Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Ilham se safa da marwa take, a cikin dakinta, ta rasa inda maganganun Jalila suka dosa, tace ita ba son Jalal take ba, amma itama tanada kuduri akansa, kuma inyaci karo da nawa, to tabbas zata rusa nawa, koda tazo nan a tunaninta seda ta zare ido, ta rusa nawa burin saboda nata muradin, to ko ta san menene shirina ne, to amma tayaya zata sani bayan ko Nana bata saniba,
Dakko wayarta tayi, zata kira yaseera, sekuma ta fasa, dole in dau mataki, bazanyi wahalar banza tsawon shekaru ina kallo wata sakarya ta rusamin shirina ba, gara tun yanzu in rusata ita danata shirin, ta mike da sauri ta nufi dakin mummy, tana zuwa ta tura kofar dakin, ta sameta tana waya, taje kusa da ita ta zauna, tana jiranta tagama,
Seda mummy tagama waya, sannan ta kalli Ilham tace
“Ilham ya akayine, naganki wani iri haka kaman mara lafiya”
Fashewa tayi da kuka, ta fada kan cinyar mummy
“Mummy wallahi nakusa mutuwa, in har yaya Jalal be aureni ba, zan iya mutuwa, Mummy ina sonshi, dan Allah asaka ranar aurenmu,”
“Yi shiru kiyi hakuri, kinji nima naga kamatar yin hakan, kila in kika aureshi ma ya shiryu sanadin haka, yanzu kidena kuka, bari daddynku ya dawo, muga me yakamata ayi, amma karki kuma zance zaki mutu saboda shi, aini na miki alkawari, indai ina raye Jalal shine mijinki, indai nina haifeshi baze taba auren wata mace inba keba, kidena kukan nan haka ya isa”
Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Ilham tayi, tareda yin murmushi a boye, a fili kuma tace
“dan Allah mummy asaka da wuri, ina tsoron ya auri wata baniba,”
“ki kwantar da hankalinki, shi kinga alamar ma zeyi soyayya da wata, ko kina tunanin akwai wadda zata aureshi a haka, aini kingama min komai da kikeson Jalal a haka, dan haka bari daddyn sa ya dawo, zamuga yaushe yakamata asaka”
Ilham ta riko hannun mummy,
“Nagode sosai, mummy”
“bakomai, kidena kuka”
Hannah zaune akan fararen kujerun dake gurin, fuskarta dauke da wani arnen glass dayake barazanar cinye fiye da rabin fuskarta, ga barima da tasaka a akan dogon hancinta, se tauna chew gum take, tana fuskantar Jeje,
“Hanna daga gurin oga KB nake, kuma yace lallai wannan itace damarmu ta karshe akan Jalal, yazama dole muyi yadda zamuyi mukammala aikin nan,” hannah ta dan nisa ta cire glass din fuskarta, sannan tace
“Idan ban mantaba shekaru uku zuwa hudu muna aikin nan, duj wani salon makirci, da kisisina ba wanda banyi ba, tunda nafara bariki, bantaba ganin dan bala’i ba kamar Jalal, ban taba haduwa da mutum me azabar taurin kai ba kamar Jalal, babbar nasarar dana samu a rayuwa akansa shine, a labarin daka bani, bayan sauyawar Jalal, ina cikin jerin matan daya sake dasu, har yake shiga harkata, amma naiyi iya kokarina alakarmu ta wuce haka amma yaki yadda, ni yanzu bani da wata dabara,
Nagama nawa, bansan meye shirinka ba”
“Hakane Hannah, nasan kinyi mana aiki, kinyi iya yinki kinmana kokari, abaya a koda yaushe ina galaba akan sa amma yan shekarun nan, nafara ganin sauyi a tareda shi, koda nagama aikina akan Jalal, sena tabattar da nayiwa Jawwad babbar illa shima, saboda tsawon wannan shekarun shiya hana cikar burin mu, Jalal yanajin maganar Jawwad fiye data uwar data haifeshi, wadda ita ta haddasa komai, “
” Baka ganin ina aka cutar da Jawwad ba a masa adalci ba, shi meye nasa aciki “
” yana da laifi Hanna kuma dole ya karbi hukunci, yanzu ki tsaya ki saurareni”
“ina jinka”
“a gurin birthday din damuka shirya masa komai ze kare,” hannah ta kalleshi sannan tace
“bangane mekake nufi ba”
“zaki gane ne Hannah, nagama shirya komai, kinsan meze faru?”
