KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Fitowa sukayi a motan akabar Abubakar da laila daidai lokacin minal ta fito yazeed na kallonta ya saki murmushi.
Dan dunguransa lukman yayi yace my man kaima na….

ya Abubakar na kallon duk abinda ke faruwa Dan haka shima murmushi yake amma ba bakin tsokana.

Cikin gida ko zaliha ido ta rufe tace wallahi sai ta bisu. Aka buga aka raya tace Sam haka aka hakura akayi yarjejeniya da ita Cewa in aka barta toh Idan ta dawo zataci abinci.

Laila ko tana hango minal Yan hanjin cikinta suka kada domin ko bazata manta sanda suka tana haduwa sau daya ba sanda ta biyo ya Abubakar itada Sulaiman, minal ta dawo Daga islamiya ta mata duka Wai Dan tasha ruwa da kofinta. Shekaru 6 dasuka wuce.

Gaishesu tayi kamin su masa Shiga zaliha Kamar an jefota da takalmi a hannu.

Minal ne  ta zaro ido Adan tsorace tace zaliha me kikeyi awake?
Lukman ne yakalleta sannan ya kalli yazeed domin a tabbatar masa.
Kai yazeed ya gyada masa alamun itace matar tasa take yaji zuciyarsa yayi masa nauyi domin kuwa bayada interest a bakar Mace shiyasa ma yakeson ayush abinda bai sani ba shine ayush bleaching tayi.

Kara analysing dinta yake yazeed shima ya dunguresa Kamar yadda yamai dazu sannan kasa kasa yace inyi magana ko inyi shiru? Still idon lukman na kan zaliha yace yanzu fito kayi?

Ya Abubakar yace Inlaw barshi ba yanzu zamuyi magana ba sai nan gaba.

Zaliha ko binsu kawai take da ido,yazeed yace kai dallah kamo matarka kasata a mota mu wuce. Ya danyi hesitating kamin ya taka izuwa wajenta ya kamo hannunta. Wani yar yaji amma ya basar zaliha kam da hankalinta baya wajen batamasan an riketa ba ta janye hannunsa taje ta shige motar kamin tace Wai me kuke jirane? Yadda tayi magana Zaka rantse uwar su ce babu Wanda ya mata magana illa shigewar da sukayi.

Lukman ke tuka motar yayinda yazeed ke gefensa sai a abaya kuma minal tana owner’s corner sai zaliha a gefenta sai laila a tsakiya sai ya Abubakar a karshe.

What do u think of laila? Kuna sonta?

Next chapter is a boom💥.

Takuce karamarsu babbarsu

Miss untichlobanty💕

23 November, 2019.
[1/11, 2:28 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by @mzz_untichlobanty@nt🌹

CHAPTER 44

Yazeed ne yasa Hannu ya gyara mirror yadda zai iya hango minal abinda bai sani Ba kuwa shine lukman ke Satan kallon zaliha ta mirror din Dan haka shima ya hararesa bayan Yan sakanni yasa Hannu shima ya
Juya dauke kai yazeed yayi kamin shima yasa Hannu ya kara juyawa.

Duk abinda ke faruwa ya Abubakar bai lura domin duk hankalinsa ya ta’allaka a yadda yaje zaune kusada laila Dan haka ya kafeta da ido yayinda take wasa da Yan yatsunta ganin yadda ya kafeta da ido bazata iya kallonsa ba.

Minal kuwa window kawai take kallo tana tunanin rayuwa yayinda zally tayi zugum da alamu ta tafi birnin China.

Yazeed da lukman a tare suka kai hannunsa zasu juya madubin kallon juna sukayi yazeed ya harareshi shikuma ya sakar masa murmushi.

Lukman ne ya kalli cikin mirror din Anan ya hango abinda ke wakana a duniyar su Abubakar.

Nuni yayiwa yazeed daidai lokacin suka iso leka mudubin yazeed yayi suka fashe da dariya.

Zabura yayi yace har Muna ido ne ? Lukman yace bamu ido Ba Muna hanya tukunnan suka kuma fashewa da dariya su minal Kam da basu gane meke faruwa ba suka tsaya kallonsu.

Fice wa sukayi suka Shiga asibitin. Wata nurse suka tambaya Inda aka ajiye Ummi din ta nuna musu tare da cewa su Shiga bibbiyu saboda ba’ason hayaniya nan dai suka fara Shiga.

A take laila ta fashe da kuka dakyar dai aka lallabata kamin min sukayi hanyar gida.

Mayar da zaliha gida sukayi,laila kuma aka kaita gidan Kanwar mamanta.
Ya Abubakar Kamar zai mayar da ita ciki. Sai bayan isha’i suka Koma gida, yazeed yayi sallama da lukman tare da Cewa akwai abinda zasu tattauna goben lukman yace ai baki daya kakeson yin magana Ba nima akwai maganar da zanyi dakai.

