KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

🌹by miss untichlobanty🌹

CHAPTER 55

Yazeed jin Kamar ana Jan gemunsa yasa yadan bude ido ya kafawa minal wacce Keta jajjan sajen nasa Dan batama lura da Cewa ya bude idonsa Ba.

Hannunsa yasa ya riko hannunta da take ja masa gemu yace kazame yau kuma da gemuna za’ayi wasa? murmushi tayi tana kifa fuskanta a faffadan kirjinsa mai dumi da sanyin kamshi.

Murmushi yayi mai Sauti yace humm ! Yar kazame taga handsome. Dago da fuskanta tayi tana mai kicin da ido tace Allah yazzy baby Idan ka Kara cemin kazame zanyi fada dakai.

Rife ido yayi yace oooo not this name again please ki daina cemin yazzy baby Wai bazaki manta bane?tace har abada kuwa. Yace haba kazame na please ki dena cemin Yazzy baby tace saide Idan zaka daina cemin kazame yace to me kikeso in dinga ce miki?kinaso in dinga ce miki beauty?kindy? Sweet? Cup cake?cutie pie? Bl……….

Datseshi tayi tace ni banaso kawai ka dinga kirana da abinda kake kiran….. Um….. Ka gane ai ta fada tana kara sa dayan hannunta dake free Wanda bai rike Ba.

Yace ah ah ni ban ganeba,tace yadda kake kiran aunty uwar gida. Dan zaro ido yayi yace kina nufin zakiyya?Daga kai tayi yaja hancin ta yace na ganoki wato kishi kikeyi.

Bata rai tayi tace ni Ba kishi nake Ba yace haba my baby Nasan fa kishina kikeyi turo baki tayi tace ni Ba kishi nakeyi Ba. Yace Toh me yasa bakya kishina ? Tace saboda me yasa zanyi kishin ka?

Yazeed’s POV

Shiru Nayi jin tambayan data aiko min don bansan yanda zan amsa mata Ba.
Bansan lokacin da bakina yace saboda kinaso.
Murmushi taci gaba dayi da alamu bata dauki abinda na fada da muhimmanci Ba. Girgiza kanta tayi sannan tace ni bana sonka kawai kai aboki nane.

Sanda zuciyata tayi tsalle dukda Cewa nuna ban tabbatar da Cewa songs nake Ba amma da tace bata sona take zuciyana ta fara suya. Da alamu ta lura da yanayin Dana Shiga domin atake naga damuwa dauke a fuskanta saide abinda ya bani mamaki sakan gemuna da tayi saijin lallausan hannunta nayi akan kumatuna tana goge wani Abu mai ruwa. Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un kuka nakeyi.

Minal’s POV

Ni ban dauki abinda yake fada da muhimmanci Ba Dan gani nake wasa yakemin. Ya za’a yi mutum Kamar ya yazeed ga kudi, ga kyau, ga Suna,ga daukaka yace Wai sonshi nake?
A Gaskiya na kamu da dinshi Ba tare Dana Shirya Ba domin bansani ina sonsa Ba,sai ranan Dana sameshi da zakiyya a parlour Suna hadiye fuskan kuna ji Nayi Kamar na mutu boyewa kawai Nayi.

Ganin yana jiran na bashi amsa yasa na girgiza kaina cikin shiririta na nace bana Sonka kawai kai aboki nane. Mamaki tare da tashin hankaline suka kamani ganin hawaye na saukowa Daga idanunsa bansan sanda nasa hannuna na goge masa ba. Me yake shirin faruwa ? Me hakan ke nufi? Me yasa yake kuka Dan nace bana sonshi? Yana sonane?

MY POV

Yazeed ne ya rasa yanda zaiyi Wai kuka yakeyi?kardai dagaske Sonta yakeyi to amma yaushe ya fara sonta? Ganin shirun yayi yawa yasa ya hade bakinsu Ba tareda yayi Komai Ba abinda ya basa mamaki shine mayar masa da tayi Dan haka baisan lokacin daya kara zafafa lamarin Ba. Sanda yaji zasu mutu saboda rashin numfashi ya sake mata baki.

A Dan kunyace ta tashi ta fice Ba tareda suncewa juna komai Ba.
Dunkule Hannu yazeed yayi sannan ya naushi iska. He ruined everything! What if da haske take bata sonshi?yayi gaggawa wajen nuna mata abinda ke ransa even though it was not intentional. Shima bai Shirya ba, yanzu ya zaiyi ya gyara abinda ya bata.

🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹

Zaliha kam though time take bawa Yan Maiduguri Dan Cewa tayi dole a miyar da ita Kaduna. Duk masifar inna sanda ta hakura ta bada gari.
Nan aka lallaba zaliha akace tayi hakuri gobe gobe zasu dawo Kaduna amma sai ta yarda tasha tsuminta.

🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹

Ya Abubakar yana shigowa Laila ta danno da gudu ta rungumesa. Shidai baisan me ya faru ba amma ganin yadda take farin ciki kuma ta wartsake yasa yasan Cewa alkhairi ne ya faru.

Janyota yayi har suka zauna yana dariya yace aunty fadamin abinda yasa Laila na irin wannan farin ciki.

Dariyan manya aunty fauziyya tayi kamin tace kafin wannan yanzu dai ka saketa tunda ba’a daura auren ba sai a lokacin ya lura da yadda suka kankame juna cikin jin kunya Laila ta gudu ciki yayinda ya cire hula yana sosa keya.

Aunty fauziyya tace ja’irin yaro ina ganinka Kamar salihi murmushin borin kunya yafi yace ba haka bane aunty.
Tace to Nide albishirinka yace goro kuma fari kamin ma ki tambaya.
Dariya tayi tace todai in fada maka babu abinda ya Shiga tsakanin Laila da Dan iskan yaronnan.
Nan ta fada masa yadda ta gano da yadda suakyi da likita.
Godiya ya dinga yiwa Allah harda sujjada baisan sanda hawaye ya zubo masa ba. Zaunar dashi tayi akan kujera sannan ta Dafa kafadan sa tace ba kuka zakayi ba hamdalan da kayi shine dai-dai addu’a zaka cigaba dayi allah ya kareku Daga sharrin makiya yace ameen.

Kicewa lailan ta samoni a mota zamuje gidansu yazeed tace Toh sannan ta Shiga ciki.
Fita yayi ya kirawo almajirai. Nan ya dinga daba musu kudi sanda ya raba sama da 10k.

Laila da ta fito sai murmushi take har tayi wani Dan kyau hakannan. Kai kwanciyar hankali dadi gareshi.
Gaba ta Shiga ta kwame ya Abubakar ma ya Shiga driver’s sit. Belt yasa sannan ya kunna motan hannunta ya kamo ya sumbata ta warce tana turo baki yace ya akayine gimbiyata? Tace ba’afa daura auren ba kake rikeni yace astagfirullah wallahi duk cikin dadin ne ni na manta ma Allah ya yafemin tace Ameen.

Motar su suka fita Suna masu jin dadi sai gidan oga yazeed.

🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹

Abangaren su yazeed kuwa minal cikin yar iskar rigannan ta nufi kitchen kuma bilhakki da Gaskiya yunwa takeji Dan 10am ma ya wuce ko time din canja Riga batada shi.
Hamdala tayiwa Allah Dayasa akwai sauran Mara 3 a tuwonsu na jiya Dan da babu da idomie zata dafa.
Aiko nan ta daura dumame ziciyarta na wurin yazeed da yanayinda ta barshi yayinda takejinsa a jikinta.
Yazeed ko shiru yayi kawai Dan bai Masan me ya dace yayi a halin yanzu ba kawai sai ya mike ya fada wanka bai wani bata lokaci ba ya fito dai dai lokacin wayarsa ta dauki ruri dubawa yayi yaga mom ne hakan yasashi yin murmushi Dan yayi kewarta Rabon dayaji muryanta tun sanda tayi masa fada.

Dauka yayi tare da fadin my sweetheart kaif asbahati? Murmushi tayi Dan itama tayi kewan Dan nata tace lallai Abu yayi dadi tunda har ka fara manta lokaci nida nake India ne yanzu safiyata? Yace sorry sweetheart kinsan Nayi missing dinki fah.
Murmushi tayi tace abinda yasa na kiraka kenan Dan gobe ina tafe. Murmushi yayi amma saboda shekiyanci irin na yazeed yace noo!sweetheart karki dawo zaki batamin honeymoon dina.

Kama ha’ba tayi Kamar yana kallonta tace dannan kace Abun naka ya girmama ! Lokacin Dana aurama ba iskanci zaka min ba? Ta fadi hakan sounding like a drama old lady.

Dariya yazeed yayi yace Allah ya kawomin ke lafiya my sweetheart kinsan fa you are my first and last love. Mom tace first dindai amma last din kam….

Yace tunda kince haka to hakan ne. Kinji abinda ya faru da zakiyya kuwa?tace me ya faru? Yace ai………….
Nan yazeed ya kwararo mata bayani tace subhanallahi Allah ya Kare na gaba toh, yasa kuma haka shine mafi alkhairi yace Ameen. Muryan Jamal ya jiyo yana Cewa my man zan biyo mom fa Dan wallahi inaso inzo in kalli love show kyauta Ba tare da na yanki ticket ba. Mom ne ta make keyarsa yace ouch da zafi fa. Mom tace araftu(na sani).

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button