da wannan batu?

Ya ake cikine tsakanin yazeed da
Zakiyya

Ina jiran comments dinku kada ku manta da offer na.

NAGODE

takuce karamarsu babbarsu

24 August, 2019

Miss untichlobanty💕
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by @mzz_untichlobanty🌹

CHAPTER 22

Sunansa YAZEED Dan gidan w…….
Bai karashe maganarsa Ba sakamakon ihun da minal tayi

Alhamdulillah! Baba da gaske ka saman miji ?ai Ba sai Nayi tunani Ba indai gidan akwai abinci shikenan anwuce gurin

Murmushi kawai baba Dan ya fahimci kuruciya na dawainiya da minal fatansa de Allah yasa mijin Ba Yaro bane inba haka Ba to Akwai matsala

Ya Abubakar ne yace iye iye ‘yar kazamar kanwata zatayi aure an girma. Turo baki tayi “ni Ba kazama bace” yace ai na sani nan dai suka ci gaba da sabgogin gabansu

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Salati yazeed yayi lokacin daya bude idonshi
Ganinsa a dakin da Ba nashi Ba yasa ya tuna da abubuwan da suka wakana awanni kadan da suka wuce Wai yau shine matarsa kwance jikinshi batare da tashin hankali Ba balle ace ta tafi office.

Smiling yayi sannan yayi pecking dinta ya tashi ya fada toilet ya sakeyin wanka sannan yayi alwala ya fita domin yin sallh

Koda zakiyya ta tashi wanka tayi  taci abinci sannan ta dauko laptop dasu tablet dinta ta fara Duba business
Yazeed ne ya shigo yace babyyyyyy!har kintashi?

Smiling kawai tayi sannan tace afternoon yace afternoon daga nan ya zauna yana shan green tea dinshi while tana aikinta

After ya gama sha yahau gefenta ya zauna suna Dan taba hiransu


/\/\om tana zaune a dakin ta wayanta ya fara ringing unknown number ne hakan yasa bata dauka Ba sanda aka kara kira sannan ta daga

Salamu alaikum

Wa alaik assalam mom ta fada zaka rantse bata iya hausaba

Mama ina wuni?Abubakar ne yayan Amina

Allah sarki Abubakar ykuke

Lafiya kalau,em……..dama akan wannan magananne Toh ta amince

Alhamdulillah, to ai shikenan next week Insha Allah uncles dinshi zasuzo

To shikenan zan Fadawa baba,ina gaida brother Inlaw

Kacewa su baban Muna godiya kuma yazeed dinma zaiji

Bakomai mune da godiya

Da haka sukayi sallama mom na mamakin yadda akayi minal ta yadda Allah dai yasa Ba’a boye mata wani Abu Ba,emm Allah dai ya kyauta

Minal kam fita tayi zata koma gidansu zaliha bakinnan har kunne
Ahanya ta hadu da su haruna(Yan shaye shayen nan from chapter 2) dauke da wani ghana must go cikeda atamfofi

Ah ah hajiya minal dama kina duniyar nan ?

Eh inanan sai akayi yaya ?

Allah baki hakuri mu Ba masifa muke so Ba

Ghana must go din suka dauka sai nishi suke zasu cigaba da tafiya.

Minal tace amma kude Anyi ragwaye wallahi anji kunya yanzu duk girman kunnan bazaku iya daga Ghana must go 1 Ba ? Sai Anyi magana kuhau cika baki Wai June karfafan anguwa.

Suka ce wa? aimu bazamu hada kanmu dake Ba ina babu ma hadi, saboda cin fiskane agaremu  ace an kwatantamu da mace.

Minal tace wannan kanku akeji sannan taci gaba da tafiyarta Dan taga alamun zasu bata mata rai

Murtala ne yace ma ta “inkincika ke yar malam yusufa baban kowa ne ki daga wannan jakar ance miki kayan wasa ne aciki
😏?

Basu ankare Ba kawai sukaga Ghana must go a sama ta daura aka.

Haruna yace na Shiga uku ni dan mutum 2 jikan mutum 4,murtala munji kunya ta d’aga!

Ajiyewa tayi ta juya zata tafi murtala yace

“Nide ina baki shawara inkinyi aure a gaba karki nunawa mijinki kinada karfinnan Dan wallahi sakoki zaiyi Dan mu maza akwaimu da son mace me nuna rauni ko zata iya Abu ta nuna bazata iya Ba,macen da take nuna Cewa mu muka cika mata kuma muka gyara rayuwarta
kai haruna kama muje”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button