Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Share please
More Comments More Typing…………………………

????️ ????️ ????️ ????️ ????️
????[9/26, 8:49 PM] Ayshercool: ????????????????????????????????????????????????????????????????????
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

_ABDUL  JALAL_

  _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

           PAGE-  51

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa’azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske,
Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what’s app akan wannan lambar wayar
07063065680

           _My First Novel _

Tana gama fadin haka ta juya tai tafiyarta, dan girgiza kai Jalal yayi, ya cigaba da danna wayarsa, Jalila na komawa taga Maama tafito daga kitchen “Ke daga ina kike?” “Yaya Jawwad ne ya kirani yace in kaimasa Abinci” tsaki Maama tayi sannan tace “inkinyi sallar magariba, ki mikawa Mummy kayan nan” “to zan kaimata Insha Allah” Maama ta wuce, Jalila kuma ta shige dakinsu tana zuwa ta tarar Nana ta dawo, “Nana Ashe kin dawo, sarkin kawaye” “bawani sarkin kawaye, zumunci dai”
“hhh to naji, ya kika baro su” “suna lafiya amma naso tare mukaje, ke kullum kina gida” “ai bayan tafiyarki nima na dan fita Maama ta aikeni” “inyee kinfara gane gari” “sosai makuwa” sukayi dariya sannan Jalila tace “Nana wai ranar Saturday za ayi birthday din Jalal” “Are you serious, ya akayi kika sani?”
“Yaya Jawwad ne yagayamin”
“Amma ya haka duk shekara tare sukeyi fa” “nima bansaniba, guri zasu kama amma muma zamuje”
“dan Allah ai basu gayyacemu ba”
“Injiwa Yaya yace zamuje muma”
“kai amma naji dadi Jalila dama an kwana biyu banfita wani outing ba”
“Haka kika iya sarkin yawo”
Bayan Jawwad sun gama cin Abinci suka fito suna hira, a harabar gidansu Jalal suka koma suna basket ball, se magariba suka bar gurin, bayan sallar magariba Jawwad yacewa Jalal, yazo suje gurin Mummy “muje muyi mata me?” “yakamata dai muje kwana biyu ban ganta ba bamu gaisa ba” “kaje kai kadai mana, ba dolene se naje ba” “Jalal ba shawararka nake nema ba, ka tashi mu tafi” Ganinda Jalal yai Jawwad ya hade rai sosai, shiyasa shi mikewa, “tashi muje” Jawwad ya tashi suka tafi cikin gidansu Jalal, Jalal ne a gaba Jawwad yana binsa, Ilham ce kadai a palourn kwance akan three seater tana daddanna wayarta, mikewa zaune tayi tareda fadin “sannunku da zuwa” Jawwad ne ya amsamata, “yawwa Ilham, ina Mummy ne?” “tana dakinta, inaga salla takeyi bari inje in kirata” ta mike ta nufi part din Mummy, Jalal dai se cika yake yana batsewa sekace wanda akayiwa wani laifi, ba a dadeba sega mummy ta fito, Ilham na bayanta, ta karaso ta nemi guri ta zauna a palourn, dan risinawa Jawwad yayi “Mummy ina wuni” “lafiya kalau Jawwad kwana biyu ya gida, yasu Maaman”
“tana lafiya” “Kwana biyu bamu hadu da ita ba, ina jira zata aikomin da kaya” “eh dazu naga an karbo, amma zata aikomiki ne” “Yayi kyau” shidai Jalal bece uffan ba, sema mike kafarsa da yayi ya kashingida, Jawwad yace “Mummy ranar Saturday yakama birthday din Jalal fa” “ina sane Jawwad, wannan karon ba tare zakuyi ba” “eh mummy, nashi zamu farayi tukuna, nace bari agaya miki” “Assalamu Alaikum” gaba daya suka amsa sallamar tareda waigawa, ko be juyoba yasan muryar Jalila ce, karasowa tayi cikin yanga, ta kalli Jawwad tai masa murmushi sannan ta durkusa kasa tace “Mummy ina wuni” “lafiya kalau ‘yan mata kwana biyu, kin buya bana ganinki” murmushi Jalila ta kumayi “ina nan Mummy bana fitane kawai” “amma baki da lafiya ne, naga kin rame haka?” Jawwad yace Mummy ta danyi rashin lafiya kam””Allah sarki ba labari, Allah ya sawwake” suka amsa da Ameen banda Jalal da Ilham dan tunda ta shigo Ilham ke mata kallon banza
Mummy tace “Jalila yi hakuri bari in dan saki aiki, jeki dakina akwai drowern mirror dina akwai, key ki dauka ki bude wardrobe dina, zaki ga akwai wani kit kibude ki dakko kudin ciki
Ilham seda ta kalli Mummy dan sam Mummy bata sata harkar kudinta, amma yau ta tura Jalila har bedroom dinta ta dakko kudi, seda Jalila tayi Jim kaman bazata ba sannan ta mike, ta nufi dakin Mummy,
“Yawwa Jawwad ina jinka, yi hakuri na tsaya surutu” “bakomai Mummy dama cewa nayi, ko zaki halacci gurin birthday din nasa” Jalal ne ya dago da sauri yana wa Jawwad wani mugun kallo, shikuma ya dauke kai kaman besan me yake ba, murmushi Mummy tayi “waceni Jawwad, Allah ya temaka, ya raya Jalal sannan ya shiryamin shi”
