KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

??

Safina! Safina!! Safina karki fita a gidannan nace ko. Wacce aka Kira da safina ne ta ja tsaki tare da kada kai tayi ficewar ta.
Motar kawarta dake jiranta a bakin kofa tayi shigewarta tare da cewa babe yau? Sheraton zamu je. Kawarta me suna rafisa tace kamar kinsan zuciya ta Dan naji ance this week akwai guests sosai. Figar Motan sukayi bayan sun sake kida kamar a club.

Suna cikin tafiya rafisa ke cewa gaskiya babe mum dinki bata kyauta miki ace big girl kamarki bazata iya using mota ba? Haba this is not right. Tsaki safina taja tace kede bari ai wata rana saina gaurawa wannan matar Mari.

Reception suka Shiga lokacin da suka iso hotel din nan suka tambaya kuma aka sanar dasu cewa yau akwai baki sannan ma ana party.
Nan suka tafa tare da biyan kudin daki saboda kar a hanasu shiga.
Daki Dali suka fara bi suna kafa kunne idan sunji alamun namiji ne kadai a dakin sai suyi knocking idan an bude sai sugani, idan Dan hannu ne shi da kansa zai musu tayi idan ko ba Dan hannu bane sai su basa hakuri suce batan kai sukayi.

Saide fa yau da matsala Dan basu samu customer ba gashi anfara complain cewa wasu Mata na damun baki.
Shawara suka Yanke idan suka duba room dinnan ba customer toh zasu nufi wajen party ne.
Knocking sukayi ba’a bude ba har suna shirin wucewa sukaji alamun motsi hakan yasa suka gyara tsayuwa tare da sake budo wasu bangare na jikinsu. Ana budewa suka saki murmushi amma me zasu gani ayush ce ta bude kofar. Wani kallo take binsu dashi da yake itama safina tanaji da kanta harara ta mayar Mata. Aiko babu bata lokaci ayush taci kwalarta tare da wulla ta chiki daki. Sauri rafisa tayi itama ta fada tana kokarin ceto kawarta yayinda itama safina ta ci kwalar ayush nan fa dambe ya kaure tsakaninsu suna zagin juna uwa da uba.
? Ganin abin yaki karewa yasa goje shiga tsakani tare da fadin wai sweetheart me ya hadaku fada ne tsawa ta daka mishi tare da cewa banza munafuki wato abinda? kakeyi a bayan idona kenan ko? Wato kanada wasu yan? Mata ko? Safina tace ke munyi miki kama da kananun karuwai irinki ne? Wani kallo ayush ta Mata kamin yace ke shegiya ki iya bakinki wannan din miji nane. Kai kuma…. ta juyo tare da sake kallon goje saide kamin taci gaba yayi saurin cewa haba wifey hotel dinnan fa ke kika kama kuma nasan zakizo toh meyasa zan kirawo yan Mata? Sannan da banida gaskiya bazan bari ki bude kofa ba saide ni in bude ince musu su jirani ko wani Abu. Tace ehhh kuma fa hakane amma ya akayi cikin duk dakunan hotel dinnan sukazo dakinnan? Yace tayaya zanyi na sani? Kallon Safinan tayi tare da cewa karamar ka….. safina ce tayi saurin cewa wallahi kina karashe wa saina tsinka miki Mari. Karuwa tana bin maza ne dan kudi Niko ina binsu ne Dan biyan bukatata. Ni safina Usman nadabo nafi karfin kudi wallahi.

Ayush tace what ke yar gidan Alhaji Usman nadabo ne? Safina tace kwarai kuwa. Murmushi mai sauti ayush ta fara tare da fadin yar uwa ai bakiyi bayani bane da wuri, toh amma me yasa kika zabi wannan harka bayan dukiyan da babanki yakeda shi? Tabe baki safina tayi tace wannan harka ta ce babu ruwanki.? Ayush tace hmm malama safina kenan ai yanzu? batun rigima ta kare a tsakanimu ai mun zama yan uwa dariya rafisa dake kefe tayi tace kai jama’a duniya juyi juyi anayi inajin dadi kamar ba yanzu kuka gama fada ba. Ayush tace kinga babu ruwanki ehe, kawai kina nema ki shiga tsakanin yan uwa.

Safina tace malama ya da sauri haka yaushe na zama yar uwar ki? Ayush tace kede bar wannan sanar dani ansar tambayan ki. Tabe baki tayi tace saboda kawai in biya bukatata. Ayush tace toh kiyi aure mana. Safina tace lokacin da nakeson ayimin AI ba’ayi ba yanzu ko ban bukata Dan na Saba da maza dayawa guda daya bazai isheni ba.

