KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Abinda yasa mutane kuwa basu ganin ta saboda a kwance taje kuma booth din bai wangale sosai ba da mai motar zai gani ta mirror ya rufe. Jin an tsaya yasata buya a cikin rigar mota.
Aikuwa baifi second uku ba securities suka duba booth din inda suke ce masa malam you are careless fa, kana bari booth ba’a rufe ba ko? Dariya hausar securityn ya bawa zayyana. Kunshewa tayi yayinda suka rufe masa booth din amma bai rufu ba nan suka gane cewa hook din ya baci ne sannan suka barshi bayan sunmai warning.

Ciki ya shiga ya yayi parking sannan ya fice bayan kamar minti biyar sai ta fito. Kokarin karanta abinda aka rubuta a sama tayi. Shoo….s..ho? Kai sho…pi..re.. a ah ri ne. Sho…pi..ri..te….

Dariya ta kyalkyale dashi tace kai ni banza ce wallahi ashe shoprise ne toh ko me yasa suka rubuta shoprite oho.
Wasu family masu yawa ne zasu shiga ta shige cikinsu suka shiga tare nan fa ta fara ciyar da idonta abinci. Officials idan sun ganta sai su tambayeta ta harshen turanci itako dayake kwakwalwar kamar na uwar ne sai kawai tanuna wani waje tace can sai ta hudu. Su kuwa basu gane ba duba da kayan jikinta sabi ne masu kyau Wanda aka bawa sabir ya basu kuma tanada harke dukda cewa batakai mamanta ba sai suke Mata ganin ajebo.

Tana cikin tafiya ta iso wajen na’urori(gadgets) sakan ido da baki tayi tana kallo cikin karamar muryata ta yara tace kai jama’a kaga wayoyi masu kyau ba irin na ummi ba. Bara in dauko Mata wancan.

Juyawa tayi taga wani ya fito mutane biyu na binshi a baya. Sai taji ana sanarwa da turanci tabe baki tayi tace ko me suke cewa oho.
Wallet din mutumin taga ya fado da alamu bai lura ba Dan haka ta dauka budewa tayi taga kudi har ta juya da gudu tanajin dadi sai ta tuna abinda minal ta fada Musu “misalin abinda ba naki ba kamar wuta ne, shin zaki dauki wuta balle kici?” Juyowa tayi da gudu ta fara binshi tana uncle! Uncle! Uncle!

Yana tafe yanajin anata uncle amma bai dauka dashi akeyi ba.? Jin ana uncle me kaman larabawa yashashi tsayawa tare da ganin wake damun mutane da ihu haka. Wata yarinya ce ta tsaya a gabansa tana haki. Cikin ?ufula yace ehm? Lafiya? Cikin yatsine fuska irin na ka renamin wayo zayyana ta kama kunkumi tare da cewa kaji min mutuminnan fa. Kama rasa abinda zaka ce min sai uhm lafiya? Karka kaga shekarana 8 karfi gareni. Nausa hannu da kafa tayi yayinda tayi murmushin gefen baki yace calm down little girl me kikeso. Tace ni ba little bace fa ehe yace okay big lady (babbar mace) inajinki, uncle yana sauri. Kauda kai tayi tare da miko masa wallet dinsa shafa aljihunsa yayi yaji babu. Murmushi ya danyi ya karba tare da shafa kanta yace godiya nake boss lady 5k ya miko Mata ta karba ta jujjuya yadau ta Rena ne sai yaga ta dauki daya ta dawo masa da sauran tace daga gani manyan kudi ne Dan haka kwalli daya ma ya isheni a madadin wadannan ka mayar dani wajen ummi na. Murmushi yayi yace angama boss lady muje ko sannan ki rike wadannan din ma na baki.

Washe baki tayi tace ba gode sannan ta riko hannunshi suka fito. Mota suka shiga nan ta fada masa abubuwa Sheda data rike a kanta na inda tabar minal yace boss lady wannan wani irin kwatance ne babu sunan anguwa sai sunan wani gini ta ina zan gane. Driver dinsa yace na gane wajen sir yazeed yace muje toh. Suna cikin tafiya tace kai gaskiya uncle motar ka nada kyau. Yace Allah ko boss lady? Nikam ya sunan boss lady. Cikin jin dadin zancen ta gyara zama tace sunana zayyana zaka iya cemin zayya, kaifa uncle yaya sunanka? Yace sunana uncle yazeed. Tace naji dadin ganinka uncle yazeed. Hirarsu suka cigaba dayi har suka iso tace yauwa tsaya anan gasucan bude kofa tayi ta sauko tare da cewa uncle na gode sai wata rana yace haba boss lady bakyaso inga mommyn mu ne? Tace nk no no mummy na kyakkyawa ce sai da kudi ake ganinta. Rugawa tayi a guje zai bita secretary dinshi yace sir mutanen nan sun iso suna meeting hall kuma kai suke jira and masu neman aikin personal assistant dinka sun hadu for interview hakan yasa ya hakura tare da sa ran zai dawo domin meeting din is important yaso ace ya kalli Fuskar maman amma ta bashi baya da alamu mutanen dake cikin motar gefenta ke mata magana.

