KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Good morning na cika alkawari,please make sure you spread a smile on my face comment and vote fah

Have a good day bye

Miss untichlobanty💕

28 November, 2019
[1/11, 2:28 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by @mzz_untichlobanty🌹

CHAPTER 47

Da safe jiki babu kwari minal ta fito ta fara aikinta koda ta kammala,tayi wanka sannan lokaci zuwa lokaci takan sauko ta Duba dinning table ko yazeed ya sauko domin ta share dakimshi tunda yace bayason ya kara ganinta.

Komawa tayi dakinta ta zauna Jim kamin ta janyo wayarta sai alolacin ta tuna batada numbern zaliha kawai sai kawai taje gaban madubi ta shafa powder da lipstick saboda rage lokaci Kuma tayi kyau Ba laifi.

Fitowa tayi daga dakin aranta tana Cewa Nasan ya fita ma tunda safe kuma ko na hadu da shi ma nuna masa zanyi ina fushi dashi muga yadda zaiyi. Murmushi tayi kamar wata shashasha ko yadda yara keyi Idan sun kulla wani abin.

Laundry room ta Shiga ta dauko kayansa set 2 data goge dazu ta nufi part dinsa koda ta Shiga Ba kowa kuma parlourn nasa ma da duhu alamun babu kowa tace Ahe duk jirannan danayi na banza ce bayanan ma.

Ta bangaren yazeed kuwa Kamar jira yake ta Koma daki sai gashi ya sauko, kitchen ya nufa ya dauko hollandia yoghurt plain flavour saboda na fridge din parlourn sa ya kare sannan ya dauki cup ya fita.

Dakinsa ya Koma yasha yoghurt dinsa Dan baya mood din cin abinci. Kwantawa yayi abinsa ruf da ciki yana mai kashe wutan dakin sannan ya rufe idanunsa once in a while yana murmushi.

Da confidence dinta ta tura kofar dakin Dan ba’a rufe kirif take ba sai ta dauka ko ya bar mata ne Dan tayi shara Kamar yadda yasaba bari Dan haka bata kawo Komai cikin ranta Ba ta shigewarta.

Hijabin dake jikinta ta cire tayi cilli dashi akan gado sai kan fuskar yazeed Wanda dama tun dazu yaji takunta kuma yasan ta shigo dakin amma ita batasan da zamansa Ba. Baice uffan Ba balle ya motsa yayi luf cikin bargonsa sai kansa dake waje wanda yanzu yake lullube da hijabin minal. Tunani yake aransa yarinyarna badai sa hijabi Ba kam. Allah yasa da kyakkyawar niya ce.

Ajiye kayan tayi akan stool kamin ta dafe goshinta da hannunta tace ni yanzu ya zanyi ? Kullum yananan yana budemin wannan yar iskanci kofar dakin kayan nasa to yau kuma bayanan.
Kicin kicin tayi da ido tace Idan na kamo yaya yazeed dinnan sai na naushi bakinsa. Sai kuma ta kyalkyale da dariya tace Wai wayaganni na danne ya yazeed sai jibgarsa nake.
Wutan dakin ta kunna kamin ta dauko kayan aikinta. Ganin bargon NASA a wargaje yasa tace kai Ashe ya yazeed dinma kazami ne fadin jumlar tayi daidai da janye bargon aiko atake ta kwala ihu zata arta a guje yayi saurin wantsalota ta fado jikinsa kokarin tashi take tanata tuttureshi amma ya riketa gam hannunshi ta fara mintsini tana Cewa ya yazeed ni ka sakeni nifa Ba yar iska bace. Bai kulata Ba illa ma tashi da yayi zaune sannan ya ajiyeta akan gadon couch ya Koma ya zauna sannan yace rosy cheeks gyara gadon kizo in fada miki wani Abu. Dan hade fuska tayi tace me zaka fadamin? yace sirrine a kunne ma zan fada miki tace toh……….

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Zakiyya zaune a parlourn gidansu Amarya tana oiling ma ayush din gashi Wanda Ba yabo Ba fallasa.
Wayanta ne ya fara ringing ta dauka kamin tayi magana akace madam the boutique has been on fire mun kira fire service sun kashe but we couldn’t retrieve our goods.
Zakiyya da batasan sanda mike Ba tace what?how comes? Are crazy? incoming call taji hakan yasa ta Duba ganin sectary dinta ne yasa ta datse da gaggawa tana mai Cewa hello maryam wani irin nonsense nakeji Wai boutique ya kam……….

Bata karasaba Maryam tayi Sauri Cewa Ba nonsense bane ma munyi gobara, the came out of no where. Yanzu haka ina hospital saboda na none a gefen hannuna amma Ba wannan Ba new boutique dinma an Shiga an kwasge kayan tas sanna aka rusa ginin.

