KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Ba’a tsufa ko girma daneman ilimi,idan bakusamu kunyi da yarinta ba lokaci bai kure ba tunda har yanxu kuna shan numfashi.
Kusaka yaran Ku amakaranta na boko da addini kodan suyi alfahari daku
Abin kunya ne ace Wai semi yar cikin Ku da Kanwarka bayanku ne zan Samar daku abinda ya dace.
Ku Duba abinda nake iya rubutawa?I am just 14 years, 11 months,20 days kuma ina university sannan na haddace takaddun addini turum. what do u expect idan nakai 18?what of 20? ba cika baki nake ba amma kuma kunsani akarancin shekarun da nake dashi inada tunanin manya.
Abin kunyane ace yar cikinki ko kanwar bayanki ta Fiki zurfin tunani.
Wani abin da ke bani haushi shine ‘Yan mata masu shekaruna yanxu Kansu rawa yake,yanzu ne suke ganin Suma sun girma baza’a barsu a bayaba,Suna ganin sunyi boobs Kansu daya da uban kowa,basuda burin daya wuce ayi shigan tsiraici ana yawo a gari ana karya ka’ida da iyakar Allah,ana kara yada zina acikin alumma,tun daga fitanta har dawowanta mala’iku na tsine mata,manzon Allah ya tsine mata,bayin Allah salihai na tsine mata, ai tundaga nan ya kamata ta fahimci ta Shiga ukku,ta gama yawo ta lalace wallahi Mu kiyayi haduwar mu da Allah abin kunya ne kaje gaban Allah kana mai saba masa ka wulakanta a duniya ka wulakanta alahira.
Su mazan da suke ganinku suce u look breathtaking,u look sexy,u look hot ke tun daganan ansami matsala hot fa akace ba cool ba kinga ko anfada miki Inda mala’iku zasuyi dake ne in baki canja hali ba. Ancemiki zasu aureki ne ?babu mai aurenki lalataki zasuyi suyi gaba,wallahi ku ji kunyan randa zaku tsaya gaban Allah ana miki shari’ah keda iyayenki. Mu rufawa kanmu asiri mu nemi ilimi muyi aurenmu cikin rufin asiri har Allah ya karbi rayukan mu.)
Lovelies kuyi hakuri yau duk Mun kare a lecture wallahi rainane ya baci da abinda ke faruwa,duk mutane sun kwashe kayansu daga gaban annabi,amma karku damu I will make it up to you😉 Ku tayani da addu’a inada test guda biyu tomorrow masu zafi ne aradu; chemistry and Arabic thanks for your love
Your one and only favorite yobe girl,karamarsu babbarsu
Miss untichlobanty💕
8 September,2019.
[1/11, 1:52 AM] Mzz_Untichlobanty💞: ðŸ†ðŸ†KURUCIYAR MINALðŸ†ðŸ†
🌹by @mzz_untichlobanty🌹
CHAPTER 25
An daura auren minal da yazeed akan sadaki naira dubu 50,Yan uwa da abokan arziki NATA taya murna makiya ma na hassada
Allah ka barmana makiyanmu kodan su zama dalilin da zamuyi nasara. Kai jama’a Imagine life without munafukai Allah barmana Ku Yan wuta😂
Mom ta aiko da kayan abinci da abubuwan da za’ayi walimah Dan babu wani event da za’ayi. Saboda abin yazo a kurarren lokaci ko mai wa’azi ba’a sami daman kira Ba.
Bayan la’asar akayi da mom Cewa za’a daukan minal around 5 pm inji ango(mom anya wannan magana kuwa zan yarda da ita?).
Hakan yasa aka fara shirya Amarya around 3:50 bayan Anyi sallar la’asar.
Liffaya mai kyau tasa wadda aka siyo mata awajen reemah’s collection. Wani sarkan gold akasa mata Wanda yake na inna ne family necklace dinsu. Babbar ya ake bawa in za’a kaita dakin miji. Kuma ba’ayarda ka siyar Ba amma zaka iya upgrading.
Kyansa yananan Dan haka ba’amayi upgrading din Ba.
Dayawa daga cikin Yan makarantansu sunyi attending, ciki kuwa harda heedaya Muhammad da ma’ani yerima Wanda suke mutunci sosai.
Yan matan ne adakin minal yayinda aketa tsokananta itako sai cika take tana batsewa wai ita batason adinga zancen batsa a gefenta.
Hidaya ce tace Nide sake fuskannaki in gama kwalliyan yayinda ma’ani ke Cewa nikam yau sai na cika camera ta da hotuna, inajin ma inna sami dama zanje in karanta photography😉
Heedaya ne tace oh mude zamuzo muji ya aka Kare a Daren farko.
