KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

A takaice de taci bakar wahala kamin ta dawo gida tayi lubus aiko ta samu anyi cirko cirko ana nemanta. Tana shigowa yazeed da tsumagiyarsa a hannu ya daga kamar zai tsula mata tsurewa tayi ta turo baki tare da kneel down ta fara kuka.

Zama sukayi yazeed yace maza yi bayani, hannu tayi ta fara ABBA Dan Allah kayi hakuri ni wallahi naji jiki na hakura da haihuwar ma tunda naga kowa ba so yake na haihu ba….. tsaro musu labarin tayi tundaga sanda ta dawo ta tarar sahla na da ciki har zuwa yanzu. Hajiyar zuciya yazeed ya sauke yace ba haihuwa bane banason kiyi, munson ki Haifa mana jikoki mana. Irin maganar nan ce ba ayinta gatsau kinji? Kuma wa yace miki tsinto da akeyi ? Ni wannan maganar ba hurumin bace idan kin kara girma zaki fahimta. Bazance nayi nadamar aure dake ba amma gaskiya akwai kura dariyar da sallah ke rikewa ne ya kuce tace ABBA dama kaima ka iya cewa akwai kura? Murmushi yayi yace me zai hanashi kuwa? Ai nima sanda naje matashi sissi kwaro ne ni. Dariya kowa yayi banda zayya da ta tashi sumul sumul ta haura dakinta. Minal ne tayiwa sahir ido alamun ya bita yana haurawa ita da zaliha suka tafa. Yazeed da luku sukace Mata da gulma. Yazeed ne ya kalli mashkur yace tuzuru wai bazakayi aure bane har ka mutu? Shafa gemunshi yayi yace kwantar da hakalinka AI a asibitin nan na kyallo nafeesa kanwar bushra da alamu da ita za’ayi yazeed yace yafi maka.?

Jamal ne suka shigo shi da zakiyya sundawo daga koyar tafiya Dan yanzu ta ajiye karfen koyan tafiyan. Jamal yace me akeyi babu mu naga ana raha kamin a amsa mishi wayar yazeed tahau ringing. Mom ce ke kira ya dauka tace Dan albarka kuzo ku yanzunnan kaida daughter mun Kira iyayenta ma akwai magana.

A hanzarce suka shirya zasu fice minal har zata kwankwasawa su zayya yazeed ya hanata janyo hannunta yayi yana Mata wani irin murmushi me kashe jiki . Mannata yayi da kirjinsa tare da shinshina wuyarta. Kunnenta ya Dan ciza sannan ya rada Mata bakyason jika ne? A hankali tace ina..so har tana mamakin yadda muryarta ya sarke lokaci daya. Yazeed yace ana making mana baby shine zaki datsesu? Bige kirjinsa tayi tace kai baka tsufa da wannan abun ne? shekara hamsin fa kake dosa Yar dariya yayi yace ji yadda muryanki ta? sauya tsaban mayata amma ni ake cemin bana tsufa ?? Handsome dani irin haka? Yanzu dai zo muje daki sai mu gani ko na tsufa…. tace kiran mom din fa? Yace ba matsala zai iya jira kinsan fa ya kamata muyiwa twins dinmu gambo. Dukan kirjinsa tayi a wasa ya dangwali hancinta

Luku ne yayi gyaran murya yace malamai akan tsakiyar beni kuke kuma har a makantar min da yaro. Kallon kabir da zaliha tasawa hannu ta rufewa ido sukayi yayin da yake kyallo ido daya yana gulma. Ganin takura tayi masa yawa yasa yace mummy ni ki barni menene ban gani ba dukda cewa ke da dad kuna fada wani lokacin ina kallonku idan muna parlour sai inyi kamar ina bacci. Ina gani kukeyi K.I.S.S yayi spelling musu. Minal da yazeed ne suka wuce suna fadin this one pass our level yayinda luku ya kalli zaliha yace tabbas na miki godiya da kikasa mukayi masa dakinsa daban tun yana shekaru 3. Dariya yayi yace da anji kunya ko daddy? Shiru lulu yayi kamin yace my boy ka dena itin wannan maganan babu kyau kaji jai karami ne babu kyau kaji? Yace okay daddy.

Bayan su yazeed yaron yayi kamin luku yace dole mu kara kiyayewa da alamu yaronnan yanada wayo. Wani likitan laifin iyaye ke sawa yaransu su baci. Murmushi tayi taja kamatunsa tace for the first time(a karo na farko) ka fadi magana wacce nayi amanna da ita babu musu.

A dakin su zayya kuwa…….

