KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Duk cakwakiyar nan da ake yi minal bata sani ba Dan har taje ta dauki naman da sabir ya bari ta fara ci. Sabir kuwa lura yayi da bata wajen hakan yasa ya saki mai nama ya juya daidai lokacin kuwa ta danna albasa a baki. Murmushi kawai yayi ya zauna a gefenta. Yace ya sunanki? ?uri tayi da ido tana kallonsa,murmushi ya sake Mata yace yunwa kike ji? Ta daga kai daidai lokacin wayarsa tayi ringing.

Yace hello hajiya. Tace sabir ina ka tsaya ne yace ganinan dawowa daga nan ya kashe. Tashi yayi tare da cewa yar uwa sai gobe ki? Murmushi? tayi ta daga kanta. Daga nan ya dale babur dinsa ya wuce itama daukar ledan ta tayi ta fara tafiya. Tana cikin tafiya ta taka kaya hakan yasa ta tsalla ihu.

Ashe daidai ginin yan shaye shaye ne lado yace tattabara daga sama gasassa.
Sabi ne yazo ya sunkuce ta bai ajiye ta ko ina ba sai cikin ginin. Kuka ta fara musu ga zafin kayan da takeji lado ne ya ajiye kwalbar giyan dake hannunsa ya fara zare belt. Baya baya ta fara yi daidai lokacin Allah ya taimaka Mata aka dauke wuta dan haka area din gaba daya yayi duhu. Kwalbar ta raruma ta kwalawa ma wani sannan ta Mike fa fara bin gini aiko ta taka kwalba. Toshe bakin ta tayi tana fita aka kawo wuta hakan yasa suka bita a guje ashe sabi nigga ta kwalawa kwalbar.

Gudu suka dinga yi kamin ta samu ta labe a lungu sai haki take taji an dafa kadar ta juyowa tayi suna hada ido ta zaro ido tare da kwala ihu…

I know that wasu haushin abin da ya samu minal sukeji. Hakuri zakuyi labarin ne yazo da haka.

Su o o har ankusa zubda kwalla saboda tausayin minal.

Karku manta kuyi VOTING,COMMENTING tare da following Dina sannan kuyi SHARING da followers dinku domin kar a basu labari.

ONE LOVE?

Miss Untichlobanty ?

28th March,2020.

??KURUCIYAR MINAL??

?by miss_untichlobanty ?
INSTAGRAM:@miss_untichlobanty

TWITTER:@miss_untichlobanty

WATTPAD:@miss_untichlobanty

?CHAPTER 79?

RECAP

Kwalbar ta raruma ta kwalawa ma wani sannan ta Mike ta fara bin gini aiko ta taka kwalba. Toshe bakin ta tayi tana fita aka kawo wuta hakan yasa suka bita a guje ashe sabi nigga ta kwalawa kwalbar.

Gudu suka dinga yi kamin ta samu ta labe a lungu sai haki take taji an dafa kadar ta juyowa tayi suna hada ido ta zaro ido tare da kwala ihu…

CONTINUATION

Ba kowa bane illa sabi nigga, aiko ya wanka Mata wani jahilin Mari Wanda ya sata faduwa ba tare da bata lokaci ba.
Dariya ya sheke dashi harda rike ciki, hakan ya bata daman rarumar dutse ta tashi a hankali sannan ta kwala masa.
Ihu ya saka yayi da ta fita a guje tana mai tallafo cikinta Wanda ke Mata zafi a halin yanzu.
Sauran yan daban ne sukayi saurin karasawa wajen sabi’u sakamakon ihun sa da sukaji. Tambayan sa suka fara yi lafiya ? Ya nuna musu hanyan da minal tabi. Biyu daga cikin su ne suka bi hanyar yayinda lado ya tsaya, ya tallafa masa ya tashi sannan ya fara kokarin kaishi gida.

Minal gudu ta sharara har sanda kafar ta suka daina gudu kamin ta Sami zauren wani gida ta shiga. Itacen girki ta gani a jibge gefe guda dan haka taje ta jingina a jiki babu bata lokaci tayi bacci dukda ko a jikinta? tanajin akwai abinda ya dace tayi Wanda batayi ba.

??

