KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

Mr. President yayi bakin ciki na rashin jami’i mai gaskiya da amana Dan haka ya hada masa taron bankwana a wajen taron ne aka Kira yazeed domin yayi jawabi cikin jawabin Nasa ne yake cewa zai koma ya kula da hard work din mahaifin sa kuma insha Allah? daga ranan har tashin kiyama baya fatan shi ko wani a zuri’arsa su kara involving kansu da government business kawai zasuyi kuma individually zasu dinga taimakon kasarsu ba sai sun tsunduma kansu a cikin ba idan an nemi gudun muwarsu toh zasu bayar. Idan sunga ana Abu da ya Saba doka toh zasu yi magana.

Kuka jama’a keyi wiwi! Anan taron ne akayi presenting award of excellence ma yazeed as the BEST MILITARY PERSONNEL of the year. It was a heart touching moment,box daya na tissue paper na karad saboda kuka anan ne nima aka bani award Dina as THE BEST FICTION WRITER of the year. Muka ci abinci muka sha sannan muka watse ana ma juna fatan ALKHAIRI.

Washe gari da safe suka lulu suka dawo Kaduna domin yazeed yayi shirin fara aiki as JEEMAR GROUP PRESIDENT yayinda minal taga cewa ya kamata su ciyar da almajirai domin godiya ga Allah Dan haka asabar din data kewayo ta Nemo tsofi 20 aka fara girki. Manya manyan tukunya fiye da lamba hamsin guda 20 aka daura kenan ko wacce tsohuwa 1 tukunya 1, yayinda aka biya ko wacce dubu hamsin kuma anyi haka ne Dan a taimaka ma tsofin ma.
inspection minal tazo yi yayinda take testing ana bude tukunya farfesun kaji ta hau kakarin amai. Dannewa tayi ta dandana ai take ta fara amai ba sassauci nan hankalin tsohuwa ya tashi itakam kashinta ya bushe.

Kowa ya rude ya rikice aka samo likita ta dubata tace yuzu dai she can’t say amma tana suspecting ciki ne da ita dan haka aka bata pregnancy test tube aikuwa positive. Nan shagali ya karu murnane ba’a cewa komai, run saga ranan minal batada aiki sai cin gurasa da zogale.

BAYAN WATA 7

Minal zaune akan gado ta mimmike kafa bakin nan cike da gurasa da zogale yazeed shigo ya zauna a gefenta,daura kafafun nata yayi a cinyan sa yana Mata tausa saboda sun Dan kumbura yace mummy gurasa na shirya sai tafiya turo baki tayi tace daddy zogale ka tafi dani Dan Allah yace a hakan? AI idan na kaiki can zaki wahala ne gara nan akwai mom kuma ai bakuyi hutu ba karki damu yanzu zakiga weekend din ya kewayo na sake dawowa kinji? Tace Tom shikenan Allah ya tsare ya kuma kare yace ameen.

Saukowa tayi dakyar tare da kanka kwanta me kwabon zogale yazeed ya ja kumatun ta yace nikam Allah ya tunamin ranan haihuwar ki, irin wannan ci da kike yi zaki rakanin ma kina cin zogale cikin mamul mamul da baki tace babu ruwanka.?

Fitowa sukayi tibi tibi suna dariya har ya shige mota bayan sunyi sallama ya sauko ya rungume? ta tare da kissing gurasa da zogale (cikinta) yace bye bye my little babies da big baby dariya suka fashe dashi kamin ya shige motan suka wuce yayinda minal ta koma cikin gida.

…………………….

Zaune take a kan gadon dakinta yayinda take hango duk abinda ke faruwa a farfajiyan gidan, aani Luna da tafarfasa zuciyar ta keyi kamar tayi hauka haka takeji. Fincike drip din dake hannunta tayi yayinda ta yage riganta jiyoyin kanta sun tashi cikin huci tace nayi regretting aurennan da nayi auren banzan nan da nayi shi ke hannu kusantar ka masoyi na yazeed. Ke kuma sh*giya sai na hallakar dake da wannan tsiyar dake jikin ki sannan ta naushi gini Wanda har jini sanda ya fito daga hannun ta inda ta lashe tare da cewa na rantse da jinin nan sai na kasheki.

WA IYAZU BILLAH!

Toh masoyana Rabin raina, a halin yanzu dai ba baku satan amsan wacece ita. Shin a ganinku wacece ita? Duk Wanda ta canka zanyi dedicating Mata next chapter.

Me Kuke ganin zai faru a gaba?idan kika canka zan miki kyautar chapters guda 3 a jere.

Shin labarin nan yazo karshe ko da saura?

Ina tsimayi amsoshin ku. Domin inyi muku wani update yau ina bukatar comments masu tsari

Kuyi sharing lungu da sako domin wani ma ya samu.