“No seka fada”
“kamar yadda muka shirya, shabiyun dare zamu fara gabatar da taron, a cikin cake din dazamu bawa Jalal ke zakiyi wannan aikin, zaki saka kwaya, a dai2 inda za a bashi, saboda sonake ya bugu ya fita hankalinsa yadda baze iya komai ba, za sakama a lemon da zs sha, da zarar ya fita hayyacinsa zamu dauke shi, mu kaishi wani gurin, kekuma zaki gabatar da aikinki”
Dan tsaki Hannah tayi
“Ni gaskiya ba a haka naso aikin yazo ba”
“to ya za ayi se hakuri, tunda shi dan taurin kaine, zamu nuna masa munfishi iya bariki”
Wayarsa ce tafara ringing, jeje ya kalli Hannah “Dan halak shike kirana”
Tai murmushi tace
“Pick it”
Dagawa yayi yasa a hands free
“Allah ya temaki, mazaje, namijin duniya sha gwagwarmaya, namjin damusa bakason raini” Jalal yace
“Kai Jeje ya isa haka, magana nakeson yi maka akan maganar partyn nan”
“ok inajinka”
“Munyi magana da Jawwad, dan haka dole a maida shi eight Jawwad yace baya son ya kai karfe shabiyu in bahakaba baze attending ba, dan haka ina so amaida shi eight pm, saboda inason Jawwad ya kasance a gurin”
What!!!!!!! Jeje yafada da karfi yana mikewa tsaye

Share please
More Comments More typing………………………..

Akodayaushe kuna raina masoya comments dinku ke bani karfin gwiwa da sani nishadi, amma in naga ba kwa comments sosai, se inji kamar inkoma posting duk sati ????????????????????
Ina godiya da adduoi Allah yabar kauna

????️????️????️????️????️
[9/24, 8:35 PM] Ayshercool: ????????????????????????????????????????????????????????????????
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

_ABDUL  JALAL_

  _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

           PAGE-  50

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa’azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske,
Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what’s app akan wannan lambar wayar
07063065680

           _My First Novel _

Jalal yace “Lafiya naji kana wani what, ko baka gane menace bane?”
“Amma meyasa zakayi manaa haka Jalal, mun riga mungama shirya komai, sannan kace wai se a maida shi eight, haba Jalal dan Allah, dolene se Jawwad yaje gurin, mene a ciki dan munyi iyamu da abokanmu yanzu….
” Kaga Jeje ba dole ai bani na rokeku ba dama tun farko dan haka, inbazaku canza lokacin ba bazan zo ba” yana zuwa nan ya kashe wayarsa, jeje ya daki tabur ya zuba ashar,
“kingani ko Hannah wallahi dole a hukunta Jawwad, a koda yaushe shi ke bata mana shiri,”
Hannah tace
“Kaga kaifa fushi banaka bane a yanzu, ka yadda kawai, in ba hakaba wannan damar ta wuce aiki ze kuma komawa baya, gara ka kirashi kace ka yadda” , jinjina kai Jeje yayi
“Shikenan amma Jawwad seyaga abunda zanmasa”
Haka jeje ya kira Jalal, yace masa sun yadda,
Washe gari babu zato babu tsammani, Daddyn Hanan sukazo shida Abdallah, suka duba Jalila, taji dadi sosai da zuwansu, dukda ba wani dadewa sukayiba, dayake hanan gaya masa abunda yasamu Jalila, daga bauchi suka dawo suka biyo suka tsaya a kano domin dubata, Daddyn Hanan yace Insha Allah shima ta bangarensa zesa aimasa bincike game da batan Ummin, sannan yaita rarrashin Jalila tareda yimata nasiha,
Daddyn Hanan yacewa Abba
“gaskiya wataran zanzo kabani Jalila, mutafi da ita bauchi, gurin kakarsu Hanan, itama taga wannaan kamannin nasu, daga bata labarin Jalila se magiya take dan Allah akaita ta ganta, dayake ta tsufa bata iya fita aida da ita zamu taho”
Abba yace
“Allah sarki insha Allah randa kuka shirya kuzo ku kaimata ita”
“To shikenan, nagode kwarai da karamcinka Alhaji usman”
Sukayi musu sallama suka nufi kaduna
Kwanan su Abdallah biyu da zuwa, su Jalila suna cikin farin ciki, sun samu admission a BUK daga ita har Nana, ranar litinin zasu fara zuwa makaranta, Abba yayi musu nasiha sosai game da rayuwar dazasuyi a cikin Jami a, ita Nana
mass communication zatayi, itakuma Jalila catering craft zatayi, da farko Jawwad yaita mata mita akan mezatayi da wani catering duk kwakwalwarta, itakuma tace shi takeso, dan tana son harkar girke2 da sanao’in hannu.
