KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Motsowa kusa da fuskanshi tayi cikin ra’da tace kai Dan iska ne kakeson ka kalleni babu Komai abin tausayi yazeed yayi ya girgiza kai tace good yanzu abinda za’ayi ka rakani in dauko Riga shara shara kaga sai in saka sai kaga jikina amma mutane haka zasuce ai inada Riga kaga Mun musu wayo ko?ta fada tana murmushi ita a dole ta kawo idea.

Tadawa su kayi sannan suka nufi dakinta suna ta shirme amma yazeed yanzu zai iya tafiya saide Ba control.
Koda suka shiga dakin minal din, Yazeed Idanunsa a rufe yace ina kika ajiye rigunan toh ? Kicin kicin tayi da ido tace bude idonka! Turo baki yayi yace aunty bacci tace baka isaba bude idonka. Cikin muryan kuka yace Kiyi hakuri to na bude.

Tace good amma fa a akwatina suke babu rigunan a wardrobe dina saboda bana sawa tunda Ba mai gani ko nasaka. Yazeed yace aunty to Daga yau ki fara sawa zannan gani pleaaase! Shafa kanshi tayi kaman Yaro tace angama.

Karamin store din dakinta ta bude ta janyo akwatin sannan ta bude suka kwaso duka transparent rigunan Baccin nata suka jera sannan ta dauki wani baby pink.

Bayan ta miyar da akwatin ta fito tace zan saka rigan.
Hannu yasa ya rife fuskansa kokarin cire bra dinta ta fara dakyar dai ta cire Dan sanda tayi minti 3.

Yazeed ne ya fara kokarin lekota ta tsakanin yatsansa tace wallahi kana lekoni zancewa mamanki kai Dan iska neh. Da Sauri yace na fasa karki fada please.

Saka wancan rigan tayi sannan ta dauke wanda ta cire takaishi laundry koda ta dowo yazeed ya fara gyangyadi da hannunsa a fuskarsa.

Tace tashi mu tafi in maka tausan. Komawa dakinshi su kayi  ya cire wandonsa Daga shi sai short nicker ya dale tsakiyar gadon. Turo baki tayi tace to NASA rigan Baka kallah Ba. Kallon yayi sai alokacin yaga yadda tayi kyau bai San lokacin da tazo ta zauna kusa dashi Ba hannun da tasa zata rife masa baki shi ya ciroshi Daga Inda ya shiga.
Tace rife bakinka kar sauro ya shiga. Yace Gaskiya ne Aunty Ba karya kinyi kyau. Washe baki tayi tace dagaske tana Dan Daga murya yace har cikin zuciyata kuwa. Peck ta masa a kumatu sannan tace amma Gaskiya ka mtsa Dan wajennan yamin kadan yace wa yace miki Anan zaki kwana dariya ta kyalkyale dashi kamin tace ai Anyi an gamayace zamuga ni bazaki kwana Anan ba. Tace to mu kulla, suka kulla yatsa sannan ta fara masa tausan Kamar yadda takeyi wa baba amma harda mugunta aciki.

Tashi yazeed yayi ya zauna a take kamin yace haba yan mata irin wannan dannan ai ko makiyinki albarka ai saiki karyamin baya. Tausa kwata kwata babu armashi.

Hararan shi tayi tace Toh sannu mai armashi sai ka koyamin tausa mai armashi ai ni Idan Nayi wa baba tausarnan har kyautan kudi ko goro yake bani wani sa’in shine zaka wanine Ba armashi? Yace to ai baba kikace ni kuma Ba tsoho ba ne.

Kicin kicin tayi da fuska tace kana nufin baba na tsoho ne?girgiza kai yayi yace wasa nake fa Kiyi hakuri,Tace yafi maka. Kwantar da ita yayi sannan ya fara mata tausan ajiyan zuciya ta sauke tace kai wallahi dadi yace to wannan itace tausan me armashi tashi kimin tace Dan imin na minti biyar sai in ma.

Tausan yayi mata har na minti biyar ko kasa da haka tunda ba Duba agogo yake ba,itako dadi takeyi zatayi winning Dan haka ta fara Baccin karya. Jin saukar numfashi yasa yace toh tashi saura ni yaji shiru. Yace aunty yana Dan jijjigata shiru.

Sake jijjigata yayi yace aunty ki tashi mana kimin. Bude bakinta tayi da kyar tace bacciii….
Turo baki yayi yace wannan fa ojorone fa. Tace zanmaka double gobe daganan ta bingire gaba daya kuma babu lokaci Baccin gasken ya tafi da ita.

