KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

A gidan Alhaji mansur kuwa zaman lafiya ake sosai mom da mama kamar yan uwa dukda ko kowacce tana da kishin ta amma sun girmi wannan AI su dai a barsu da kokarin birge Alhaji mansur ko da inna zasu koma tsokanar sa take wai daga yin aure har yayi kumatu ko kwana uku beyi ba.

A gidan yazeed kuwa minal ce tsaye gaban madubi tana taje gashinta.? Yazeed ya fito daga wanka yazo ya tsaya a bayanta tare da karban cumb din. Murmushi tayi tace kana jiyo mutanen ka fa. Murmushi yayi yana cuku cuku da gashin yace na jisu saka rigarki mu kunna kallon mu. Tace kai bazaka sa ba? Murmushi kawai ya Mata yace zamuyi wasa ne anjima kadan. Girgiza kai tayi tana mamakin rashin kunya irin na mijinta. Tirare ta shafa sannan suka kunna kallo su.

Bayan mintuna sukaji knocking pause suka sa kuma suna daidai inda aljani ya fito ma ayush amma su basa ganin komai. Bude kofar minal tayi bayan yazeed yasa jallabiya. Summy (yar lesbian) ce minal tayi murmushi tace ki shigo. Shigowa tayi ta zauna a kujera kanta a kasa tace kuyi hakuri kun ganni war haka wani Abu na gani shine nace dole in fada muku shin nine ko kuma kun gani

DAN ALLAH KU MAIDA HANKALI NAN WAJEN KAR KU RIKICE ………

tace a CCTV footage Dina ina cikin kallon abinda ke wakana har na ga ayush tana magana ita kadai bayan ta sauko daga gadon kawai sai hotan ya dauke bayan sakan 3 ya kawo amma bata daki. Na duba kaf gidannan ban hanata ba kuma har bayin da mahaifiyar ta take na leka banga kowa ba.? (bazata iya ganin aljanin a camera ba)
Yazeed ne ya duba nasu suma Abu daya ne ya faru hakan ya daure musu kai sosai minal tace karki damu kije ki Kwanta idan ma guduwa tayi San kudin ta zai dawo da ita.

Sigina summy ta Mata cikin tsokana yace wata ta kagu infita toh yanzu zan wuce. Tsaki minal taja tana dariya ta jefe ta da pillow tare da fadin ki rufe mana kofa de. Bayan ta fita jugum minal tayi yazeed ya riko hannunta? yace karki damu komai yazo karshe da izinin Allah wahalar ki ta kare zo kiga wani Abu ya fadi hakan yana janyota jikinsa……….

ABINDA ya faru kuwa shine tun a can baya lokacin da alama su minal munafurci kasa kasa yazeed ya soma bjncike kamar yadda kuka sani Wanda hakan yasa ya zargi goje cewa shi ya saka musu kayan Maye abin sha Dan basuda wani makiyi sai shi. Garin binciko ne ya gano cewa goje (Dan uwan lailai matar ya Abubakar wanda har yaso ya Mata fyade Allah ya sha da ita.) yana auren ayush kanwar zakiyya abin ya bashi mamaki sosai. Hakan yasa ya hada one plus one dinshi yadda akasa lukman ya auri zaliha maybe shiyasa take daukan fansa hakan yasa ya zurfafa bincike Dan ya tabbatar kar yayi kuskure toh amma yana bukatar Wanda zai shiga jikinta ana cikin haka har wata rana summy tazo neman aiki amma babu vacancy.

Marainiyace daga ita sai mahaifiyar ta mara lafiya hakan yasa ta hakura da zama babbar mace ta nemi aiki a companyn yazeed. Sosai ta bawa Jamal tausayi yake bawa yazeed labari nan yazeed yace ya nemota akwai aikin da zata mai.
Koda tazo yazeed ya sanar da ita yadda zatayi ta shiga jikin ayush har ayush ta yarda da ita ta dinga bata mission sannan ya Mata gargadin kisa idan tayi kuskure tunda lokacin ko tunanin retire baiyi ba. Ita kuwa abin nema ya samu dama yar karya karya ce amma ba yar lesbian ba. Ta zama yar lesbian ba karya ne duk a cikin shirin yazeed Wanda minal ce ta bada shawara.

Numbar ta ya karba sai yaga ashe ma yana da ita. Numbar da ke chatting da zakiyya ne lokacin da zatayi tafiya. Yace menene hadinta da zakiyya? Tace kawai ita burinta ta dinga shiga cikin manyan Mata hakan yasa duk group din da akwai manyan Mata toh sai tayi karya karya ta samu ta shiga anan ta samo numbar zakiyya yazeed yace matarsa ce zakiyyan Dan haka tayi hankali.