KU BIYONI A CHAPTER NA GABA KUMA CHAPTER NA KARSHE DOMIN JIN YADDA ZAMU KARE WANNAN LABARI MAI FARIN JININ NAKU WATO KURUCIYAR MINAL.? SHIN ZAYYA ZATAYI CIKIN KO YAYA ? ME YASA MOM KE NEMAN SU YAZEED? Ko ciki ne da ita? Cabdi……..

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty ?

4th June, 2020.

?? KURUCIYAR MINAL??

? By miss Untichlobanty ?

? CHAPTER 98 (FINAL)?

RECAP
Bayan su yazeed yaron yabi kamin luku yace dole mu kara kiyayewa da alamu yaronnan yanada wayo. Wani lokutan laifin iyaye ke sawa yaransu su baci. Murmushi tayi taja kamatunsa tace for the first time(a karo na farko) ka fadi magana wacce nayi amanna da ita babu musu.

CONTINUATION

A dakin su zayya kuwa sahir yana shiga ya fincikota yace ke wai wace iriyar yarinya ce? Ke bakiga cewa kin girma bane bazakiyi kiyi da sahla ba? Kuka ta fashe dashi tana Jan majina tace toh Dan Allah ni menene laifi na Dan nace inason haihuwa? Ba duk Kaine da lefi banda sanda nace muku haihuwa nakeso amma kujera min fada kaki la taimaka min mu samu da sai kace ni ba matar ka bane.

Dafe kai yayi San yanzu ya gane cewa zayya yarinyace sosai. Dafe kai yayi tare da sauke ajiyan zuciya murmushi ya Mata a hankali ya riko hannunta yayi pecking zaro ido tayi kunya ya rufe ta. Shikam ma dariya ta bashi amma ya rike zaunar da ita yayi anakin gado yace haihuwa kikeso ko? Ta daga kai yace toh zo in baki yana me daurata a cinya.

Bakin laffayar ta taja ta rufe fuska wai ita jin kunya a hankali tace kunya kikeji ta daga kai kamar doluwa. Kamin tana shan hannu idonta a kasa tace ni idan zayya tana kallon film me irin sumba rude idona nakeyi saboda ba kyau. Lakutar hancinta yayi yace AI ba barsa take kalla ba film ne shiyasa ta fiki wayewa. Rufe idonki yanzuma, rufewa tayi kiri daga nan labari ya canja salonsa……

Su yazeed kuwa suna isa suka tarar da kowa an dallara su ake jira. Bude taro da addu’a akayi sannan Alhaji mansur ya fara magana

Ba komai bane ya tara mu anan wajen sai wani abin mamaki da ya riske mu lokaci daya Wanda zaiyi ma wasu dadi wasu kuma bazaiyi musu ba.

Wato alokacin da aka gwada mu domin bawa bushra bargo munyi mugun mamakin yadda akace babu Wanda nashi ya hau da nata hakan yasa likitan a sirrance yayi mana gwanin DNA yayinda ake gwada na sauran yan uwa dukda ko ba’a tsammace ya hau ba.

Ga mamakin mu sai tahau Dana matar ka ya fadi haka yana kallon yazeed. Shiru kowa yayi yaci gaba da cewa ba abin mamaki bane Dan hakan zai iya faruwa amma anfi tsammanin ya dace Dana yan uwanka na jini.

Lokacin sakamakon DNA ta fito amma likita baima nina mana yayi ba saida yayi na kowa inda ya tabbatar mana babu shakku cewa bushra ba yar mu bace yar malam Yusuf ne mahaifin minal. Zaro ido kowa yayi ana kimanin ya haka ta kasance.

Yaci gaba da cewa na gasta ne duba da kamanceceniya da sukeyi sosai idan ba ka lura ba sai ka kasa banbanta su. Wanda run a fari naji mamaki .

Yanzu Abu daya nake son tabbatarwa kallon minal yayi yace shekarunki nawa tace 36 jinjina kai yayi yace rana da wata fa tace 2nd September.? Yace tabbas wannan ranan aka haifi bushra. Babu shakku ku yan biyu ne kuma yadda akayi kuka rabu Allah shine masanin.? Fatan mu Allah ya hada kanku.

Baban kowa ne yayi godiya bayan sallama yace toh tunda ta tabbata yata ce amma ku kuka rikota ni bazan harbeta ba na bar muku Abu daya de za’ayi dole abi ka’idar manzon Allah ta canja sunan mahaifi amma nikam na bar muku ita tunda har tayi aure ma ba anfanin na karba.

Godiya Alhaji mansur yayi daga nan aka dan jajanta mutuwar safina kamin kowa ya warware. Inna da tsufa ya fara kamata Dan ta dara shekaru? hamsin da biyar tace tace ina kishiyar tawa ne akace hajiya zayya AI gida muka barota tana wani aiki. Tace Allah yasa na arziki ne ba shirme ba. Kallon kallo sukayi sukace ameen.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button