Karku manta kuyi following Dina @miss_untichlobanty ta haka ne zan gane masoya na, na gaskiya.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU wato

Miss_untichlobanty ?

11th march,2020

??KURUCIYAR MINAL??

?by miss Untichlobanty ?

?CHAPTER 74?

RECAP…..

Surutu taci gaba da mai har bacci ya dauketa. Gyara Mata kwanciya yayi kamin ya kunna film abunsa…….

Koda jirginsu ya iso tashinta yayi tunda ba halin ya dauketa, ta departures’ door suka fito suka fito suka hango cars gida biyu ga wani ya daga carbon paper an rubuta captain yazeed abdulmajeed wajen motan suka nufa nan sojoji sula Sara masa direct hotel din da zasu sauka akayi dasu minal da zaliha an saki baki yayinda luku ke cin magani dan yanzu baya sakar wa zaliha fuska.

Akwana atashi anyiwa yazeed aiki kuma its successful. Nan fa su minal aka rikice nesa yazo kusa. Dakyar da dubara akayi abin, kunya duk ya isheta Dan gani take kowa yasan abinda ya faru.
Wasa wasa yau watansu 3 a Germany amma shiru kake ji babu ciki babu alamarsa ga yazeed yabar aiki jingim kuma next week za’ayi bikin kara masa girma wato ya zama major general yazeed abdulmajeed Umar.

Haka suka tattara ya nasu ya nasu suka dawo mom duk ta damu saboda tanason taga jikokinta kamin rai yayi halinsa tunda batasan sanda zata tafi ba.

Koda suka dawo Nigeria har anayi auren laila da ya Abubakar da kuma zakiyya da Jamal ba tare da bata lokaci ba. Yanzu haka laila nada cikin wata da sati biyu daya ma minal da fari ta dau abin wasa amma da taga cikin Laila abin yadan fara damunta amma ganin ai ba’a wani Dade ba yasa ta kwantar da hankalinta, yazeed na lura da ita kaf amma ya zuba Mata ido.

Shiri suketa yi yayinda minal da zaliha keta yin fada akan lallai sai minal tayi kwalliya yayinda ta dage cewa bazata yi ba.
Zaliha tace kinsan Allah idan dai bazakiyi kwalliyar nan ba zamuyi fada ? Bakisan cewa za’a dauke ki a camera bane ga yan jaridu da gidan talabijin dukzasu zo minal tace tunda ba gasar kyau za’aje ba bazanyi ba kuma ai miji akewa kwalliya ba ?artin banza dawofi ba. Kuma ni ance miki zanje ne dan adaukeni? Zanje ne Dan mijina. Dauko gyalen da zatayi rolling tayi Dan kayan da tasa baya bukatar hijab ta dau Jakarta ta fice dan zaliha ta bata haushi.

?

A bakin kofan side dinta tayi kicibus da yazeed ciccibarta yayi yana fadin wa ya tabamin baby na? Dauke kai tai tana kumbura yace my minal fishing harda ni ne? Sharesa tayi bai dirar da ita ko ina ba sai dakinsa, dakyar yashanyo kanta suka sha romance ganin yana neman zurfafawa yasata guduwa.

Haka akayi bikin Karin matsayi akayi su pictures kowa na farin ciki aka watsesaide kash basusan cewa nanne farin matsalar su ba.
Yazeed kwance kan cinya minal a parlour suna kallon wani Indian series tsabar abin tausayi minal batasan sanda ta fashe da kuka ba dariya yazeed keta Ma ta wai ta jona Shaun asararru masu yiwa film kuka sai turo kanshi take tana ya tashi tunda abin hakane daidai lokacin luku ya tsindumo babu ko sallama sai haki yake da alamu gudu yayi. Yace ina wayarka inara kiranka baka daga ba? Yazeed yace ba wannan yafi muhimmanci ba, wa ya baka izinin diro min cikin bangare ba ko sallama. Tsaki lukman yaja cikin haki yace kai dalla share wannan bakas……. bai karashe ba yazeed yakai masa naushi tsabar kishi. Minal tayi saurin rikeshi tare da kallon luku tace ya akayi? Yace government tasa an rufe gaba daya account din yazeed saboda ana zargin wai ya hada baki da yan siyasa anacin kudin kasa sannan bazai iya sayar da kadarorinsa ba ma atakaice de har company yanzu duk NASA ne amma suna under government so he does not have a say a kansu har nanda 3 months? Abu daya aka barma daga gidannan sai ka zabi mota daya. Yanzu haka EFCC suna bin cike kuma you can’t use your passport kamar kasan ba kuma baza’a baka Visa bama koda emergency har sai 3 months ya cika.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button