KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Untichlobanty: Mun gode!
Ya abkr: Ba damuwa.(shafa kan laila)
Untichlobanty: 🎶wani ya kasa hakuri a daura,yana nema ya tarowa kansa zunubi🎶
Yazeed: waike baki iyayin shiru ne?
Untichlobanty: Gaskiya na fada ai
Yazeed: (ya jefomin pillow na kace😛)
🌹ðŸ€TO LAILA🌹ðŸ€
Q1. Ya kikaji lokacin da abubuwa suka rikice miki?
A. Na Shiga cikin rashin hankali Wanda bazai misaltu Ba. Amma aduk lokacin Dana tuna Allah madaukakin sarki yace ‘wa iza sa’alaka ibadiy anniy fa inniy karib, ujibu da’awattid dâ’i iza da’ân fal yasta jibuliy wal yu’uminû bîy la’alahum yarshiduûn’ sai inji karfi guiwa tazomin sai Nayi addu’a a haka har Allah ya yayemin.
Untichlobanty: masha Allah
Q2. Untichlobanty: shin kina ganin ya dace in hadaki da ya abkr?
A. Toh da yayanki zaki auramin?
Untichlobanty:😂 sunan babban yayana ma Abubakar ai kinga faduwa tazo daidai da zama.
Laila: hmm mtsw
Untichlobanty: (turo baki)wai meyasa kowa yake hantara nane?
Duka characters: saboda bakya iya rufe bakinki.
Untichlobanty: (Cikin tsawa) karyane Idan Nayi shiru harsai kundauka azumin magana nake.
Yazeed:please ki gwada mu gani.
🌹ðŸ€TO JAMAL🌹ðŸ€
Q1. To kai Jamal me zai dawo dakai Nigeria?
A. Saboda inga love mana
Q2. Kana ganin hakan Ba sa ido bane?
A. Ku da kuke karantawa Ba sa ido kuke musu Ba?
Mai tambaya:(dogon nazari) &?;%#$&#??!
Q3. Kai yaushe zakayi aure?
A. Ban saniba nima Ku tambayi untichlobanty
Q4. Wa kake ganin untichlobanty zata aura maka.
A. DEEJEH kanwar minal mana
Untichlobanty: (kicin kicin da ido tareda gade fuska) excuse me yazeed zanyi magana na minti daya. Wa ya baka izinin bada leakage? Nace ka fada musu ne?
Jamal:(kama kunne)Kiyi hakuri bazan karaba please!
Untichlobanty: huciðŸ˜
Yazeed:in Anyi magana kice zaki iyayin shiru
Minal: ka sake mata Mara Dan Allah haba.
🌹ðŸ€TO DEEJEH🌹ðŸ€
Q1. Me zakice game da auren yayarki?
A. Gaskiya na mata murna dukda ko bama shiru da ita amma ina sonta. Fatana nima allah ya bani miji kyakkyawa,me ilimi da mutunci kaman nata.
@real_Meenal: ai jam…
Untichlobanty: sister please shhh
Q2.yanzu ke shekarunki nawa?
A. Na kusa inyi 15 saura wata hudu.
Q3. Kinason kici gaba dayin boarding?
A. Laaa bakusan yaya yazeed ya mayar dani wani day school ba?😀in fada muku private ce ma.
Fans:ðŸ˜ðŸ˜‚ bakida dama wallahi kema Kamar yayarki
Khadija: aradu na fita hankali.
Minal:(Cikin harzu kowa)kina nufin banida hankali?
Yazeed: calm down baby….
Zakiyya: me zan gani haka?
Zaliha: Wai babyy….. Hmm
Khadija:😀laaa adda zaliha Ahe har kin gama wayar?
Everybody: (an tsaya kallon deejeh dake Washe mouth tana kokarin saka kwalli)
🌹ðŸ€TO BABA AND INNA🌹ðŸ€
Q1. Me zakice game da mijin daya Sauri yarku Amina?
Baba: a Gaskiya a kuma iya ganina yarone dayasan darajar Dan adam, yasan ya kamata sannan Yaro ne mai dattaku da nagarta. Koda kuwa bai mana Komai Ba yar mu ya aura a zamaninnan kamin ka sami me kudin dazai auri yar talakawa sai an tona
Yazeed: (Washe baki tareda Sosa kai)
Inna: Wannan Gaskiya ne malam.
Minal:(Cikin shagwaba)baby kayi pecking kumatuna
Yazeed: a gaban su?
Minal:ina ruwa na, kai Ba miji na bane?
Untichlobanty and fans:😨
Q2. Me zaki iya Cewa game da zaman su
Inna: yo ai idonku ya gane muku Dan haka bamu bukatar mice wani Abu
Baba:wannan Gaskiya ne saidai mu bisu da fatan alkhairi kawai.
Allah yayi albarka
Kowa:AMEEN!
🌹ðŸ€TO MASHKUR🌹ðŸ€
Q1. Kaine Doctor Mashkur ko?
A. No Dr Ahmed ne. Nine Dr Mashkur mana ki wani tamabaya.
Mai tambaya: Daga tambaya?
