Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what’s app akan wannan lambar

07063065680
What’s https: //chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Is a free book

Ina yinku AbdulJalal novel fans irin???????????? da duk sauran masoya wannan novel ina jin dadin comments dinku love u all ❤❤❤

I want comments not stickers or just thanks????????????????
Your comments give me courage

Haka suka cigaba da tafiya sunayi suna hira jefi² har suka shiga garin Kaduna
Karfe 4 dai² suka iso kofar gidan su Jalila, suna parking Jalila ta fito bata tsaya bi takan JAWWAD ba balle trolley dinta, ta sakko ta ruga da gudu cikin Gida,
Ummi tana tsakar gida ta idar da salla Jalila ta shigo da gudu ta fada jikinta tana murna
“I really miss you ummina”

“To karyani ki huta sarkin fitina ga yanda kika shigo da gudu kaman an koroki,”

“Bikiyi missing dina ba ko ni duk na damu saboda rashinki a kusa dani amma daga zuwana kin faramin fada”
Ana haka JAWWAD ya shigo da trolley din Jalila,

“Au shi kikabari da dakon kayannaki? Kekam se a hankali”
Ummi tafada tana ture Jalila daga Jikinta

“Ba komai Ummi naga ta kagu ta ganki ne yasa ta manta da trolley”
Yafada yana murmushi

Murmushi Ummi tayi
Har kasa ya tsuguna ya gaida Ummi ya zauna
Ta amsa fuskata cike da fara’a haka ya zauna sukayi ta hira da ummi,
Ummi tana kaunar Jalal kodan yadda yake son diyarta dakuma yadda mahaifinsa yake tsaye akan lamuransu ita da yarta
Bayan haka kuma JAWWAD yarone me matukar biyayya da hakuri

Sallar la’asar yayi, be wani dade ba yace tafiya zeyi,
“Jawwad tun yanzu”
“Ummi bana son tafiyar dare ne”
“Hakane kam bata da dadi”

To Dan jirani ina zuwa daki ta shiga ta dakko wani turare me kyau tabawa JAWWAD yayi godiya sosai

Yayiwa Jalila alama da ido ta tashi tarakoshi waje
“Sisyna zanyi missing dinki zuwan nan naki yayi min dadi gashi kin dawo kin barmu”

“Allah sarki yayana nima banji dadin rabuwa daku ba “

“Sisyna kiyi karatu kinji nasan ke mutuniyar kirki ce, banda kula kawayen dabasu zuwa makaranta
Banda tsokana da shagwaba”
Ya karasa maganar da sigar tsokana

“Insha Allah yayana”
“Good very good sister, insha Allah very soon zan dawo mukoma”
Dan turo baki tayi batace komai ba

Mortar ya bude ya dakko wani jaka yabawa Jalila
“Thank u very much my brother”
“Shhhhh don’t mentioned dear”

“Wish u safe trip brother thank u very much ka gaida min da Nana ta”
“Zan gayamata and karki manta dayiwa yayanki addu a”

“Addu a mekakeso in maka”?
“No bani ba Jalila yayanki Jalal”

“Yaya kaikam narasa wanan kaunar da kakewa Jalal”

“Hmm sisy na kenan zakiji komai insha Allah in kinkuma zuwa kano zakiji dalili”
Yabude mota ya shige yatada mota yana daga mata hannu
Seda ya bace ma ganin Jalila sannan ta koma cikin Gida

“Ummina gayamin me yafaru bayan tafiyata ?”
“Ke dai bari Babyna gidan ba dadi daba kya nan, kawayenki na islamiyya se sintiri suke min, nayi missing dinki sosai daughter na”
Ummi tafada tana shafo fuskan Jalila

Jalila ta riko hannun ummi
“Allah sarki ummina haka kike sona dama?”

“Hmm Jalilana a duniyar nan a yanzu wanake dashi bayan ke kin ko son soyayyar dake tsakani da da uwa, da baki tambayi haka nakesonki ba”

To amma ya akai tsakanin Jalal da mummyn Sa basa jituwa shi bayajin wannan soyayyar ta mahaifiyarsa a ransa, Jalila tai maganar a zuciyarta

Da daddare bayan Ummi da Jalila sunci Abinci
Ta je ta dakko trolley din ta, ta dakko kyautukan da ta zo dasu ta nunawa Ummi sannan ta dakko Wanda ,Jawwad yabata

Katuwar teddy ne Ja da kuma manyan kwalin chocolate kusan guda biyar
“Allah sarki yayana Allah ya karemin Yaya Jawwad har yanzu be manta abinda nake so ba “
Ummi kallonta ta tayi tai murmushi
“Hmm Jalila kenan, Jawwad ya biyewa shirmenki hada siyamiki teddy da girmanki”

“To ni ummi har wani girma nayi
Yawwa Ummina tambayarki zanyi”

“Allah yasa nasani”
” Naga nabaki abunda akabani a gidansu Jalal baki tambayeni waye Jalal ba ko kinsanshi ne?”

“Eh nasan yaron koba makotan su Jawwad ba”?