Shigowa ciki sukayi kamin yacewa minal tayi wanka ta Shirya ta sauko taci abinci Toh tace sannan ta sauko.

Gyada kai tayi sai ta tuna bayason gestures sai tace Toh sannan ta haura sama.

Wanka shima ya Shiga yayi sannan ya saka kayan baccinsa ya sauko yana Cewa yunwa nakeji amma hanji na ya daure maybe I should take some cappuccino.

Sofa ya samu ya zauna kamin ya janyo wayansa ya fara scrolling messages.
Minal ce ta sauko cikin wani farin rigan bacci na satin amma Ba shara shara bane saide yana like mata a jiki once in a while.

Kallonta yake tayi har ta ido gabanshi bai ankare ba tace gaji still kallonta yake.
Hannunta tasa ta tafa a gaban fuskansa tace nace maka gani.

Hannunta ya kamo ya janyota ta fado jikinsa kokarin tashi ta fara yi ya kankameta sannan ya Daga mata gira daya yace sannu da zuwa.
Kiciniya ta farayi tana Cewa ni Dan Allah ka sakeni Wai na maka kama da yar iska ne? Murmushi yayi yace Kayan jikinki ya amsa mini wannan,sannan tunda gaki kwance ajikina ai kinzama yar iskan ko turo baki tayi ta fashe da kuka ni wallahi ba yar iska bace yace time will tell. Itadai bata kulasa ba banda ci gaba da magana da tayi tace to ai kaika janyoni kuma ka wani rikeni sai kace zaka mayar ni ciki yace to wa ya sani ko cikin zan mayar dake.

Ganin babu sarki sai Allah yasa yasa ta kwanta luf ajikinsa babu abinda ke tashi a parlourn sai sautin numfashinsu kasa kasa minal taji yace “sai Anyi magana mutum yace shi ba Dan iska bane.
Tace me kace yace tunani nake. Harararsa tayi sannan ta kuma kwanciya can sai yace Wai meyasa bakison kirana da suna nane ? Saide kawai ki fadi magana,Ko kuma kicemin oga sir. Ko bakisan sunana bane ?

Girgiza kanta tayi a kirjinsa tace na sani mana ba kaima baka kirana da sunana ba saide ka dinga cemin insaram yace to mene sunan nawa?Dago da kanta tayi tana washe ha’kwara ita a dole kunya tace kawo kunnanka kaji.
Matso da kunnansa yayi a hankali kuma a kunyace tace oga ya..zeed.

Sanda tsikar jikinsa suka tashi domi. Tunda yake bai tabaji sunansa yayi masa dadi Kamar yadda yayi a bakinta ba.
Dan haka yace me ki kace ?ma’ke kafada tayi alamun bazata fada ba.
Puppy face yayi Yace please my insaram! Turo baki tayi tace ba gashinan ba kana sake cemin insaram yace to na daina Idan kika fadamin sunana to zan chanja miki suna.
Hannu tasa ta rufe fuskanta sannan tace oga yazeed
Yace to ki cire ogan tace yallabai zansa ?yace a ah tace to yaya kakeso Insa maka yace ah ah kawai ki kirani da suna na.

Tace a ah ba tarbiyya bace in kiraka da sunanka ko ba Komai ka girmeni.
Murmushi yayi yace beauty is secretly trying to be romantic da muryar tsokana. Turo baki tayi cikin shagwaba da wasa tace wallahi ya yazeed da gangan kake min turanci Dan kasan ban iya ba yace sorry Toh na daina karki damu kema zan koya mini turanci. kinaso ki Koma makaranta gyada kai tayi yace good zannayi miki lesson a gida inyaso sai Kiyi jamb da WAEC ko ? Tace eh yace beauty tace Waye beauty kuma yace Kece mana Sabon sunanki kenan. Ya miki? Ta gyada kai tare da Cewa eh yace kinsman ma’anarsa tace yana nufin kyau ba? Smiling yazeed yayi sannan shima ya gyada mata kai yadda take mai sannan yana kumatunta yace Ashe de beautyn tawa ba laifi.

Shiru wajen ya sake dauka kamin yazeed ya sake Cewa beauty ta dago ta kalleshi yace inason ki saki jikinki in Muna tare kinji? Ta gara kai yace kinaso ki zama kawata ? Ta sake gyada kai turo baki yayi yadda take mai inya mata abinda bataso yace bazakimin magana ba? Tace inaso in zama kawar taka. Tasar da ita yayi ta daina shima ya gyada zamansa Daga kishingida sannan ya miko mata Hannu yace friends? Shaking hannunsa tayi yace bakice friends dinba tace friends sai suka kyalkyale da dariya.
Daidai lokacin cikinsa yayi masa karar yunwa abinda bai tana faruwa dashiba ko a mission kuwa.
Pouting yayi yace beauty yunwa nakeji tace muje kaci abincinka to yace nope cappuccino zansha tace cup…po  mene? Yace cappuccino kin gaba sha ? Girgiza kai ya harareta tace a ah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button