Anata shirye2 birthday Jalal, Yanzuma Jalal ne da Jawwad a harabar gidan akan fararen kujeru, suke zancen yaya birthday din ze kasance, Jalila ta fito zata fita,
“Yaya barka da yamma”
“Yawwa baby ina zuwa haka?”
“Maama zan karbowa kaya, a jambulo”
“Bari mu tafi tare, semu ajiyeki dama fita zamuyi”
“To yaya, bari inje waje in jiraku”
Jawwad ya kalli Jalal, “Dakko motar, bari inje insaka kaya”
Jalal ya fito da motar waje, Jalila bata shiga motar ba tana tsaye a waje har Jawwad ya fito, suna shirin tafiya sega wani abokinsu Jawwad yazo wucewa, tsayawa yayi suna gaisawa, dayake tsohon abokinsune kuma sun dade basu hadu ba,
Jawwad yace “kai faruk ba a ganinka ko a gari, ina ka shige haka ne?”
Wanda aka kira da faruk yai dariya “ina nan Jawwad, makaranta ce munata fama, kasan yanzu ina ABU zaria bana zama sosai a kano, yanzuma wani filin baba mukazo gani unguwar taku, Jalal nema bana ganinsa sam” Jalal ya kalli Faruk ya danyi murmushi, sannan yace
“Nima ina nan haduwa ce dai tai wuya, ya karatun? “
“Alhamdilillah Jalal, y garin, ya karatu ko har yanzu baka koma makarantar ba” Jalila dai na tsaye jikin mota tana jinsu, Jalal yace
“Gari gamu a cikinsa, makaranta kuma bana zuwa har yanzu”
Jawwad yace, “Faruk, yana Jalal yana shirin komawa makaranta kwanan nan insha Allah”
“To Allah yasa”
Jawwad yace “au Jalal nayi mantuwa, bari inje in dakko wayata, ka karbi lambar faruk mudinga gaisawa”
Jalal yace “Ok seka fito”
Jawwad ya shiga gida, faruk ya kalli Jalal, yace “Jalal wannan kuma wacece?” jalal ya dan kalli Jalila sannan yace
“gata nan tambayeta mana”
“Hmm Jalal halinka yana nan dai” faruk ya kalli faruk “y’an mata yakike? “
“Lafiya kalau” faruk yakuma cewa “Jalal ban san wannan ba, kanwarka ce kota Jawwad, kokuma…. Jalal ya katseshi ta hanyar cewa
” kai faruk, kaima surutun nan naka yana nan da shegen son mata” dariya sosai faruk yayi, ana haka sega wata mota tazo wucewa, amma akayi parking mutumin ciki ya fito, babban mutum ne, ya tunkaro su a fusace da farko faruk be ganshiba seda gabaya, dan bude baki yayi ya zaro ido, mutumin yana zuwa ya kalli Jalal sannan ya kalli faruk,
“Kai faruku, ban hanaka kula wannan dan iskan yaron ba, danayi sa a na rabaka dashi, shine yauma kakuma lallabowa, gurinsa ko, sekaima ka lalace kamar sa, kai ko kyamarsa ma bakayi, dubeshi kana kallonsa kaga mutumin banza wuce kabar nan gurin ko in kifa maka mari, “
Faruk ya fara in ina” A a Bab… Baba, dan Allah kayi hakuri, gaisawa kawai muke
“Zaka wuce ko sena marekan, nahanaka hulda da yaron nan, inkuma kaima kafara shaye2 ne kaima se inji, ba Shiri faruk yai gaba, yana waiwayensu
Jalal dai bece komaiba ya sunkuyar da kai yai shiru, Haka nan se Jalila taji ba dadi, mussaman da Jalal ya sunkuyar da kansa bece komai ba,
Mutumin ya juyo ya kalli Jalal, ya nunashi da yatsa