Yazeed bai bude idanun sa ba sai wajajen karfe Goma na dare. Akan fuskar ayush suka fada ta sakar masa wani murmushin munafurci tare da fadin brother sannu da tashuwa. Kallon ta yayi da alamar tambaya yace brother? Tace eh karka damu dama likita yace min zaka iya manta wasu abubuwa so karka damu, San baka dukkanin information da kake bukata. Jinjina kai yayi alamun toh yana kare Mata kallo Dan shi bai ma yarda da ita ba yace wacece ke? Murmushi tayi tare da zama a bakin gadon sa ta riko hannun sa. Dan janyewa yayi tace karka damu ni muharramar ka ce,ni kanwarka ce, your baby sister ka tuna?? sakan jiki kadan yayi yace toh me yasa aka kawo ni nan? Tace saboda tun sanda mahaifin mu ya rasu kake cikin damuwa hakan yasa kake samun wani ciwon kai me tsanani Wanda yakan sumar dakai wani lokaci ko ya sabbaba maka manta wani Abu toh wannan karan da alamu alakarka da mutane ka manta.

Jinjina kai yayi domin maganan ta kama kwakwalwar sa. Yace munada mahaifiya tace eh tana gida yanzu kaga hotanta. Ta fadi hakan tana mai nuna masa wallpaper wayanta. Hoton su ne su hudu, shi da ita da mummy da umma hani. Yace toh ai Mata biyu ne wajen waccece ita? Tace me kwalliyar nanne mana. Wancan kuma umma hani ce nanny din mu. Ajiyan zuciya ya sauke yace bani ruwa insha, Darius tayi kamar shasha tace au na mance na tsaya ina maka surutu.? Murmushi kawai yayi tare da karbar ruwan yasha.

Nan dai taci gaba da masa bayanan karya shi kuwa Allah sarki bai sani ba sai shiga yake tare da rike komai da take fada masa.

??

Gidan mahaukata sukasa aka kai mom bayan an haukatar da ita. Mai kawo abin ci ne tazo tana wulla musu hara ta iso dakin mom Wanda yake na karshe. Tana kallon mom taji kamar ta Santa kuma lokaci daya taji mahaukaciyar ta kwanta Mata a ranta. Wulla Mata nata abin cin tayi mom taso ta dauka ta kyalkyale da dariya kamin kuma tace na gode.

Fara co tayi tana yamutsa fuska da ka ganota kasan bata Saba shan wahala ba. Tsayawa kallonta tayi kawai sai taji hankalinta ya kwanta da mahaukaciyar. Bude dakin tayi ta shiga sannan ta rufe, a take mom ta fara ja da baya tana fadin karki matso kusa dani! karki matso kusa dani! Matar tace kwantar da hankalin ki ba abin da zan miki.

Zama tayi a gefenta kawai sai mom ta fashe da kuka. Matar me suna senior hauwa tace me aka miki kike kuka? Mom tace ?a na, zasu cutar min dashi! Senior hauwa tace ina yake kuma yaya sunan shi? Shiruuuu mom tayi kamin tace nima ban sani ba, na manta sannan ta sake fashewa da kuka.

Rarrashin ta senior hauwa tayi haka sukayi hirar su dukda cewa wani lokacin mom din takan Mata hauka amma dukda haka tana zargin wani Abu tana ganin haukan mom din ba haka kawai bane.

??

Washe gari da safe aka sallamo yazeed kuma har wannan lokacin ayush tana like dashi, mummy ne tazo tayi musu oyoyo, taci ado ta kashe saurin dankwalin shaddar nan, gwala-gwalai ta ko ina abin nema ya samu.

Daidai lokacin wayan ta yayi ringing hakan yasa tayi excusing kanta kamin ta haura sama. Goje ne ke kiran ta, tace baby ya akayi ne? Yace lafiya kalau wifey dama so nake mu hadu tace okay no problem ka sameni a Sheraton hotel, royal suit daki na uku yace ba matsala sai mun hadu.

Motar luku ne suka ta iso suka fito suna cewa ina president? Wai attack dinka ya tashi ko? Nan sukayi masa jaje domin suma an juyar da kwakwalwar su sannan suka koma side dinsu, kuma a daidai lokacin ne su zakiyya suka shigo ita da Jamal. Yazeed yayi shaking hannun Jamal yace gou are Jamal ko? Jamal yace yup ashe baka manta ba. Dariya yazeed yayi yace ai little sis ta fadamin tace idan naga balarabe toh shine cousin Dina jamal. Jamal yace tabbas kuwa amma ka daina damun kanka, uncle ya tafi babu abinda yake bukata sai addu’ar mu. Mummy ta fara share kwalla kamar da gaske.

A halin yanzu dai abinda suka nuna ma duniya shine baban yazeed ne ya hada jini da larabawa saboda kimanin yazeed da kuma Jamal idan ba haka ba ai mummy yar najeriya ce futuk dan haka basuda explanation shi yasa suka hado wannan karyar tunda dai a zahirin gaskiya mom ce balarabiya kuma sun batar da ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button