KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Tace mai zubin samudawa da ido kulya kawa sannan ta Diba aguj

Bata tsaya a ko Ina ba sai gidan aunty fauziyya zata fada a guje taji gate a kulle ga wani mota shigen na yazeed ya shigo Latin take fitsari ya cika mata Mara take gumi ya fara karyo mata.

Bubbuga gara din ta farayi aiko zaliha na bude mata ta nufi ban daki tana mai cillo da takalmanta.
Bayan ta fito aunty fauziyya tace ina kika tsaya tun dazu muMun dauka kin Koma gidane ma kuma ya akayi kika bari fitsari ya matseki?

Labarta musu abinda ya faru tayi aiko sukayita dariya zaliha tace ai in kinsan wata bakisan wata Ba 😂

Nandai zaliha ke fadamata irin haushin data bata har ta tafi ta barta

Nan aka dago da zancen auren zaliha har minal take basu labarin baba nason ya mata aure amma yace sai mai Dan ilimi

Minal tace nidai indai gidan da abinci Toh shikenan banida damuwa kai amma fa banda mai warin hammata.

Aunty fauziyya tace har kura zatace da kare maye ?
Keda bakyayin minti uku kingama wanka? Harvwani bakison mai wari?

Zaliha tace ai ta gyara yau bakiga har kwalliya na mata Ba

aunty Fa’iza tace dallah dubi wani gira Kamar Anyi bakin fenti dukkanku Ba abinda kuka iya

Haka dai suka dinga hira suna kwasar dariya Kamar Ba gobe

Minal shaf ta manta dacewa Ba kwana zatayi Ba

Aunty fauziyya kuwa ganin a holiday suke kuma taga minal da katan jaka sai ta dauka kayanta ne aciki

Zaliha kuwa dama sati zatayi mata

Aunty fauziyya Ba laifi mijinta yanada rufin asiri mijinta Dan kasuwa yanada shago akasuwa
Itakuwa tana gyaran jiki,dasu makeup,da turaren wuta Wanda inna ce ta koya mata makeup kuwa
Training class tayi
Kuma Ba laifi tana samun alheri.

Da daddare suka dafa Dan malele

ï¿?

suna cikin sha

Minal tace Innalillahi wa inna ilaihi raji’un

Aunty da zaliha sukace menene?

minal ta side manjan dake bin mata hannunta kamintace na manta baba yace karnayi dare

Atare sukace dama Ba kwana zakiyi Ba ?

tace eh

Aunty fauzy ta kalli agogo pass 9 tace dare kuma yayi Tara ya wuce
Wayar baba tanananko?

Minal tace eh

Aunty fauxy tace yauwa bara na kirasa na fada masa

Nan ta kira baba tace minal zata kwana a wajenta

Yace to Ba Komai daganan ma ta kara mata fada akan tsafta Dan yau yaji dadin yanda ya ganta tace Ba Komai Insha Allah zata musu fada dukkansu biyu ma

Nan sukayi sallama

Anan suka tattara suka kwanta dama mijin aunty fauziyyan bayanan.

Yazeed’s POV

Yazeed kuwa koda minal ta falfala a guje tsaki yayi yace idan na kama yarinyannan sai Nayi mugun saba mata sai ta gwammaci ba’a haifeta ba

Komawa mota yayi zakiyya nata dariya tace swthrt kaga bakinta kuwa itafa gani take ta kure kwalliya

Yazeed yace gaba zakky ke wato duk rashin kunyar da tamun Ba dameki bako? Tace wannan tsakaninku ne ai

Dear pls let’s go !

Yace my zakky you will never change

Sannan ya kunna mota suka tafi yanata gungunin abinda minal tamai zakiyya sai dariya take Kamar tababbiya

Abin mamaki take basa zakky wace iriyar mutum ce?kawai yayi smiling.

At night

After sun dawo daga dinner dinsu
Suna hira a parlour mom tana fada masa Cewa she is planning on visiting her family

Wayan YAZEED yayi ringing it was his aboki,a brother as well Jamal

Jamal yace Hello captain.

Yazeed yace Dude how far?

Jamal:guy I have a surprise for you?
Yazeed: and what’s that?
Jamal:gobe zan shigo garinku
Yazeed: are you serious?
Jamal: of course yes!
Yazeed:okay I will send habu(personal)driver to pick you up
Jamal: guy pls kazo da kanka
Yazeed: no need to plead with me I will come,by what time would u land?
Jamal:that’s why I like you,emm we will land by 12:30pm Insha Allah
Yazeed: okay see yah
Jamal: bye
Yazeed: bye…………

Hope you love this chapter?

