KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Minal ko murmushi take tana binsu da idanu Dan batada abin Cewa
Aikin sukayi kokarin karba minal tace ah ah sukace to shikenan suyi tare kamin ta yarda amma dukda haka tana tsoran kar yazeed ya ganosu 

Su kuwa sai hira suke mata yarda tambayarta ko zata kwana musu Dan sunaso suyi kawance da ita tace musu ai Ba kwana Ba kwanaki ma zanyi ta fadi haka tana bawa kwanakin karfi, aiko sunji dadi Dan su nasu gane me take nufi ba

kafin karfe 10 sun gama Komai saura part din yazeed Wanda dama tunda basu ke gyarawa Ba lukman ne kuma yazeed yayi masa message Cewa Ba sai yazo Ba.

Su atine sai janta suke da hira tun tana nokewa har ta saki jikinta sumo abin ya musu dadi, binta tace ni wallahi na kosa naga amaryar Allah dai yasa Ba irin madam zakiyya bace

Atine tace yo imma batada mutunci ai ita ya shafa minal de tayi tsit tana jinsu
Minal tace to ita bari taje sama tayi wanka larai tace Wai ko kema bikin kikazo ne naji kina Cewa bari kije sama kiyi wanka ? Rasa amsar da zata nasu tayi sai atine tace kinada kayan sawa?
Binta tace ki wani tambaya dole da kayanta zata zo mana

Minal tacewa atine Dan Allah kinga rabu dasu zo Kiyi mini wani taimako

Sukace to sai kun dawo kamin su minal suka wuce dakinta ta cire hijabinta sannan ta kalli atine

Atine ko zare idanu takeyi domin in batayi kuskure Ba nanne dakin da aka kawo Amarya

Minal tace kinga kwantar da hankalinki nice amaryar ni zoki nuna mini Inda zan sami kayan sawa
Atine ta zaro ido tace Kece ME?

Minal tace kinga shiyasa ma ban dadi muku Ba saboda ban Shirya yin bayaniba zoni ki nuna Mani

Nuna mata dakin dressing atine tayi da yadda zata canja combination din saga 00000 sannan mata na toilet ma

Kamin ta fita tana mamaki da kuma al’ajabi minal kam wanka tayi sannan ta koma parlour jin shiru yazeed bai fita Ba yasa tace kika ma ya five run asuba idan Ba haka Ba ya za’ayi ace mutum yana bacci har 12.

Alokacin data koma kitchen domin dauko su tsintsiya su atine na kitchen din Suna cin abinci Suna ganinta sukayi caaa Wai meyasa bata fada musu akwai chemistry a tsakaninsu da oga sir Ba ?Wai kuma me yasa oga sir ya mata abinda ya mata kaman wata 3 zuwa 4 da suka wuce?

Murmushi tayi tare da tabe baki tace sirrin ne

Daukar tsintsiyarta da packer tayi ta wuce side din yazeed

Kirjinta ne ya fara tsinkewa karfa yaje yananan,hakan yasa ta fara sanda Kamar Mara Gaskiya sannan a hankali ta bude kofar da take ganin side dinshi ne tunda de tasan na mom

Leko kanta tayi taga……….

Me tagani?

Uhm kun ganni all of the sudden ko?ai bazan iya babu Ku bane kun zama wani bangare na life dina.

Ina sonku sosai fans dina😘
Don’t forget to vote,share and comment

Miss untichlobanty💕

4th October, 2019
[1/11, 1:54 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

CHAPTER 28

Leko kanta tayi taga wani tsararren parlour wanda bata taba ganin irinsa Ba
Ko babban parlourn dake gidan taga baikai wannan kyauba dukda ko wannan din Ba wani girma bane dashi na hauka amma ya hadu

Kamshin daya bigi hancinta ne yasata dawowa saga tunanin data Shiga ga wani AC daya bugota har yanasa tsulan cikinta tashi
Shahada tayi ta Shiga da yar karamar sallamarta Wanda ko ita kanta bata jishi dakyau Ba

Sanyi ne sosai a parlourn Dan har tadan soma rawar dari a kasan ranta tace kaji daki sai kace cikin fridge Allah yaso da hijabi nazo….
Kalle kallenta tayi kamin ta soma abinda ya kawota

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Yazeed kuwa tunda ya Komai bacci bashi ya tashi Ba sai around 12:00pm
A yangance ya tashi daga kan gadon nasa ya sauka Kamar bayason jikinsa ya rabu da lallausar katifar
Bandakinsa ya bude Wanda yaje tsaf Kamar Ba namiji ke amfani dashi ba, wanka yayi kamin yafito ya shafa mai yana tunanin yadda rayuwa ta juye masa