” Ummi shine, amma kinsan yazama dan shaye² bashi da tarbiyya Sam bakiga yadda yakewa mamansa ba ya akayi kika sanshi?”

“Allah sarki Jalal da ba haka yake ba daga baya yazama haka abokin Jawwad ne tun suna yara kanana
Daga baya yakoma haka saboda wani abokinsa ko wayake oho?
Amma naji ance hada laifin mahaifiyarsa amma bansan ya akayi ba nikam”
“To Ummi ya akayi mahaifiyarsa tabari yazama haka”

“Ke rabu dani nima ban saniba sarkin tambaya meyasa baki tambayesu a can ba ni rabu dani bacci nakeji”
“To shikenan Ummi “

Har sun kwanta bayan wasu mintuna da kwanciyarsu,
Jalila ta nisa
“Ummina”
“Na’am Jalilana”

“Yaushe zaki kaini garinku inga yan uwanki?”
“Jalila meyasa kikayi min wannan maganar, so kike ki hanani bacci ko rigimar zakimin daga dawowarki ko baby, bana so yi baccin ki kawai nasan kingaji”
“Ummi bazan iya bacci ba sekin Sa ranar dazaki kaini garinku ni wallahi ko wasu irine ina so inje in gansu Dan Allah Ummi koba Sa sanmu ni inasonsu a haka Ummi kitemaka”
Jilila ta karashe magNar tare da rike hannun Ummi tana hawaye”

Fizge hannunta Ummi tayi
“Nemi gurin kwanciya kafin in wanka miki mari”
Ummi ta daka mata tsawa haka Jalila ta kwanta ta juya wa Ummi baya tana kuka
Har cikin zuciyarta Ummi takejin kukan Jalila tareda tausayinta.

Tayi rigingine tana tuna abubuwa da dama dasuka shude


Aliyu Imam Habib shine cikakken sunan mahaifin Jalila su biyune kawai a gurin iyayensu shida yayansa Usman Imam Habib (babansu Jawwad)
Mahaifansu sun haifi yara dayawa sun rasu su biyune suka rage asalin iyayensu Fulanin Adamawa ne ne akayi wata rigima yan fashi suka je rigar fulanin aka karkashe wasu, yawan hare² da ake kaiwa fulanin ya tilasta wasu suka watsu a Sassan Nigeria an kashe musu yan uwa da dama malam imam da shi da me dakinsa mairo sukayo hijira zuwa kano.
an kashe musu yan uwa dayawa, wasu daga cikin yan uwan Nasu kuma basu San inda suke ba abinda suka tsira dashi bashi da wani yawa, duk da kasan cewar su masu arziki a rugarsu amma haka suka siyar da abinda ya rage musu suka taho kano (ta dabo jalla babbar Hausa kodame kazo an fika)

Zuwansu kano a lokacin duniya tana kwance , a lokacin in akayi baki masarautar kano zamanin sarki Ado bayero ke bawa baki masauki Dan haka masarautar kano su sukabawa su malam imam masauki, inda akabasu katon Gida a unguwar mandawari
Gidansa ya kasance kusa da gidan wani alaramma malam shehu, malam shehu yanada Tarin almajirai dan haka zuwan malam imam kano basu San kowa ba wannan makocinasu shiya zama kamar Dan uwansu
Shi ya kai Imam kasuwa ya hadashi da wani almajiransa ya koya masa san’ar takalma a kofar wambai
Sannan in ya dawo sukan zauna da malam shehu ya koyamasa karatun addini
Imam yasamu Ilimi me tarin yawa a gurin malam shehu wanda ya kaishi ga zama mahadddacin qurani, sannan yana samun alheri a kasuwancinsa yA tsaya akan gaskiyarsa dai² gwargwado,
yana samun rufin asiri a sana’arsa
Haka bangaren matan malam uwar gidansa ta dauki mairo kaman Yar data Haifa yayinda amaryarsa takasance masifaffiya Dan bata shiga shirgin mairo tunda taga uwargidamta ta dauketa kaman ya, uwargidan malam shehu ta iya saka Dan haka ta dinga koyamata sakar kayan sanyi

A zamansu a kano mairo ta haifi yaronta na farko ya rasu a ranar da ta haifeshi yarasu bayan wani Dan lokaci ta Haifi na biyu
Suka masa sunan Usman wato sunan malam shehu, yatashi da ilimin addini da soyayyar iyayensa gashi malam shehu ya daukeshi kaman jikansa yana matukar kaunarsa da ya isa sakawa a makaranta akakai usman makarantar boko
Seda mairo ta kuma haifan yara biyu suna mutuwa sannan ta haifi Yaronta namiji akasamasa Aliyu
Addu’a Imam yayi tayi Allah ya bar masa Aliyu Usman ya samu Dan uwa,
Usman ya tashi da matukar kaunar Dan uwansa kullum yana tare dashi har Goya masa shi mairo takeyi,
Ba ‘a Dade ba
Ta kuma haifar mace itama ta rasu daga nan bata sake haihuwa ba,
Haka suka rungumi yaransu suna kula dasu malam imam be sakasu a harkar kasuwanci ba se dai ya tsaya musu akan Neman Ilimin su, na islama Dana zamani,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button