KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Yayi hakanne dan ya tsokaneta amma ga mamakinsa yaga tasa hannunta cikin nashi sai gashi ya mike.
Zaro ido yayi abinda bai taba yiba  hakan yasa wani sihirtaccen kyawunsa ya fito cike da mamaki ya kamo dantsen hannunsa ya na lagutsawa itako ji take Kamar ana mata cakulkuli Dan haka ta soma dariya tana kokarin ta kwace.

Cikin sa’a ta kwace hannunta yazeed ya biyota yana fadin ai baki isa ba, ina kika samosa karfinnan yar kazame?kode namiji na aura ?

Haka suka dinga kewaye dakin Suna dariya kamin Daga karshe yazeed ya samu ya cafkota. Ga mamakinsa kawai sai ta rungumesa sanda ya dauki Yan sakanni ya dawo Daga shock din daya Shiga kamin shima ya kewaya hannunsa a kwankwasonta.

Babu abinda ke tashi a dakin sai sautin nufashinsu kamin minal ta datse shirun ta hangar Cewa nagode.
Yazeed yace namefa tace na Komai ma.
Shima yace nima na gode ta.turo baki tace kwaikwayona kakeyi?ya girgiza kai tace to kaima name yace nima na Komai dukanshi tayi a kirji sannan ta falfala a guje tana fadin aradu kwaikwaya na kayi.

Murmushi yayi kamin ya fito parlourn ya sameta har ta zuba plate daya zata zuba wani yayi saurin riko hannunta yace me kike shirin yi?tace abinci nake zubawa mana yace a wuri zakisa mana ta zaro ido a karo na 5 tace kana nufin tare zamuchi ? Ya Daga kai tace a ah ka……

Bata karasa Ba sakamakon pecking lips dinta da yazeed yayi yace banasin korafi zuba mana.

Zubawa tayi ta cika plate din harda tozo yazeed yace Wai mu bawa zamuci abincin ne ?tace mu biyu mana yace shine kika zuba dayawa haka sai kace mu 5 ne?
Murmushi kawai tayi ta rufe flask din .
Dauko plate din yazeed yayi yakai kan carpet yayinda yaje riko da dayan hannunta.

Masu Neman update gashinan an muku

Miss untichlobanty💕

4th December, 2019
[1/11, 2:28 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by miss untichlobanty🌹

CHAPTER 50

Janyota yayi har gaban abincin ya zaunar da ita sannan shima ya zauna itakam kallonsa kawai takeyi.
Idan tace ta taba tunanin yazeed zai zama haka to karya takeyi. Da bayan aurenta da sati daya wani ya fada mata Cewa yazeed zai zama haka da babu dalilin dazai hanata jibgarsa.

Shiko yazeed ganin ta tsareshi da ido yasa ya hura mata iska a fuska yace yar kazame ya akayi ne?ko duk Kyan nawa ne yasa ki yin muhawara da zuciyarki?

Bata rai tayi tace duk Wanda yacema kanada kyau to ya cuceka, yace zama ki fadi Gaskiya ‘Yan mata.

Plate din data rufo abincin ya bude aiko atake yaji wani irin kamshi ta doki salansar hancinsa hakan yayi sanadiyar cikinsa ta bada wani kqra kuuuuu.

Minal ne ta kyalkyale da dariya yazeed kuma ya turo baki yadda take masa yace yar kazame banaso! Gwaliyo tamai tace nima banaso.

Spoon ya dauka ya dibi loma daya ya fara taunawa wth a straight face. Minal da ta nutsu tana jira taga reaction taga ya yatsine fuska. Take idonta ya cicciko da kwalla yazeed ko harararta yayi cikinbdaga murya yace me wannan kika Fadawa mutane.
Take hawayen dake makale a idonta ya gangaro tace kayi hakuri ni wal………
Hannu ya Daga mata yace karki wani bani hakuri ya zaki Fadawa mutane abinci Kamar abincin Yan aljanna?so kuke na suma?

Tsayawa kallonsa minal tayi baki a bude yayinda ya sheke da dariya sanda yayi mai isarsa sannan.

Yasa Hannu ya rude mata bakin yana Cewa kar kuda ya Shiga bakinki,maganin mai cemin banida kyau.
Kicin kicin tayi da ido kamin takai masa naushi ya fara tarewa yana Cewa haba yar kazame na yi hakuri,haba yar kyakkyawa.