Koda Jalila tashiga taga part din Mummy ma ya tsaru, katon palour ne, me dauke da kayan alatu, se tangamemen kofar bedroom dinta, ya tsaru matuka, kaikace a kasar wajene, Jalila ta nutsu ta dau abunda aka sata ta fito.
Jawwad ya gyara zama sannan yace “Mummy in bazakije ba ga Ilham, ko yan uwa ai yakamata sumana kara suyi attending” Jalal ji yake kaman ya make Jawwad, shi bayason gayyar surutu, amma Jawwad se gayyato masa tarkace yake Ilham tace “Jawwad aini ko ba ku gayyaceni ba zuwana gurin birthday din yayana dolene, dan haka zanje nida kawayena” wani uban tsaki Jalal yayi, duk suka juyo suka kalleshi, Mummy tace “kagani ko Jawwad, nikam Allah yakawo silar shiryuwar Jalal, yanzu a haka kake tunanin inyi attending gurin birthday dinsa, ya dizgani a gaban abokansa, Sam baya ganina da mutunci”
Ai kuwa Jalal a fusace yace “kagani, nidama bance tazo gurin birthday na ba, seda nace bazanzo ba amma ka janyoni kaga har zata faramin korafi sek……. Sekuma sukaji yayi shiru, ya koma ya kashingida, fitowar Jalila taji Jalal yana wannan masifar suka hada ido, ta girgiza masa kai, alamar ya dena, shine abunda yasashi yin shiru, yakoma ya kashingida, duk abun nan ba wanda ya lura dame ya faru se Ilham, wadda taji kaman an dakko dutse an sakamata a zuciyarta.
Jalila ta karaso ta durkusa tabawa mummy kudin, Mummy tace “tafi dasu, kibawa Maama kice kudin wancan kayanne, ban mata transfer bane saboda wayata, ta dan samu matsala” “to zan gaya mata Insha Allah, seda safenku” Jawwad yace “bazaki jirani ba” “a a yaya, seka taho”
Ilham ce tafara mikewa ta tafi dakinta, sannan Jalal, shima tashi yayi ya bar dakin, dan Jawwad yagama bata masa rai, Jawwad kuma ya tsaya, yaita rarrashin Mummy kan halayen Jalal, sannan yai mata sallama ya tafi.
Koda Ilham ta koma dakinta ji tayi kaman ta dora hannu akanta ta fasa ihu, wannan wace irin masifa ce, tunda take a gidan nan, mummy bata shigar da ita cikin sha anin kudinta, amma yau da kanta ta tura Jalila kan kudinta, kuma karewar abun takaici wai hartayiwa Jalal signa ta hanashi abu, kuma ya hanu, lallai akwai sauran aiki, meyasa wannan yarinyar ta shigo rayuwarmu tayi kane2 haka, me yakamata inyine, kozan yi yawo tsirara se burin mahaifiyata ya cika, amma ta yaya? Wata zuciyar ta tambayeta, shiru tayi zuwa can kuma tayi wani irin shu’umin murmushi, tareda jinjina kai, “muje zuwa, Jalila kin tara kin samu, senayi sanadiyar da mujiya seta fiki farinjini a cikin al umma”
A satin ranar Monday su Jalila suka fara zuwa makaranta, Abba ya daukar musu driver saboda Kar a dorawa Jawwad nauyi dayawa shima ga nasa karatun, Jalila taji dadin fara zuwa makaranta, in ka ganta kai kace irin salihar nan ce, dan ko magana batayi sosai, wanda yana cikin halin Jalila in taje guri seta karanci kowa tsaf sannan zaka san wacece, ko magana bata fiyeyi ba, sannan bata yadda tayi kawa ba har yanzu, a satin nan tunda tafara zuwa hijjabi take sakawa har kasa, se farin glass, yauma uban dogon hijjabinta dark blue har kasa ne a jikinta, se jakarta data rataya, sunfito daga lectures tana jikin wata bishiya inda suke haduwa da Nana, taji wasu suna zundenta wai ga ustazan jami a, gigin secondary ne ta shigo a ustaziyya kafin afita kuma anyi clean, irinsune mugayen tantiran makaranta in suka waye, itakam ko ta kansu batabiba, dan ko kallo basu isheta ba, a ranta tace “kucigaba karku fasa, ku bari in zama yar gari, zaku gane baku da wayo dan ba ruwana da wata jami a, mutun yayimin senayi masa, but now kuci karenku babu babbaka” tana tsaye nan Nana ta karaso, suka nufi motarsu, a hankali Jalila take gane halin yan ajinnasu, da yaran masu kudi, dana talakawa masu dorawa kansu karya, yan rainin hankalin lecturers, da masu iyayi, kowa tana ankare da halinsa, tana ganesu, amma still ba ruwanta da kowa, wasu suyi gulmarta a gabanta wasu a bayan idonta, seta nuna musu ita magana ma abun wahala ce a gurinta,
Nana kam hartayi kawaye daga zuwanta, yayinda dabi un Jalila suka tafi da imanin kawayen Nana, ta iya gayu maganarta kawai abun burgewa ce balle tafiyarta da sauran
mu amalarta, sedai suna mata kallon me girman kai, saboda gani suke kaman wulakanci take musu, inba Nana ba bata kulasu, dan ta yanayin shiga da mu amala tana iya gane, mutanen banza dana kirki, Jalila kenan me abubuwan ban mamaki

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button