Harara minal ta ballo mata,aka fashe mata da dariya Ashe ta shaka,zaliha tace kai Ku rabu da ita bari ayi Daren farkon wannan Cuno bakin da take duk zata dena saide muga mutumiyar ka an zama miji dadi
Alamun zatayi kuka muryanta yayi tana Cewa wallahi zaliha karki bari na kamaki shegiya yar…..
Innace ta shigo tace inkika karasa sainaci ubanki.
Tunda ake hirar bansa baki Ba ina zaune a gefe ina typing a wattpad dina saboda kar ace na fiya rashin kunya sai alokacin na sako baki nace “assha!inna kin bata goma boyar bata gyaru ba in ita batayiba aike kinyi”
Dakuwa tayimin tace ingo naki yar jakan uban yarinya da baki cau cau Kamar babba kodan kinganki cikin Yan mata shiyasa kika falle ko?kinsa niqabi kamar da gaske ashe dai…….shegiya Da I damu Kamar na Yan chaina
Kafin ta karashe nayi Sauri nace wallahi Nide Ba yar China bace ina turo baki,aiko inna tayi kaina na fita a 360 har inacin karo da mutum Ashe ma sakina ce da habiba (from the nemesis of sakina)yi hakuri kawai nace kamin na ‘buya a zaure ina haki sannan na sauke niqabi na,na saka gilashi na saboda naga alamun maza a waje.
Ciki su sakina suka Shiga aka gaggaisa kamin suka wuce domin mazajensu na jiransu.
Kanwar dad din yazeed aunty nafeesa da Umma habiba wadda take step paternal grandma ga yazeed sai kuma aunty nina Kanwarka mom Wanda suka iso yau da safe sune sukazo daukan Amarya tare da motoci 3 kacal saboda basuso bidi’an tayi yawa
Aiko nan aka fara tashin hankali minal fa da taga da gaske tafiya za’ayi da ita kirjinta ya fara lugude duk dadin da takeji taji babu shi ya tafi kawai sai ta fara hawaye wiwi Ba magana nanfa wattpad fans dinta sukayi CAA anata bata hakuri amma ina kukan karuwa yake tunba sanda sukayi sallama dasu inna Ba dasu baba da ya abubakar.
Inna da baba hawaye suke hankali kwance yayinda idanun yaya abubakar suka ciko da kwalla deeje Kam an jika gaban riga ma da hawaye da majina sai alokacin na lura da kwalliyar da tayi kominta yayi matching da kayanta hatta Jan baki da eye-shadow, da brows din duka blue ne. Abin dai sai kun gani. Nikam share kwallan da zai zubo min Nayi domin tausayi. Rabuwansu was heart touching haka aka kwashemu mu 10 aka kaimu gidan amarya.
Tundaga kofa akayi mana maraba,kai Mun sami tarba me kyau dakin zakiyya aka nuna mana muka kai minal Dan bada amana mu Yan mata 8 da tsofi 2.
Ba yabo ba fallasa ta karbemu. Amma ni dai hankalina bai kwanta ba kuma naga alamun hakan a fiskan wasu daga cikin mu amma dai sai Nayi shiru. Kar aji mutuwan sarki a bakina.
nuna mana dakin minal akayi Wanda yake part din baki ne na sama kuma acikin sashin zakiyya yake ada amma an daba kuma an gyarashi kai ya hadu. Allah dai ya kyauta ya Kare Daga sharrin makiya
Aikuwa hidaya ta cika alkawari Dan photo kam gida yashashi har minal dinma sanda akayi mata pic amma sanda ta sake ado tukunnan.
Haka dai har dare yayi munata shewa da tadi kamin aunty Nina ta shigo tace mana motocin tafiya najiran mu haka Muka tattari kafufun muka tafi minal Kam kukanta ta bude sabon shafi Dan ta manta da Cewa ita daya zamu bari(saima ankai mutum kabari zai San kadaici. Allah dai yasa muyi dariya a kaburburanmu.).
Hmm ai batamasan gidan wa aka kawota Ba saboda kanta na cikin gyale har muka kaita daki kuma ai batasan yazeed Nada mata Ba kuma bata tbna Shiga side din zakiyya Ba Dan haka bata gano ba.
Lokacin ko da akayi musu maraba kuka take ga hayaniya Dan haka bata gane muryan mom ba.
Aunty nafeesa da mom ne suka shigo,mom tayi Sauri taje wajen minal yayinda ta dago chin dinta tana mai Cewa ” ‘yata me ya sameki?”
Kuka minal ta kara fashewa dashi ta rungume mom Dan ta dauka mom tayi attending bikin ne