Juma’at Mubarak

7 June,2019

Mzz untichlobanty💕
[1/11, 1:40 AM] Mzz_Untichlobanty💞:

🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by miss untichlobanty🌹

🍀CHAPTER 10🍀

Morning

Koda su minal suka tashi akayiwa yara wanka

sukayi  karyawa suka ci Suma sukayi wanka suka danyi hira

Anan  aunty fauziyya tayiwa minal fada sosai akan tsafta sannan ta bata wasu yan turare tace tanayin aiki dasu
ta bata wasu sako ma ta kaiwa inna(nima bansani me acikiba)
Waje ta fice domin nemo almajiri ya kai mata gyaran takalmi aiko taci karo da kandala mai gyada wanka mata mari tayi tace ke kandala da ubnki me kikazo yi nan unguwar iye? Kuka kandalar ta fara tana kokarin kwashe gyadatta daya bare tace wallahi saina hadaki da aunty salma minal tace inkin fasa kinki Allah ita kanta salmar tayi kadan balle ke banzar bazara kunun bayan ludayi. Dama itama Daga haka ta fara Daga talla ta fara bin maza unguwa unguwa yanzu ta zama magajiya adai juri zuwa rafi. Bankadeta minal tayi tace shgiya jaka.

Gyaro mata takalmin akayi sannan ta kama hanyan  gida domin Azahar ya kusa pass 11:00am………..

Yazeed’s POV

Yana tashi da safe after yayi all necessary things needed ya gaida mom sannan yadan fita.  motanshi fara tare da guards 2 kamin 12:00pm yayi ya dauko Jamal .

After yaje wani cafe yanashan favorite cappuccino dinshi phone dinshi yayi ringing.

Zakiyya:swthrt awhile naga fita ko?pls if you don’t mind kabiya restaurant da mukaje jiya ka siyo mana pizzan naga akwai a menu dinsu kaga sai ka daina siyowa a dayan wajen kasan yaufa Thursday

She said all of that in not more than 2 breath

Yazeed: haba dear!can’t you atleast say good morning, u didn’t ask about my well being or anything all you care about is the pizza which we will eat later at night ?

Zakiyya: sorry good morning
Hope zaka siyo pizzan ?

Yazeed: naji

Zakiyya: and also kafin ku dawo kudan biya ta boutique dina Ku karbo min wani sako( legendaries), bye love you tiiit

Yazeed:love yo…..

Oh god,bukatanta ya biya she can’t even wait for me to say bye

He called the waiter,paid for  cappuccino dinshi

And went out security men dinshi guda biyu na biye dashi

Kofa suka bude mai ya Shiga motan sannan suka rufe daya ya Shiga drivers seat dayan kuma front passenger seat

Na driver’s seat ne ya kunna motan ya kama hanyan airport

yazeed yace we are going to zakby unique boutique  before going to the airport

Drivern ya karya kwana sukayi hanyan boutique

Minal POV
Tana cikin tafiyarta tana er wakenta akan babban titi wasu en shaye shaye suka hangota

Thug 1:boss kaga wata er shila kuwa
Thug 2:kunama yarinyannan tayi
Thug 3:boss kawai mu sankacota mana
Thug 4:boss nifa inason sidin kwano
Thug 2:goje(thug1) Ku kai min ita
Mansion amma kuyi ahankali Dan yarinyar ta Shiga raina
Thug 1:lallai yarinyannan ta Shiga ranka boss tunda har sai an kaita mansion baza’ayi Anan Ba
Boss:banason maganan banza ni har kishinta ma fa ya kama ni
(Kaji min rashin kunya irin na Dan tasha Wai kishinta ya kamashi ni yama bani haushi)
All thugs:hahahahaha boss kenan mude in an gama a aiko mana
Boss:zundum me kuke jirane Ku dauko min amaryata

Minal tana tafiya taga en shaye shaye sunyo kanta fuska tayi taci gaba da tafiya

Goje ne yace amaryar mu ji mana
Bata kulasu Ba amma tana fake dasu

Scorpion ne yayiwa Goje alama da ido akan su kamata basu ankare Ashe Amaryar su ta Dade da arar kafar kare acan nesa suka hangota ta auna a guje suma da gudu suka bita

Gudu take batasan inda take wulla kafarta ba wulan keluwa (kwana)tasha inda ta hango booth din wani mota a bude da gudu ta daga kayan ciki ta Shiga kasan kayan yazeed yaji  jijjigar motan kuma baiga fitowan su ezikel Ba a karo na biyu hakan yasa ya leko

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button