Dan tunani ayush ta shiga yanda zata rike safina Dan idonta akan kudin mahaifinta ne. Aikuwa sai ta tuno lokacin da zakiyya ke raki akan jarabar yazeed hakan yasa tayi saurin cewa idan kuma na samo miki Wanda yakeda komai har wannan fa? Safina tace ai babu bata lokaci zan bar bin maza.
Ayush tace rest your case hajiya ta kin samu bani numbarki kawai. Sharing number dinsu sukayi suna ta jin dadi kowa bukatarsa zai biya sannan suja rabu.

Koda safina ta koma gida carko carko ta Sami iyayenta. Baban ta na ganinta ya daka Mata tsawa ke me sunan mama daga ina kike? Nace cabdi,wannan shine ihu bayan hari. Turo baki tayi tace daddy wai kaima irin momy zaka zama ne? Yace shashashan yarinya ayimin shiru. Wallahi idan baki fito da miji nanda 3 months ba babu ni babu ke. Bubbuga kafa ta fara tare ta haye sama tana fadin lokacin da nace ayimin cewa akayi banida kunya yanzu kuma za’a dameni. Mum dinta ne tace idan kika bari na sameki wallahi zan ballaki.

Kallon Alhajin tayi tace Alhaji kaga abinda nake fada ko lokacin da kake bata ta, tazo tace tanason aure kace Sam sai tayi karatu saboda tayi taking over business dinka. Toh gashi yanzu ita auren ma baya gabanta.

Zama yayi tare da sauke ajiyan zuciya yace hajiya ki yafemin na lalata rayuwar diyar mu guda daya tak. Maganin hawan jininsa ta Nemo masa duba da yanayin sa tasan zai bukace su.

Minal kuwa tana bude idonta tace idan baka da hankali tabani kaga ikon Allah.
Ummu ce tace ke amina tu magana kikayi koko kunne nane sai alokacin itama minal tayi magana hakan yasa ta rungume ummu tanajin dadi.

Ummu tace aminatu yaya sunanki na asali? Minal tace amina ne kuma banda sunana babu abinda nake tunawa. Ummu tace kenan bakisan me cikin jikinki ba? Ta daga kai. Ajiyan zuciya ummu ta sauke tace ina kyautata miki zaton mutumiyar kirki amma da alamu kinada zafi. Nikam zan ajiye ki idan har kika haihu ba’a nemeki ba toh zan aurar dake, kinaso? Minal tace ni banason a rabani da ummu na. Ummu tace karki damu ko gidannan bazaki bari ba.

Fita tayi tare da karbar tuyanta a hannun sabi tana fadin shege ja iya abin arziki amma bakayi da tuyar kakemin kana samun albarka befi maka ba? Tashi yayi yana fadin ko ki karbi wannan abun ko na barar da komai. Kuma na dauki naira dari biyu tace nide karka sake kayimin shaye shaye da kudi na. Yace ke kika jiyo tare da bazata cikin gari.

??

Safwan ne da sahir suka shigo dakin yazeed da gudu suna fadin daddyn mu ya jikinka? Murmushi yayi tare da rungume su lokaci daya suka kwanta mai hakan yasa babu shakku ya yarda cewa yaransa ne.

Ayush ne ta shigo tana fadin kai kuyi ahankali kunsan daddyn ku bashida lafiya.
Dariya sukayi sukace daddy kaji aunty ayush ko? Wai muna damunka ? dariya yayi tare da cewa yaushe yara na zasu dameni?

Ayush ne tace brother akwai abin da nakeson in fada maka. Gyara zama yayi yace kaga dai yanzu 7 years kenan da rasuwar mummy sufwan ya kamata ka kara aure ko Dan su. Jin Jina kai yayi yace wannan gaskiya bari zan Nemo musu mummy, kunaso ko? Suka daga kai da sauri tare da fadada murmushin su amma dai sahir abun bai kwanta masa ba.

Ayush tace AI na samo maka kanason ka hadu da ita? Shiru tayi kamin yace
KO BAN GANTA BA NASAN ZABINKI YAYI DON HAKA ZAN AURETA!

GENG! GENG!! GENG!!!

Cabdi akwai cakwakiya fa jama’a.

Me zaku iya cewa gameda CHAPTER dinnan? Ya kuke ganin za’a kaya ne wai.

Karku manta kuyi VOTING tareda FOLLOWING Dina.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button