Q2. Dama haka ko wani lokaci kana arrogance?
A. A ah tambayar da Anyi min ne dai sai a slow
Q3. Shin kana ganin patients din zasu farfado?
A. Ina sa rai de, aini Ba Allan musuru bane bansan gaibu Ba.
Q4. Kanada aure?
A. Banida shi
Q5. Kana ganin untichlobanty zatayi maka aure a littafinnan?
A. Karma tayi taga iko Allah
Untichlobanty: me zaka yi?
Mashkur: rokanki zantayi har sai kinmin
All:😦ðŸ˜ðŸ˜‚
Q6. Wa kake ganin za’a aura maka?
A. Gaskiya ina tunannin wacce za’a aura min itace…..
Untichlobanty: wallahi Idan ka karasa sai nasa kayi hatsarin jirgi kan ka iso ma.
Mashkur: Toh fans kunji ni kuma ban Shirya barin littafinnan Ba.
Fans: baza dai ka fada Ba kenan?
Mashkur: dalilin dayasa nakeson masu karanta littafinnan kenan, kunada sense irin na karshe dinnan.
Untichlobanty: (harara) what do you mean?
Mashkur: karki samu damuwa Ba abinda kike tunani bane ke legend ce ai.
Untichlobanty: (Dage kai tare da hura hanci.) Kai ka jiyo
🌹ðŸ€TO UNKNOWN VILLAIN 🌹ðŸ€
Q1. wacece ke?
A. Me yasa zan fada muku?
Mai tambaya: just curious
Q2. Me yasa kika tsani su yazeed?
A. Me yasa kuke Shiga Harlan da bata shafeku Ba ? And anyway ba karantawane littafin kuke Ba? Sai Ku jira ai duk tambayoyinku za’a answer muku.
What do you think of the Q’s and A’s?
Will be waiting in the comment section�
Don’t forget to SHARE
Miss untichlobanty💕
[1/11, 5:13 PM] Mzz_Untichlobanty💞: ðŸ†ðŸ†KURUCIYAR MINALðŸ†ðŸ†
🌹by miss untichlobanty🌹
CHAPTER 59
Bayan sun Shiga daki zama su kayi akan gado nan yazeed ya fara koyawa minal darasi Inda kullum zasu dinga yin vocabularies guda 20 tareda ma’anoninsu. Sannan zai dinga koya mata figure of speech.
Yayi mamaki sosai na yadda brain dinta ke daukan abubuwa saboda ta maida hankali sosai itama sai a lokacin ta gane Cewa abin maida hankali ne kawai.
Bayan sun gama karatu tayi masa tausa. Yace ta kwanta itama ya mata tace a ah ya Sosa mata kai kawai.
………………..
🌹ðŸ€DAWN🌹ðŸ€
Da sanyin ASUBA bayan an sallamo su zakiya Dan dole ta dage sai ta kamo hanyan dawowa gida babu yadda mahaifiyarta batayi ba amma tace Sam dole sai ta tafi.
Ayush tace haba sister Kiyi hakuri mana jijinki ya gama wartsakewa. Hararanta tayi tace ni da ke Waye babba? Ayush tace Kece zakiyya tace to ki shiryamin yarana mu tafi.
Ayush tace Toh. zakiyya tace ina nufin harda ke zamu tafi. Tace me yasa harda ni? Zakiyya tace saboda ban gama warkewa ba kuma kema your heart is broken.
Mummy tace Toh kibar min su sahir din mana. Zakiyya tace sanda nace kar a kawo min su ba dagewa kikayi saina rikesu ba?so yanzu nima ina son abina.
Hakadai Daga karshe suka Koma gida karfi da yaji suka Shirya kaya tareda kamo hanyar Kaduna.
🌹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€
Kai Jamal tashi Daga baccinnan Mun kusa sauka. Hade rai yayi yace mom bacci nakeji sosai tace Toh sai ka Fadawa pilot din ai ya jira ka gama Baccin kamin mu sauka Dan Allah ni tashi.
Daidai lokacin tayan jirginsu ya Dan gwali kwalta.
Suna saukowa mom ta cire wayanta a airplane mode zata kira yazeed.
Mummy ni yunwa nakeji
Hararan Jamal din tayi tace waikai meye matsalarka ne kwana biyu uhm? Ko kaima aure kakeson in maka.
Zaro ido yayi yace nii?na shafawa kaina ruwan sanyi ki rufamin asiri…..
Tace Toh shikenan dama maganar bata tsaya ba. Yace dakata kiji mana ai Idan kikamin din ma bata baci ba.
Rankwashinsa tayi tace ja’iri zama kayi magana ni rabani da sabgar aurenku yazeed din ma ya na jare dashi?
Daidai lokacin ta kara wayanta a kunne bayan ta fara Kiran yazeed.
🌹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹ðŸ€ðŸŒ¹
Koda su yazeed suka tashi sukayi sallah minal tace bari tayi tattare tattare ta daura abinci tunda Shigan safiya su mom zasuyi yazeed yace besan wannan zance ba kawai ta dawo su kwanta.