“kaikuma bakai ba dana, idan nakuma ganinka dashi wallahi hukuma ce zata rabamu da kai, dana ba lalatacce bane ba kamar kai, ni dana kamiline, baze yiwu ka koyamasa shaye2 da rashin tarbiyya ba,” Jawwad ne ya kawo kai ya fito ya tarar da cin zarafin da akewa Jalal, tsayawa yai cak yana kallon ikon Allah, mutumin ya cigaba da bala’i
” ni banyi sake ďana ya lalace ba dan haka bazan bari ka lalata min shiba, niba nusarin ubane ba kamar ubanka, daya bari ka lalace kalleka, kowa ya ganka yaga dan iska mara tarbiyya sha3″ harzuka Jalal yayi, ya kura ma baban faruk ido, amma abun mamaki still Jalal yaki cewa mutumin nan uffan
“Shima baban nasa bashi ya saiwa kansa ba, kuma ba laifi yayiwa Allah ba ya jarrabeshi da fitinanne yaro ba, haba baba, a haka gaka dattijo amma aji wannaan maganganun suna fita daga bakinka, to in Allah ya doramaka ya zakayi? Akan wani dalilin zaka dinga zaginsa dan kawai ya gaisa da danka, shi Jalal din shi yaiwa kansa, ka gayamin wanda akayi shawara dashi kafin a halicceshi, ko kaddara abunda ze faru a rayuwarsa”
Gaba daya ido suka zuba mata baki bude, suna kallonta, tsagwaron bacin raine kwance a idonta, bil hakki take fadan maganganun da take, kana kallonta kasan har zuciyarta ranta ya baci, Jawwad ne yai yunkurin cewa
“Jalila meye haka, ba kya ganin babban mutum ne? Baba kayi hakuri insha Allah Jalal baze kuma…
” Wai yaya Jawwad laifin me akayi masa kake bashi hakuri, ABDUL JALAL ne ya taka kafa yaje inda dansa yake kokuma shi yakawo kansa, baba irin wannan abubuwan da akewa mutane irinsu Jalal shike kara lalatasu, yazama bame jansu a jiki, kowa se kyama da tsangwama, danka da kake fada akansa ma mutum ne, kuma baka isa ka hana Allah ikonsa akan shiba, in Allah ya jarrabeshi shima, yazakayi a ganina in bakayimasa addu a ba bekamata ka zage shi haka ba, da kake cemasa mara tarbiyya kazagi mahifinsa da ya dau mataki akanka fa, kasan a hakan nan se ya zageka tsaf bazaka iya masa komai ba, kuma kaga hakan baze maka dadi ba”
Jawwad yace na shiga uku, halin Jalila yana nan ashe, bata canza ba, shiru2 da take na kewar Ummi ne ashe, yayinda Jalal yai shiru yana satar kallonta, Jawwad yace
“Ke kiyimin shiru, meyasa kike haka, sa ankine”
Baban Faruk yace, “Kyaleta i like her confidence, kin birgeni sosai yarinya at least, kin tunamin abunda na manta, nagode sosai” ya kalli Jalal yace
“Am sorry my son, nasan na bata maka rai, kayi hakuri” yajuya ya wuce ya hau motarsa ya tafi
Jalal be taba tunanin tsiwar Jalila ta kai haka ba, babban abunda yabashi mamaki yadda ta zakakalkale haka, bayan itama rashin mutunci takemasa, juyawa tayi ta bude bayan mota ta shige abunta kamar batayi komaiba, Jawwad yacewa Jalal “taho mu tafi” ba musu Jalal ya bishi, amma Jawwad ya zauna a mazaunin direba, Jalal yana kusa dashi, Jawwad dan waigo ya kalli Jalila sannan yace
“Baby ya haka, abunda kikayi kin kyauta kenan? Babban mutum ne fa, haba baby dama baki canza ba?”