Kwanciya yazeed yayi akan ruwan cikinta shima ya bingire haka dai suka dinga auna style din bacci kala kala musamman ma minal Dan babu lungun da batakaiwa ziyara ba akan gadon tsaban birgima.

🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹

Da safe around 8 zakiyya ta hau ta dire Cewa sai ta kira yazeed yayinda mamanta tace ta bari a sallameta  mana tace lala.

Wayanta aka bata aiko ta laftowa yazeed kira……

🌹…….

Yazeed kwance minal akan kirjinsa ko sallahn asuba basuyi ba saboda kwayar dake kansu.

Wayarsa ce ta fara ringing aiko ya tashi atake saboda yadan tsorata amma sai yaji wani Abu mai nawi ya danneshi kallon kirjinsa yayi yaga minal tana bacci hankalinta kwance Dan batamasan wani Abu waishi waya ya buga ba.

Dama kunsanta da nauyin bacci a haka ma ya aka kare?

Ahankali ya dagata ya kwanta da ita akan pillow yana murmushi kamin ya tashi ya dauko wandonsa dake wulle akasa ya Ciro wayan sai alokacin ya lura da yanayin da yake sannan duk abinda ya faru na haukarsu ya dawo masa kamin ya Lula duniyar tunani wayansa ya kara ringing hakan yasa ya dauka.aiko kuka ne ya fara ma dodon kunnansa marhaban.

Yace subhanallahi zakiyya menene ya fadi haka yana zama akan gadonsa gefen minal.
Tace baby boutique dina? Yace me yafaru da boutique din tace ya kone gaba daya Wai babu abinda aka cire sabon ma an kwashe kayan ciki sannan aka rusa.

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un kawai yazeed ya iya fada kamin yace Kiyi hakuri Allah yasa haka shine mafi alkhairi bari idan kin dawo zamuyi magana sai a gyara ko? tace Toh baby saina dawo.
Yace I miss you tace me too sannan ta kashe wayarta ba ko godiya.

Wallahi banyi niyan typing ba amma danaga comment din wata Wai batayin bacci dakyau kwana biyu saboda jiran update shi yasa na fara rubutu karfe goman dare.😜

Waiting for your comments and don’t forget to share

Karamarsu babbarau ce

Miss untichlobanty💕

9th December, 2019
[1/11, 2:29 AM] Mzz_Untichlobanty💞: 🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by miss untichlobanty🌹

CHAPTER 53

Juyowa yayi domin ya kalli minal dake gefensa wacce ringing din wayarsa ta biyu ta tasa aiko suka hada ido tayi Saurin rufewa Kamar mai Baccin gaske.
Yazeed yayi murmushi cikin rashin kuzari saboda har yanzu bata gama sauka Ba tunda Ba saba sha yayi ba yace na kamaki kazame kallo na kikeyi.

Blushing ta fara bada San ranta Ba kumatunta yayi jaa Kamar tumatiri kamin ta tashi ta zauna tana mai rife ido da Hannu.

Tace ina kwana ? yace lafiya amma Daga yau Ba ina kwana nakeson kice min Ba. Tace Toh me zance? Motsowa yayi ya janyota jikinshi sannan cikin kunnenta yace good morning zaki ce min sai kimin sumba.

Girgiza kai tayi tace ni kunya nakeji. Yana smirking Yace humm! Amma Idan zan iya tunawa dakyau jiya rigarki ma kika cire a gabana kuma da kiketa rife ido a haka muka kwana.

Sai alokacin minal ta tuno aiko ta zabura ta fara kokarin Jan bargo yace rabu da bargo babu laifinsa.
Turo baki tayi tace ai Dan bana hayyaci nane.

Serious face yazeed yasa ya hade gira alamun tunani sannan yace zamu tattauna akan wannan ma amma yanzu karfe nawa ne? Minal ta zaro ido tace bamuyi sallah ba!!

Aiko ta tashi da gudu ta nufi toilet.
Wankan tsarki tayi dukda babu abunda sukayi amma dai a Kore kokonto.
Fitowa tayi yace ko dauko kayanki muyi sallah Anan sannan ymshima ya Shiga.
Dauko doguwan Riga irin na shan iska tayi sannan tasaka ta zauna a bakin gado tana jiranshi yayinda ta Lula tunanin me yasa aka basu Kayan maye?kuma Waye ? Sannan taga yaya aka zuba musu?

Tana cikin tunanin na batasan sanda yazeed ya fito Ba saiji tayi ya hura mata iska a fuska yace kazame me kike tunani? Tace zan fada ma muyi sallah tukunna.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button