KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Jikin minal ne yayi sanyi taji ta tausaya musu. Dukda batasan labarinsu ba tasan sun Shiga gararari gunjin kukan da taji ne ya dawo da ita Daga tunanin da ta shiga. Ganin su tayi rungume da juna Suna kuka.

Safwan yace wallahi dadynmu baya sonmu ya tsanemu kuma momyn mu ma ta tafi ta barmuuu???bamuda parents rungumesu minal tayi tare da basu hakuri sannan tace karsu zamu ai suma iyayensu ne ita da zakiyya momynsu ne kuma yazeed dadynsu ne.

Sallah ta koya musu tare da fada musu with time zasu koyi komai da akeyi a cikin sallah Karfe 9 tayi musu wanka tana cikim shafa musu mai yazeed ya Shiga fuskan shagwaba yayi mata yace kin barni ni daya yarannan sun kwacemin ke. Dariya tayi tace gaba daddy karatu fa mukeyi yazeed yace haba? yara na Ku tabba kun maida hankali kunji. Mommy kizo muje daki.

Tace daddy ka shirya sahir toh saboda mu tafi da wuri tunda shi na shafa shi. Cuku cuku yazeed ya dinga yi da kayan har minal ta gama Shirya safwan sai dariya suke masa safwan yace daddy kanaso inyi maka karatun da mommy ta koyamin? Yace eh kamin muji karanta mai yayi sahir ma yayi yace good good very good for my sahir and safwan. Ku kwanta Kuyi bacci. Safwan ne ya rike hannun minal tare da mata puppy eyes yace momy dake zan kwana. Yazeed ne ya lallabasu tare da musu alkawari kamin su tashi Daga bacci minal zatazo kamin suka hakura.

Koda suka Koma daki suna rufe kofa yazeed yayi hugging minal tare da fadin i missed you baby. Murmushi tayi tace me too.

Zaunar da ita yayi a bakin gado sannan ya mata godiya akan yanda ta rike amanan su sahir.

Murmushi ya mata yace sweetheart rufe idonki. Zan baki surprise.
Rufe idon tayi can yace open your eyes tana budewa ya mika mata form karba tayi ta Duba taga na jamb ne Dana WAEC da NECO tsalle ta daka ta rungumeshi tare da fadin Alhamdulillah zan Koma makaranta.

Dadi yaji aranta yaja kumatunta yace baby girl da Nasan komawa makaranta zai saki wannan farin cikin da na mayar dake tun randa na auroki.

Karatunsu su kayi bayan sun cika form sannan suka kwanta yazeed na fada mata zai tafi wani mission yaso ace da ita zashi amma bazai yuwu ba saboda rananda zai tafi ranan za’a fara WAEC shagwaba ta dinga yi masa har sukayi bacci.

Da sassafe taje ta tashesu safwan sukayi sallah sannan suka Koma bacci.
Dawowa tayi ta kwanta around 7 ta daura breakfast tare da hada na Yan hospital. By 10 kowa ya gama shiru anci breakfast sannan suka hadu a parlour domin tafiya asubiti su Mashkur sai santin abincin suke.

Yazeed ne ya nufi kofa ya juyo ya tabbatar kowa bata kallonshi sai ya kashe wa minal ido tare da blowing kiss abinda bai saniba shine kowa yana fakonsa Dan haka aka fashe masa da dariya ya Daga kai ya fice yana mai danne dariyarsa.

Fans Kiyi hakuri wallahi na zama busy daya wa ne shiyasa chapter din babu yawa love you all

??KURUCIYAR MINAL??

by miss untichlobanty

?CHAPTER 66?

Hospital din dasu ayush suke suka fara zuwa nanma likitan yace baza’a iya moving dinta ba saide nanda Dan wani lokaci yazeed yace karka damu wannan da kake gani? ya kware a fannin shiyasa na kirawoshi yazo har kasannan so he can take care of her condition. Doctorn yace mr yazeed are trying to say mu bazamu iya aikin mu bane ? Yazeed yace ba haka nake Nufi ba. Inaso be dai ayi moving dinta hospital da take akwai komai and tight security. Dr yace ok I will try my best domin keyi moving dinta amma yanzu Kam mashkur yace can I check on her? Dr. Yace that’s against the rule tunda ba a hospital dinnan kake aiki ba sannan permission da aka baka is only restricted to (iyakarsa)FIRST CLASS MULTI SPECIALIST ne idan ba under emergency ba wato bukatar gaggawa.

