Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

“Wait please meye kuma namin fada kibarni in tsara rayuwata yadda nakeso ba ruwanki da abinda nake aikatawa makaranta ko inje ko kar inje ai bada kudinki ake biyaminba duk kin takuramin kin tsaneni ni am doubting ma if u are my biological mother ????????????

“Allah wadaran naka ya lalace tur da Dan daze tsaya gaban mahaifiyarsa tana fada yana mayarwa,
Anya kana Neman albarka a rayuwarka asara ta tabbata ga me sabawa iyayensa
Gaba daya suka waigo domin ganin me maganar……..

More comments more typing

????️????️????️????️????️
[8/31, 8:26 AM] Safiyya: ????????????????????????????????????????????????????????????????????

_ABDUL  JALAL_

  _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

           PAGE-  3

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa’azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

   _My first novel_

Gaba daya suka waigo suna kallon inda jalila take maganar, taci gaba da fadin
“duk d’a nagari me fatan nasara a rayuwarsa, baya fad’i in fad’a da mahaifiyarsa wannan ba halin d’a nagari bane me neman albarka,
wannan ba komaibane kake face tsantsar rashin tarbiyya!!”
ta kare maganar tana kallon cikin idon jalal,
ta kalli mummyn Jalal tace “mummy seda safe Nana ta taho da sakon”

  Idanuwansa ne sukayi jawur jijiyar kansa ta daddaga ganin yarinya Karama ta tsaya tana gaya masa miyagun maganganu, 
Wani yunkuri yayi da nufi ya karasa inda jalila take ya hukunta ta

mummy tasha gabansa ta rikeshi gam, duk da ta danji ba dadi da Jalila takira Jalal Mara tarbiyya amma ta dake tare da fadin

“Karka kuskura ka tabata abinda tafada gaskiya tafada kadan kagani Indai haka zakacigaba dayiwa rayuwarka, indai zaka cigaba da gayamin maganganunu daka gadama kana wuakantani agaban mutane.”

fizge hannunsa yayi da karfi
“kicikani wallahi sena kakkarya yarinyar nan ni zata gayawa wannan maganganun wallahi sena koyamata darasin da harta mutu bazata mantaba,”
Da gudu jalila ta ruga ta fice daga palourn.

hannunsa ya fizge daga cikin na mummy ya rufa mata baya a zuciye, amma kash kafin ya fito harta bace kaman walkiya yanemeta yarasa, har bakin gate yafito amma be ganta ba, yanufi dakin me gadi Yakama buga masa kofa iya karfinsa,
a sukwane me gadi ya fito babban mutum amma haka ya zube agaban jalal jiki na bari “ranka ya dade….” Begama ba JALAL ya katseshi

“kaii yarinyar da ta fita yanzu INA tayi,” jalal ya katseshi

“Ranka ya dade sallah nakeyi banga fitar kowa ba”
” shut up!!! Useless man Sam bakasan aikinkaba dakiki kawai,”

A fusace ya shiga part dinsa zuciyarsa na tafasa, he wish Yakama yarinyar nan da ya nuna mata waye jalal,
‘me yasa kika rikeni kika hanani daukar mataki akanta yafada a fili Dan karamin flower base din dake kan side bed dinsa ya dauka yayi jifa dashi yana huci,

“Waima Yar uban waye daga ina take”
Kaman yataba ganinta amma yamanta a ina ne

wayarsa CE tafara ringing, bros jawwad ne yafito akan screen din wayarsa, yadaga wayar yakara a kunnensa, “
“Dan uwana meyasameka tun dazu nake nemanka kazo ka karbi ajiyarka,
Wai yanaji kanata hucine me yafarune,”
“bari bros bakomai zan fitane inna dawo zamuyi magana wata Yar iskar yarinyace ta zageni kuma idona idonta sena lahira yafita jin dadi” JALAL yayi maganar a hasale,

“Subhanallah haba Dan uwana ya kake fadin haka kaifa me hakurine fushi banakabane nasan maybe wani Abun kayi mataa kamanta da ita kawai yanzu dai kana ina”

“Bazan mantaba din wallahi sena koya mata hankali” cewar JALAL

“Easy bross karkayi fushi Manzon Allah salallahu”

“………..alaihi wassalam” Jalal yakarasa masa, “zaka fara Toni fita zanyi semun hadu da anyi magana sekace mutum yayi hakuri ka dauka kowa irin Kane”

“Dan uwana ina maka nasiha kaji tsoron Allah Dan an bata maka rai kar in kafita kasha giya Dan Allah kar kasha giya koka aikata abinda ba shikenanba babu abinda zata qara maka se bacin rai,
garaka… ..”