Ana cikin haka ne har ayush din tasa summy tayi kamar tayi zina da zakiyya da sauran duk abinda ta sata yayinda take surfowa su yazeed rahoto su kuma sunata tara shedan da zasu bawa zakiyya si nuna Mata cewa yar uwarta ba yar uwarta bace kuma ba mutumiyar arziki bace saide kash suna planning su tona Mata asiri idan minal ta haihu ranan suna a Mata tsamo tsamo amma kafin sukai ga yin haka tayi musu tsafi.

Bayan sun warke kuwa gani sukayi tunda batasha jibgar gidan suna ba dole su Rama abinda ta musu kamin su Dan ka ta hannun yan sanda ayi kasheta tunda itama ta kashe jarirai.

Acikin gaba daya tafiyar rayuwar sun nan akwai muhimmin Abu da suka fahimta. KAYI KOMAI AKAN LOKACIN DA KAKE DA SHI DAN BAKASAN YA GABA ZATA KAYA BA KARKACE ZAKA JIRA WANI ABU, SANNAN DUK WAYONKA BAKA IYA TSALLAKE TSAUTSAYI DA AJALIN KA.

Abinda summy ta fahimta kuwa shine DUK LOKACIN DA KA DAGE SAI KA SAMU ABU TOH WAHALAR BANZA ZAKACI KO KA SAMU BE ANFANE KA BA KO BAZAKA SAMU BA. LOKACIN DA KA KOMA GA ALLAH KUWA IDAN YAGA DAMA YA BAKA ABINDA KAKE NEMAN A DUNIYAN KUMA YA KARA MAKA DA ALKHAIRI A LAHIRA. Matar da ta taimakawa mom tabar gidan mahaukata kuwa ba kowa bace illa mahaifiyar summy wayo sumaiya. Yazeed ya biya Mata kudin magani ta warke har ya nema Mata aiki amma bayan wasu shekaru ta rasu.

CIGABAN LABARI

safina asararriyar matar yazeed tana baccinta me dadi take jiyo hayaniya sama sama har ta farka jin mommy ce yasata yin tsaki tace tsohuwar nan zan Mata wulakanci wallahi bazar bazar ta shigo dakin mummy ta sameta shaman cikin fitsari tana mazari tsabar tsoro.

Tace tsohuwar munafuka ya akayi mummy tace kinga yar albarka safina taimaka ku ciro ni. Safina tace jibgegiya dake saide in jaki mummy tace nide cireni daga bayin nan kinji matar kirki. Tace badan halinki ba kawo hannunki. Sannan ta taimaka Mata gyara jikinta tayi sannan suka zauna a bakin gado yadda kasan shiri sukeyi tun da.

Cikin son jin labari safina tace wai ya akayi ina aishar? Mummy tace ke bar batun yar iskan nan ai yau na leko barzahu na dawo. Safina tace ban gane ba labarin tass mummy ta tsara Mata ta nutsu ta shanye tas sanda mommy ta gama tace kuma sai akace miki zan yarda? Kai mummy kin iya hado ta mummy tace nima ban yarda da ayush ba sanda na gani.

Yin duniya mummy tayi safina bata yarda ba daga karshe ma dariya ta sheke dashi ta koma dakinta. Ta kwanta tare da kashe wuta ahankali ahankali iska ke kadawa a jikin labule yana kara karfi kofofi da da taga ne suka fara kara ga bakin kura yana kadawa hajaran majaran. Ruwa mai karfi ne ya tsinke tare da cida daidai lokacin kuma yazeed ya sumbaci minal yayinda safina…………

???BANCEWA KOMAI KAWAI KAR KU MANTA DA VOTING, COMMENTING TARE DA SANAR DA KAWAYEN KU SUMA SU KARANTA.

ALLAH TA VAR JAUNA SANNAN YA KARBI IBADUN MU BAKI DAYA.

Miss untichlobanty ?

17th may, 2020.

? CHAPTER 95?

Yin duniya mummy tayi safina bata yarda ba daga karshe ma dariya ta sheke dashi ta koma dakinta. Ta kwanta tare da kashe wuta ahankali ahankali iska ke kadawa a jikin labule yana kara karfi kofofi da da taga ne suka fara kara ga bakin kura yana kadawa hajaran majaran. Ruwa mai karfi ne ya tsinke tare da cida daidai lokacin kuma yazeed ya sumbaci minal yayinda safina…………

A bangaren ayush kuwa aljanin nan daureta yayi kullum zaizo ya sha jininta bayan azaba da yake Mata da wuta tare da bata tafashasshen ruwan diwa mai jini da azabar wari. Gashi bata ganin komai sai jarirai. Kullum tamabayar ta me tayi masa? Ganin ta dameshi yasa yace ke saurara kiji, nine aljanin da aka tura na mantar da kowa da sharadin duk randa suka sake yin aure zan rasa nawa auren ba wannan kadai ba matar tawa ni zan kashe da hannuna.
Dan haka yanzu na rasa matata, amarya ta a sanadin ki shiyasa ya zama dole ki zauna da ni.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button