Yana gama fadin haka ya wucesu tare da shigewa office dinsa dama saga dakin da ayush ke kwance ya fito.

Kebewa gefe yazeed da mashkur sukayi Dan yau ba’a taho da luku guy ba.
Acewar yazeed ya zauna ya angonce.

Kuskus suka fara mashkur yace nifa ban yarda da likitan nan ba. Idan ba haka ba ya za’ayi yace baza’a iya moving coma patient zuwa wani hospital ba alhalin she is out of danger?
Wanda akwai risk ma shine idan za’a fitarta waje kuma shima za’a iya. Yazeed yace ni dama can bai kwanta min arai ba so abinda zamuyi mu dauki abunmu mu mayar gida sai ka kuka da ita sauran sai a barsu a hospital Dincan ko kaga za’a ragewa my zakiyya wahala ma.
Mashkur yace haka zamuyi nan suka sanarda mom tace hakan ma yayi Dan kallon da likitan ke Mata bai kwanta Mata ba domin kallon banza take Mata na yan iska domin akallon da yake Mata babu alamun aure yake sonta dashi.

Ran yazeed ne yayi mugun baci Dakyar suka lallabashi ya huce. Koda suka fadawa dr din tuburewa yayi aishi Sam Baza’a fitarda ita daga nan ba yazeed ne yayi kwalarsa tare da yarfa mai tafi sanda bakinshi ya fashe yace na baka 30min a shirya komai domin mayar da ita gida. Zamuyi arranging komai kaji ko? Da sauri ya daga kai yazeed yace maza maza go to work.

Kafin minti 30 an shirya komai sannan aka hadasu da nurse yazeed yace bayaso zasu iya kula da ita sannan zasu dauko nurse daga asubitin da suke zuwa wato FIRST CLASS kuma kabilar China ce ma.

Aiko haka akayi bayan an mayar da ita gida tare da nurse dinta akace mom da minal su zauna a gida ujili ujilin yayi? yawa. Minal ce ta lallabo zakiya akan taje tayi su Wanda ta shirya taci su abinci ba musu tayi koda ta fara cin abinci kawai sai ta fashe da kuka a tsorace minal da yaranta sukayo kanta suna tambayan lafiya tace tunda nake ban taba cin abinci mai dadin wannan ba saide abin takaicin ni ko abinci ban iya dafawa ba amma yarinya kamarki ta iya sai yanzu nake nadamar rayuwar da nayi a baya dadina daya Danayi nadama run lokaci bai kuremin ba yake yar uwata amina shin zaki koyamin rayuwar zaman aure? Daga kai minal tayi zakiyya ta kuma cewa shin zaki koyamin addini na? Minal tace da izinin Allah sauko wa kasa tayi ta rike kafafun minal tana fadin na roke ki da Allah ki yafe min duk cin mutuncin da na miki.

Dagota minal tayi ta sauri tana fadin babu abinda kikamin Wanda naji haushi ma na yafe miki tun da dadewa Allah ya yafe mana Baki daya daganan suka rungume juna cikin farin ciki. Mom dake sama tana kallonsu ta share guntun kwallarta yayinda su sahir suka fara tsalle da waka suna fadin mommy da mommy sun zama kawaye!
mommy da mommy sun zama kawaye!!

Dariya su minal sukayi kamin zakiyya ta share kwallarta taci gaba da cin abinci can tace toh yanzu kamin komi ya kankama mu fara karatun me zaki fadamin Wanda idan na rike bazan tabe ba.
Murmushi minal tayi tace idan akace Allah ya hana Kaza ko annabi ya hana toh karkiyi komin dadinsa domin zaki iya mutuwa kina aikatashi akwai situation da idan kamar Ansaki kiyi ok a kasheki toh idan fada akace kiyi sai ki fada amma niyarki ta kasance a tsarkake idan ko aikatawa akasa ki kiyi misali kisa to karkiyi gara a kasheki saboda ta iya yuwuwa Wanda akasa ki kashe din rayuwarsa tafi taki anfani ma al’umma toh kinga gara ki mutu da ya mutu kinga kenan Kamar kin ceci Ranshi ne kuma kinyi shahada tunda kasheki akayi. Manzon Allah (SAW) yace Duk Wanda ya cecin ran mumini Kamar duniya ya ceta sannan duk Wanda ya kashe mumini toh kamar ya kashe duniya ne baki dayanta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button