Zayya tana isa taga wasu yan Mata suna fadin baiwar Allah ya haka zaki zauna da yarinya me bacci a titi kina kuka dauke kai tayi ganin sun takura yasata cewa ta mutu…. zayya tace me?! Ummu me kike cewa sahla ta mutu? Har idonta ya ciko da kwalla ya fara zuba faduwa tayi a guiwanta ta matso kusa da ita tace kanwata karki barni Dan Allah.? Daya daga cikin yan matan ne tace karkice ta mutu muje gida a kawo likita ya duba ta dai tana da rai.
Mikewa minal tayi cikin fitar hayyaci tace kin tabbata tana raye baiwar Allah karki sakamin rai fa.
Sai a lokacin suka kalli fuskarta take suka ja da baya baya sunan fadin wayo Allah mun shigesu. Nafeesa tace aunty me nake gani haka?

GENG GENG GENG ME YASA KUKE GANIN SUKA TSORATA? SANNAN YAYA RAYUWA ZATA KASANCE? DONT FORGET TO VOTE, COMMENT AND FOLLOW ME.

DEDICATED TO @?+234 703 556 2830?,@?+234 814 123 0581? and #kuruciyarminalfans

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU wato

miss Untichlobanty ?

12 April, 2020.

?? KURUCIYAR MINAL??

? By miss Untichlobanty ?

? CHAPTER 83?

RECAP

Zayya tana isa taga wasu yan Mata suna fadin baiwar Allah ya haka zaki zauna da yarinya me bacci a titi kina kuka dauke kai tayi ganin sun takura yasata cewa ta mutu…. zayya tace me?! Ummu me kike cewa sahla ta mutu? Har idonta ya ciko da kwalla ya fara zuba faduwa tayi a guiwanta ta matso kusa da ita tace kanwata karki barni Dan Allah.? Daya daga cikin yan matan ne tace karkice ta mutu muje gida a kawo likita ya duba ta dai tana da rai.
Mikewa minal tayi cikin fitar hayyaci tace kin tabbata tana raye baiwar Allah karki sakamin rai fa.
Sai a lokacin suka kalli fuskarta take suka ja da baya baya sunan fadin wayo Allah mun shigesu. Nafeesa tace aunty me nake gani haka?

CONTINUATION

Nafeesa wacce bazata wuce shekaru 18 ba tace aunty me nake gani haka? Me aunty bushra keyi anan ba yanzu muka barota a gida ba? Dakata, y
anzu na gane abinda sabir ke fada dazu Allah sarki ashe da gaskiyarsa

Mintuna kadan da suka wuce

Sabir na komawa gida ya iske wannan labari haka yadan bi sawu amma bai gansuba cikin tashin hankali ya nufo gidan da yake gadi domin su taimaka a sanar a gidan rediyo, talabijin da sauran su.

Acan kuwa……
“Oyoyo aunty Bushra sannu da dawowa” nafeesa wato feena ke fadin haka yayinda ta rugo a guje saura kiris ta fadi a beni sanadiyyar karar motan da taji. Wata budurwace ta fito daga ciki tana yarfe gashinta dake kan farin fuskarta tare da gyara tabarau din dake manne a idonta murmushi ta saki lokacin da ta sanya kanwarta nafisa a idanunta. Rungume juna sukayi feena na turo baki cikin shagwaba tahau magana…

Amma wani hanzari ba gudu ba na kasa saurara balle har na rubuta abinda take fadi domin nifa ba kowa nake gani a tsaye ba sai minal cikin kananun? kaya saide wannan tafi minal kiba da kirji sannan minal ta fita gashi? da tsayi.

Sauran yan gidan ne suka fito suna Mata marhaban. Ana cikin haka sabir ya shigo duk ya hada gumi yana fadin hajiya wannan baiwar Allahn ta gudu daga gida sabod……..
Maganarce ta makale masa a makokoro cikin rawar yatsa yake nuna bushra yace yar uwa me kukeyi anan sannan ina yaran. Wani kallon ka renamin wayo ta mai tace (Dan Iska me ka kirani yanzunnan?) what the fuck did you just called me? Baki ya bude zai bada amsa amma bai samu dama ba sanadin Marin data yanka masa. Mahaifiyarsu ce ta riko ta tare da cewa ke bushra bakida hankali ne zaki daki namiji? Kuma ya girmeki? Banason rashin tarbiyya, au abinda kika koyo a turan kenan? Toh bari mahaifinki ya dawo zakiga ikon Allah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button