Wai yanxu shine yake da mata biyu,Wai jiya shi aka kawowa amarya kuma ma shi Ba wannan ke damunsa Ba
Ace mom ta rasa Wanda za’a aura masa kar fadin duniya sai wannan yarinya,wannan fitsararriyar,wannan gold digger din.
Hmmm nannauyan ajiyan zuciya ya ajiye sannan ya fara shafa wani mai me kamshi ajikinsa a hankali Kamar bayason ya shafa.
Daga mutum ya gansa yasan Cewa lallai wani Abu na damunsa dukda ko hakan bai yiwa kyawunsa wani lahani ko sauyi Ba

Ahankali ya tashi yana tafiya Kamar bayason yayi tafiyar,Ahankali ya Daga Zara zaran yatsunsa Wanda ke dake da fararen nails ya danna pin din dressing room dinshi ya Shiga sannan ya tsaya agaban wata kofa na glass a hankali ya bude sannan ya dauko wani gray hoodie tare da black three quarter.
Drawan under wears dinshi ya bude sannan ya dauko gajeran wando amma banda singlet jin Kamar motsi a part dinshi yasa ya leko
Amma baiga kowaba hakan yasa ya koma ya sanya kayansa cikin nutsuwa
A hankali yaji kamar an bude kofan dakinsa Dan haka ya kara lekowa domin ganin Waye Ba tare da dauko socks din dayayi niyya Ba.

Stake Dan guntun annuri dake tattare dashi ta dauke. Minal ya gani tana leken dakin domin tabbatar da Cewa bayanan ajiyan zuciya ta sauke tare da shigowa da Dan karfin guiwanta amma Ba a rashin nutsuwa Ba.

Baice mata kala Ba itama bata lura dashi ba domin kuwa idanunta ta ware bil hakki da gaskiya tana basu abinci

Jingina yayi a bakin kofar da yake sada dakinshi da dressing room din yana kallonta kawai yama rasa mai zaice ko yayi mata

Sanda ta karewa dakin kallon tas tanata murmushi Kamar wata shashasha

A hankali ta tube hijabin dake jikinta tayi wulli dashi kan stool din dake gaban mirror Wanda tayi nadamar yin hakan domin atake wani sanyi ne ya daketa Wanda har yafi na falon hakan yasa tadan shafa jikinta

Wannan hali nata tunba yauba inna ke fama da ita na cillar da hijabi ta ko’ina Ba tare data ninke Ba acewar inna wata rana Zara wulla kan Dan aljani

A hankali ta karaso izuwa bakin gadon sannan ahankali ta janyo bargon dake kan gadon kamshin yazeed ne ya daki kofar hancinta Wanda yasata lumshe idanu tare da kara bude kofofin hanci domin ta shaki kamshi

Wani Abu taji yana mata yawo ajiki amma ta share Dan a halin yanxu bata bukatan wani distraction

Abangaren yazeed kuwa kallonta ma kawai yake takaici ya cika masa zuciya Kamar ya mata suka ya rasa yadda zaiyi

Wani karago ne ya tsaya masa a makokoro flinching and unflinching fist dinsa kawai saiya Komai cikin dressing room din nasa

Minal ko ninke bargon tayi sannan ta ajiye badan ranta yaso Ba sai Dan kada hawan jini yazo ya tarar da ita a dakinsa (aikin gama ya gama)

Gadon ta fara gyarawa sanda ta gyara tsaf sannan ta kalli gadon gaji batada burin dayawuce ta kwanta akai

Kunji mutuniyar Ku fa na dakinta ma anhanata hawa balle na oga kwatakwata

Aiko kankace me,saiga minal ta tsuguna a gefen gadon sannan ta daura fuskanta akai tanashafa gadon da hannunta mai dauke da baby fingers masu tayi da laushi Wanda suka sha lallen amarci

A hankali ta mike sannan tayi abinda ya kawota dukda Cewa dakinnasa Ba wani datti bane dashi domin yazeed dinma Ba baya bane wajen tsafta.

Tas ta gara Komai sannan ta dibi kayan aikinta tayi gaba tare da manta hijabin nata adakinsa.

Shiko yazeed koda ya fito ya kalli Inda ta ajiye hijabin kwafa yayi dabadan dukan mace baya birgeshi Ba da babu abinda zai hanashi gyara mata zama,aiyana irin zaman dazaiyi da ita na halin ko in kula acikin gidan yake. Daga karshe ya tashi ya bude wani kofa na daban Wanda shi kuma balcony dinshi ne. 
Mika yayi tare da furzar da iska yana mai shafa lallausan sajen dake habarsa Wanda suka a kwance luf luf.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button