“ka taba ganin an haifi mutum da hali ace ya canza, in tsoho beji kunyar hawa jaki ba jaki baze ji kunyar kada tsohoba, a matsayinsa na babba abunda yayi ya dace kenan, kozakayiwa mutum rashin mutunci karka hada da mahifinsa, shima daganinsa kaga criminal idonsa kawai zaka kalla kasan ba mutumin kirki bane”
Shi Jawwad Jalila ta dena bashi mamaki tsoro take bashi
“Ke Jalila ya akayi kikasan criminal ne, karki kuma, baban wanine koba komai ya haifeki”
“Yaya nifa ba karya nayiba bakaji yadda yake magana ba ne? Shima wannan nusarin Jalal din yanaji ana zaginsa yai shiru, inkaga yana masifa to akan Matane, yadinga wani muzurai, matsalar mutum ya dinga abunda bashi da kyau kenan wanda ya isa da wanda be isaba sunemi suci mutuncinka”
Bude baki Jawwad yayi ya waigo yana kallonta, dama haka take, tunda ake fadar iya tsiwa na Jalila be taba tunanin ta kai nan ba, rasa bakin magana yayi, shikuwa Jalal ko motsawa beyiba daga inda yake balle ya nuna yasan dashi take, sema tunani da yayi zurfi a ciki, amma yana jin duk abunda take fada, haka motar tai tsit har sukaje jnda zasu sauketa, tace
“Yaya Jawwad ka jirani man in shiga in karbo, semu tafi bannaa son tafiya ni ka dai, kasan ban san kan garin nan ba”
“gashi kuma ba gida muka nufa ba, zamuje siyayya ne” cikin shagwaba tace ” eh naji, ko ina zakuje dai, dan Allah kujirani”
“To yi sauri karkimin kuka” tayi murmushi ta bude motar ta fita”
Jawwad ya dan kalli Jalal sannan yace
“Jalal, Jalila ba karamin mamaki ta baniba, ban taba zaton zata iya haka ba, babban mutum kaman wannan sam bata da tsoro, amma kaima bazan gaji da baka hakuri akan abubuwan datake yimaka ba, kuruciya na damunta, har yanzu yarinya ce”
“Wane kalan kaya kakeso musaka ranan, so nake muyi shiga iri daya”
“A a ya ina maka magana kaikuma kana min wani zancen daban”
“Kasan akwai kaya da daddy ya turo dasu zamuje mu duba, in bamu samu wanda mukeso ba semu siyo wasu, i wish daddy yana Nigeria zanyi birthday” Jawwad ya fuskanci Jalal rainin hankali yakeji, wato baya son wancan zancen da sukeyi, dan haka ya rabu dashi.
Bayan barin Alhaji kabiru gurin nan, ya dinga tunanin wace wannan yarinyar haka, wace ce ita, mene alakarta da Jalal haka, wayarsa ya dakko ya kira lambar Jeje, bugu biyu Jeje ya dauka,
“Allah ya temaki, oga KB”
“Jeje tambayarka zanyi”
“to Oga Allah yasa nasani”
“akwai wata yarinya danagani a gurin Jalal, ko kasan wacece dinsa”
“ya take oga?”
Ya fasalta masa siffar Jalila, jeje yace gaskiya be santa ba amm ze bincika masa.
Jalila ta fito, tazo ta bude motar ta shiga, Jawwad yace “har kinfito”
“Eh Yaya banason bata muku lokacine”
Jawwad ya kunna mota, suka hau titi, suna hirarsu da Jalal, aka jima se cewa tayi
“waimu ba za a gayyacemu bane?”