kitt JALAL ya kashe wayar in yatsaya cigaba da sauraron JAWWAD ze kuma bata masa rai,

Lamabar Jeje ya nemo bugu biyu ya dauka ya kara wayar a kunnensa
“Man where are u now?” Banji me akace daga daya bangarenba
“OK I will be there”
Ya kashe wayar yafice daga gidan

Da gudu ta karasa cikin gidan sukayi karo da Abba a hanyar shiga gidan tanata haki kaman tayi wrestling,
“Meyakoromin ke haka diya tagari”
“Am..mmm… Maama CE ta aikemu shine nayo gaba wani kare yabiyoni tafada tana maida numfashi”

“Shine kike wannan gudun in kika fadi fa matsoraciya kawai ba a yiwa kare gudu inbahakaba wataran seya cijeki” yafada cikin wasa
“Tunda kin shigo Gida seki tafi a hankali”
“To nadena abbana”
“Good girl, kodayake yanzu tazama lady”
Murmushi tayi tashige ciki kai tsaye ta tafi dakinsu tana kuma sauke numfashi

“Tab daya kamani dana gane kuskurena yadda idonsa yayi ze iya sumar dani fa”
Tayi maganar a zuciyarta
wayarta ta laluba tafara trying lambar Ummi amma taki shiga har tagaji ta aje wayar,
ta mike tashiga bandaki tayo Alwala tafara gabatar da sallar isha’i ta idar da sallah ta canza kaya zuwa na bacci ta nashirin kwanciya Sega Nana tashigo

“Se yanzu?”
“Eh nai ta zaman jiranki baki dawoba nagaji shine na karbi sakon na taho, dama atamfofine maama zata Cuba”
“Hmm yayi kyau” cewar Jalila.

Can na hango shi yana zaune kan wasu fararen kujeru matasa ne maza da mata suke kaiwa suna komowa daganinsu kaga yayan Hutu masu karancin tarbiyya,
fuskar nan tasa a tsuke kansa dauke da wani irin aski ga Suma fal akansa se cika yake yana batsewa da anjima yadan ja tsaki.

“Man what’s actually wrong with u tun dazu bakacemin komai ba what’s happening”

Jalal ya danja karamin tsaki kawai se yakasa gayawa jeje abinda yabata masa rai

“Just forget”
Shine abinda ya iya cewa ransa fal takaici
“Anyway since u decide not to share ur problem with me Dan ja kaya at least it will help u reduce ur temper”

Ya fada tare da tsiyaya masa Wayne a cup ya mikamasa ya Sa hannu ya dauka ya shanye ya kara masa yakuma shanyewa yana shirin kuma zuba masane

“DAN UWANA KAJI TSORON ALLAH DUK INDA ZAKAJE KAR KASHA GIYA KO KA AIKATA ABU MARA KYAU BA ABUNDA ZATA KARA MAKA SE BACIN RAI”

Kalaman Jawwad ne suke dawo masa se yaji haka nan jikinsa ya danyi sanyi.

Hannu yadagawa jeje yacemasa”enough “
“Kana nufin ta isheka” cewar jeje”
“Yeah” yafada a takaice

“Am going ” Jalal yafada yana duba agogon hannunsa
“But man kaman akwai abunda yake damunka”

“Bakomai ni na wuce Gida”
Yafice daga gurin.

“Nana dakika baro gidansu jalal kinganshi kafin kifito”

“Aa nadai ji fitarsa a mota amma bamu hadu ba, akwai matsala ne”
“Aa babu koma”.


Washegari da safe Jawwad ya shiga gidansu Jalal, seda ya shiga suka gaisa da mummyn jalal sannan ya fito ya nufi sashen Jalal,.
Kofar bedroom dinsa ya bude ya shiga yana kwance yanata bacci, agogo Jawwad ya kalla 9:30am amma Jalal be tashiba, girgiza kai yayi.

Ya taba Jalal ” bross wake up gari ya waye fa kalli rana tayi sosai “

Dan motsawa yayi kaman baze tashi ba, sannan ya tashi zaune yayi mika yana Dan yatsina fuska

“Jalal anya kayi salla kuwa?”
“Banyi ba”
yafada hankalinsa kwance
“Haba Jalal sekace ba musulmi ba quarter to 10 fa amma bakayi sallar asuba ba why?”

“In kai zanyiwa innayi kar ka karba” yafada yana shirin mikewa

“No am sorry jekayi sallar kazo muyi breakfast”
Yafita yakoma palour yana jiransa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button