Take zakiyya ta yanki jiki ta fadi kasa sumammiya. Ace sukiyar da tayi shekara kusan 5 tana Tarawa cikin minti 5 babu su?ina impossible.

Inda Allah ya taimaka baki nasu wani hallara Ba tunda har yanzu saura 4 days a fara shagalin bikin ma Dan haka akayi asibiti da ita.

Sanda tasha drip 6 a rana daya dukda ko bata farfadoba saboda tsabar shock.
Yan gaisuwa kam sun kasa karewa an mayarda asivitin Kamar gidan Suna sai Shiga da fice ake.
Ayush zaune akan wani kujera a gefen gadon zakiyya taga Kamar hannunsa yana motsi. Rike hannun tayi ta fara jijjigawa tana kiran sis?sis sannu kinji ? A hankali zakiyya ta bude idanunta aiko babu bata lokaci hawaye sukayi sallama suka bemi mazauni a idanunta.

Mamanta ne tazo kusa da ita tana lalkashinta kamin tace Kiyi hakuri zakiyya akan namiji kike Neman kashe kanki? Sakinki yazeed din yayi ayush ne tayi saurin Cewa gaba mama saki kuma ? To mema zakiyyan tayi da za’a saketa?
Mama tace to inva saki Ba mezaisa ta sume har gadon asibiti caraf akaji zakiyya tace dukiya, dukiya itace abin da ta janyo.
😭mama dukkan dukiyan Dana Tara sun tafi,mama tace ban ganeba, zakiyya tace Nayi gobara babu abinda ya fita a boutique dina.
Dakin dake cike da mutane ne ya kaure da Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un.
Nanfa Yan Jaje ma suka fara rububi anata kawo gudun muwa.

🌹…………………

Abangaren malama zaliha kam Ba kanta Dan yanzu tadan dawo daidai Inda tace Allan katafur sai an nemo lukman ya saketa, ita bazata iya cin amanan Sulaiman Ba. Mahaifinta da aka sallamo washegarin faruwar abin ya nuna farinciki sosai dajin Wanda ya aureta.

Ganin dai kowa yanason auren yasa ta saduda amma da sharadi bazatayi zaman aure dashiba. Side ido suka zuba mata Suna kallon ikon Allah so saikace hauka? Allah dai shi kyauta ya kuma bata lafiya Dan gani suke ta tabu.

🌹……………………..

Laila na zaune a dakin da mahaifiyarta ke kwance rai a hannun Allah. Aunty kuma ta Koma gida bata dawo ba goje ya bankado kofar dakin. Harararsa tayi tace me ya kawoka? Murmushi yayi cikin muryarsa ta Yan shaye shaye yace rayuwar Abubakar na cikin hatsari.

Laila tace what? Wani Abubakar din ? Yace Abubakar Yusuf dai da kika sani Kiyi sauri.

Batasan Inda take wulla kafunta Ba hankalinta tashe tana rokan gone da ya hanzarta kar wani Abu ya sameshi
Koda suka fito farfajiyar asibitin babu kowa Duba da Cewa magriba tayi wasu masallatan ma har sun kira sallh matse bakita yayi kamin ya cusa mata tsimma ya daure sannan ya sakata a Booth.

Figar mortar yayi yabar farfajiyan asibitin wani gida ya kaita ko ince irin dakunannan da samarin yanzu Yan Abu yarima ashana kida,Yan zaman kashe wando keyi. Banda warin sigarin ,hamamin amai da zarnin fitsari babu abun da dakin keyi Ba Komai bane a ciki illa katifa sai karamar TV da wata akwati daya sai kwalaben giya a gefe da dusan sigari.

Cirota yayi Daga booth din ta hada gumi tayi jagab ya fara janta zuwa cikin dakin, turjewa ta farayi ya gaura mata mari take ta fashe da kuka. Hankadata ya dingayi har ya wullata kan katifan sannan yace zan since miki baki domin ya zama dole in dan dana su amma Idan kika sake kikayi ihu kinga wukannan daina Burma mini ita da fatan kinajina ? Hararsa tayi yace wallahi wannan kallon wani irin shauki yakesamin.

Since bakin yayi kamin ya kara da Cewa gara kiban hadin kai muyi mu gama lafiya asirinmu a rufe.
Tace wa’iyazu billah aini ina Neman gafarar ubangijina na shigowa wannan dakin da kuma zama a wannan katifar da bansan sau bawa akayi zina akanta ba. Ka since min hannuna! Bara kaji Wallahi tallahi karshenka bazatayi kyauba.
Kuma haihuwarka asarar nakuda da ragon Suna ce.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button