Hararansa tayi tace kaci sa’a.
Hannu tasa ta dumbuzo loma,yazeed Wanda ke shirin fauna lomarsa ta biyu ya kware a take saboda firgicin katan loman dayaga minal takai baki sannu tace masa sannan ta bashi ruwa yasha ta dawo ta gefensa tana shafa bayansa tunda dazu fuskantar juna suke.

Bayan numfashinsa ya dawo daidai yace yar kazame kicemin bana gani daidai tace da akayi me fa yace da gaske duk wannan lomar bakinki kika sa ? Ta Daga kai yace kafci ai wannan yakai inyi loma Biyar dashi. Tya kiga miko mata cokali yayi sannan shima ya dauka.

Spoon din yasa ya Dino daidai cinsa wani Dan Nasan a baking cokali yakai bakinsa yace lesson number 2, haka kakeson ki dinga cin abinci tace kafci wannan kawai kace na mutu da yunwa Gaskiya saide in gwada maka wani Wanda yafi wannan daina gani ko yayi.
Yace gwada mu gani. Cokalin ta cika sannan yakai baki yace atleast gwara wannan.
Tace to kauna lesson 1 dazan koyama shine ka dinga cin abinci da yawa bude bakinka ta fadi hakan tana ciko cokali, yace ke wannan yamin yawa ai so like in mutu?tace Allah sai kaci Idan Ba haka Ba kuma in daina kulaka. Masa bude bakinka kamin in zaneka ta fadi hakan Kamar da Dan shekara Bihar take magana.

Yazeed badan yaso Ba haka ya bude bakinka ta dinga dura masa itama tanaci sanda suka cinye tas.
Yazeed ji take Kamar an kika sa a wurin saboda irin cikar da cikinsa tayi.

Yace Inda in kara cin wani abinci sai bayan kwana 3 ya fadi hakan yana Dan nishi.
Minal ko dariya tayi alamun kana ruwa sannan tace ai bata in kara maka labari tuwo miyan taushe zamuci anjima kallonta yayi Adan tsorace yace menene kuma wannan tace zaka ganshi.

Yace to kije ki ajiye mana wannan abun anjima sai musha tace Ba sunansa abun Ba sunanshi kunun aya yace to kunun aya.

Yace yauwa har na kusa in manta duk dare zamu dinga yin karatu dake zan koya mini karatu da rubutu kamin ki koma makaranta,ko bakyaso? Washe baki tayi tace inaso mana Nasan baba zaiji dadi sosai in yaji wannan labari kuma Nayi alkawarin in maida hankali into karatu babu wasa yace good girl give me five ta miko masa Hannu sannan suka tafa Suna masu fashewa da dariya.

Mikewa tayi yace don’t forget after each lesson sai kin min tausana fa karki dauka na manta ne and also Daga yau karki kara yin wani aiki kinji kawai ki dinga share part dina sai ki mana abinci. Murmushi tayi tace na gode sannan taje ta ajiye musu jug din kunun ayan fridge din falonsa,tunda tasha dazu da safe shiyasa bata wani damu dasha yanzuba.

Bayan ta dawo ta zauna yace toh ni zan Dan fita kinsan Jennifer ce tasa mana poison acikin cappuccino Dan haka dole in tuhumeta Inji Wanda ya sata.

Minal tace ikon Allah mutum mugun ice,Wanda ka yarda dashi shine zai sokeka a baya Allah ka rabamu ka kuma karemu Daga sharrin makiya. Yazeed yace Ameen sannan ya mike domin ya shirya koda ya shirya cikin khakinsa yayi mugun kyau ya fito a parlourn ya tadda ita tana kallon TV yace Toh yar kazame ni na wuce tace to sai ka dawo Allah ya bada sa’a.
Yace Ameen Ba rakiya ne?tace muje Toh in rakaka.

Har bakinka main kofa ta rakashi zata rude kofa yace baki jiba tace um? Yace Daga yau in zan fita zaki dinga min bye bye hug and peck kinji ?tace Nasan me hug din amma me kuma peck?
Pecking lips dinga yayi yace shine peck. Hannunsa ya ware ta rungumesa tanata Washe baki itakam yanzu babu abinda zatayi  sai godiya ga Allah Dan rayuwa ta ma ta dadi Alhamdulillah.

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Da fatan ka yi aikinka daidai Dan banason kuskure irin na wannan banziyar arniyar Jennifer, nasa boka cuku cuku ya kaita gidanne dab tayi min aiki amma saboda rashin kwakwalwarta gashi an kamata.

Ta dayan Abangaren wayan ne akace ma babu wata matsala Nayi Komai daidai yanzu haka nabar gidan
Tace good I will transfer your balance yace thank you ma.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button