Jawwad yace “mu mun isa dole a gayyace ku mana”
“hadasu Nana, da Ilham”
“Eh mana hadasu” shidai Jalal bece uffan ba, baze so zuwan Jalila gurin nan ba dan yasan tabbas setayi surutu intaga abunda be mata ba, kuma yasan dole ayi shaye2 a gurin, meyasa Jawwad ya amsa mata suje gurin nan, a titi suka sauketa, sukuma sukayi gaba, ta dade tanajira sannan ta samu napep ta karasa gida, a palour ta tarar da Maama da Abba ta kaiwa Maama kayan, Abba yana mata sannu da zuwa, Maama ta bubbude kayan ýan kunnaye da sarka masu matukar kyau,
Jalila tace “Maama bari in daukesu a waya a tura social media, za a samu costumers tunda new design ne” dayake a gaban Abba ne se Maama ta sakar mata fuska,
“eh hakan yayi kyau, in anjima dan Allah ki mikawa mummy, dama saboda ita nasa aka karbosu tacemin ana so”
“to shikenan bari inyi salla” harta mike zata tafi, Abba ya kirata ta dawo
Yace “daukar muku, keda Nana kowa biyu, se a gayamin kudin”
“to Abba mungode Allah yasaka da Alkhairi, Allah yasa afi haka”
“Ameen ya Allah, Allah yayi Albarka” Jalila ta tashi ta tafi dakinsu, yauma Nana bat nan, Jalila tayi salla taci Abinci, ta kwanta tana hutawa, ta dau wayarta tana ta tura kayan nan social media a haka har bacci ya dauketa
Jawwad sun sha yawo, shida Jalal se kusan la’asar sannan suka dawo sun gaji matuka, sallar la’asar sukayi, sannan Jawwad ya kira Jalila a waya yace dan Allah akai musu Abinci, ji tai kamar tace A a saboda batason yawan zuwa inda yake tunda mahaifiyarsa bata so, amma Nana bata nan Halima ma haka, badan haka ba da bazataje ba,
“to Yaya gani nan zuwa, bari in kawo”
“to shikenan muna jira”
Jawwad ya kalli JALAL, bari in shiga in dan watsa ruwa kafin ta kawo abincin” Jalal yace
“to kifi, sarkin ruwa seka fito” befi 3min da tafiyar Jawwad wanka ba Jalila ta shigo da kayan Abinci, tai sallama amma Jalal ya mata banza dama bata sa ran ze amsa ba, ta ajiye Abincin, harta juya zata fita taji muryarsa
“Ke zo nan” kutmelesi wai ke, juyowa tayi da niyyar yi masa rashin mutunci, kawai taga yamata wani mugun kwarjini, gashi ya kafeta da ido,
“gani mene?” tazo kansa ta tsaya tana zumbura baki, hannayenta ya janyo da karfi seda ta durkusa akan gwiwoyinta, seda ta danyi kara ta dago ta kalleshi tareda fizge hannunta, saboda taji zafi
“Idan na kuma kiranki, kikatsaya min aka, kamar itace sena miki abunda zaki karye, mara kunya kawai” kallon up and down ta masa ta dauke kanta
“Ubanwa kike cewa nusari dazu, wait tukuna ma, uban wayasa kiyiwa mutumin nan rashin kunya, ke yayiwa koni, meye alakarki dani da zakiyi wa babban mutum kamar wannan rashin kunya, inkinyi dan ki birgeni ne, to baki birgeba dan JALAL bayasin shishshigi”
Murmushi Jalila tayi wanda yai matukar yi mata kyau, “wayace maka saboda kai nayi, aini birgeni yayi da yayi maka haka, kasan wanda yasan darajar dambu shike zuba masa mai, duk inda naji ana cin mutuncin iyaye koba nawa bane raina baci yakeyi, saboda karya zarce da zagin daddy shiyasa nai magana domin dakatar dashi, ba wai dan kai ba, kwakwalwarka ta dinga lissafa maka dai2 mana” kuramata ido yayi baya ko kiftawa, sekuma yayi dariya
“Karya kikeyi, idonki ya nuna abunda kike fada a yanzu karyace kawai,
Sekuma ya hade rai
” Zan miki wani kashedi, idan kika kuskura kikazo gurin birthday na duk abunda yasameki kekika jiyowa kanki, danban gayyaceki ba, tashi kbmibani guri, mummuna uwar magana kawai” mikewa tayi ta danyi gaba sannan ta waigo ta kalleshi
“wallahi senaje, ai ba dan kai zaniba, saboda yaya Jawwad zani, tunda shi yace inje, dayake abun na rashin gaskiyane shine wai ba a gayyaceniba, to wallahi senaje, inyaso in naje a dakeni, ragon maza kawai nusari.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button