Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Jawwad ya dakawa Jalila tsawa abunda be tabayiba

Share please
More comments more typing………………………..

????️????️????️????️????️
????????[9/23, 10:27 AM] +234 802 426 7634: ????????????????????????????????????????????????????????
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

_ABDUL  JALAL_

  _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

           PAGE-  47

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa’azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

A har kullum ina jinjina da godiya ga masoya wannan novel nawa, comments dinku da addu oinku ina jin dainsu matuka, ina godiya kwarai dagaske,
Domin sharhi, gyara, kokuma shawara a nemeni ta what’s app akan wannan lambar wayar
07063065680
Ina godiya matuka Allah yabar kauna

   _My first novel_

Mamakine yakama Jalila jin yadda Jawwad ya mata tsawa, abunda betaba yi mataba,
“Jalila meyasa kike haka, na sha gayamiki Jalal ma kamanni yake agurinki yayanki ne shima”
Dauke kanta Jalila tayi, ta cigaba da zubar da hawaye, Jalal juyawa yayi ya fita yabar dakin, Jawwad ya bi bayansa
“Jalal dan Allah kayi hakuri, rashin fahimta ne tsakaninka da Jalila amma bazata karaba, yanzuma tana cikin damuwane shiyasa”
Murmushi Jalal yayi “Never mind dan uwana, nima ba fushi nayi ba, Allah yakara sauki” daga haka ya nufi motarsa ya shige, sam Jawwad beji dadin abunda Jalilan tayiba bata kyauta ba, be kamata ace tagayawa Jalal wannan maganar ba dukda basa jituwa, yasan ba danshiba babu wanda ya isa yagaya masa wannan maganar ya kyale,
Ya juya ya koma cikin Asibiti, yaje ya tarar da Still Jalila tana kuka, tana surutai akan Ummi, Halima nata bata hakuri, bebi takanta ba, ya kwashi wayoyinsa ya kwasa ya fice daga dakin.
Ana idar da sallar magariba Abba yazo, yaji dadin ganin Jalila, ta farfado ta fara samun sauki, sedai tarame sosai, ta danyi duhu, shima Abban haka ta dinga masa kuka, tana surutai, ita ummi,
Abba ya shiga yi mata nasiha me ratsa jiki
“Jalila ki karbi kaddararki a duk yadda tazo miki, nima inata kokarin inga munsamu inda take amma abun ya gagara, inkika mika al amuranki ga Allah komai zezo da sauki, jikina yana bani har yanzu tana raye, kuma zata dawo, karki cutar da kanki da wannan kukan da kikeyi, “
Abba ya kalleta sannan ya kira sunanta” Jalila”
“Na am Abba”
Ya cigaba da cewa “nidin nan ma misaline a gurinki, ba uwa ba uba, ba danuwana, gashi bamu da wasu dangi nakusa kona nesa, nasan bazaki rasa sanin tarihinmu ba nida mahifinki a gurin umminkiba, mu biyune kawai a gurin iyayenmu, kuma suma ba yan garin nan bane, gudun hijira sukayo, a yanzu haka bani da kowa, daga Allah seku ya’yana, ku nake kallo inji dadi, lokacin da nake kan ganiyar bukatar kulawar dangina, Allah ya karbesu gaba daya, amma hakan be hanani rayuwa ba, dukda har yanzu inata fafutuka ko Allah zesa insamu wani daga cikin danginmu,
Dan haka ki kwantar da hankalinki, kinada Allah kuma ni mahaifine a gurinki, duk rintsi duk wuya, babu abunda zesa in juya miki baya, ko Ummi na nan kobata nan, ina kaunarki yata ce ke jinin dan uwana, kicigaba da addu’a ki kwantar da hankalinki, kinji yarinyar kirki, zuciyata na shiga kunci idan naga hawayen marainiyar nan kuma amanar Aliyu, bana son zubar hawayenki, kiyi hakuri duk lokacin da kike kuka ji nake kaman naci amanane, “
Sosai nasihar Abba ta ratsa zuciyar Jalila, wanda yasa jikinta yin sanyi matuka ga kuma tausayinsa daya kamata
“insha Allah, Abba zan cigaba da addu’a in tana raye Allah yasa tana hannu nagari, inta rasu kuma Allah ya………. Kawai seta fashe da kuka
Sosai tausayinta ya kama Abba, Halima dake gefe ma kuka take, Jawwad ma ji yayi kaman ya tayata
Abba yace” tana rayema Insha Allah, kuma zamu gano inda take “
Gyada masa kai tayi, Jawwad yace
“Abba Maama tazo dazu ta dubata”
“yayi kyau” shine kawai abunda Abba ya fada, ya tashi ya tafi, bayan tafiyar Abba, Jawwad ma barin dakin yayi, yaje office din doctor Salis, bayan sun gaisa, Jawwad yake tambayarsa yaushe ze sallami Jalila
“se ta dan kara hutawa, nan da ko kwana biyune, tana bukatar kulawa, saboda abunda ze iya biyo baya, amma nan da kwana biyu ze sallameta Insha Allah” daga haka sukayi sallama ya fito, Jawwad koda ya fito bekoma gurin Jalila ba ya tafi gida, seda akayi sallar isha’i sannan ya dauki Nana ya kaita Asibiti, daya kaita ma a gate ya tsaya ta sauka ya juya, Nana tayi murna ganin Jikin Jalila da sauki, hira Nana take tayi mata amma tayi shiru, zuciyarta duk babu dadi, dakewa kawai takeyi,
“Nana ina yaya Jawwad”?
“Ai yana ajiyeni ya juya, inaga ko wani gurin zashi” Jalila ta dan jinjina kai,

Jalal kwance a dakinsa ya kurawa ceiling ido, dagani yayi zurfi sosai cikin tunani, dan lumshe ido yayi, tareda yin Ajiyar zuciya, kirjinsa yamasa nauyi matuka, ya mike zaune ya dafe kansa da hannunsa biyu, sallama tayi a palournsa, yai shiru be amsa ba, ta karaso da tray a hannunta ta nemi guri ta zauna a kusa da shi, hannunta biyu ta saka ta cire masa tagumin
“Yaya Jalal meyake damunka tagumi fa babu kyau” dan kurawa Ilham ido yayi ya dauke kansa
“Yaya kayimin magana mana, naganka wani iri”
“Me kikazo yimin nan?”
“Fruit na kawo maka, kuma naga kwana biyu baka zama a gida, kwana uku banganka ba, duk na damu, ko cikin gida baka lekamu”
“Inkingama ki tashi kibani guri”
“Haba yaya Jalal, in damu da kai har inzo inda kake amma ka koreni, please yaya Jalal kabani dama mana a rayuwa, wallahi I love you Yayana, please marry me, in ba kaiba rayuwata tana cikin hatsari ina bukatar kulawarka, bazan iya auren wani ba kaiba”
“Idan kika bari na kuma yi miki maganar ki barmun dakina, sena miki abunda baki taba zatoba, sha3 mahaukaciya kawai” daga haka ya tashi yabar palourn ya shige bedroom dinsa,
Mutuwar zaune tayi, gaba daya notin kanta ya kwance tarasa mezatayi, ita namiji yake wulakantawa haka, dole tanemi mafita, Jalal yafara kaita bango matuka, tana cikin nazarinne wayar Jalal daya bari a hannun kujera tafara ringing, amma setaga lambace ba suna, hannu ta kai ta daga wayar tasaka a kunnenta, da dagawarta taji muryar mace tafara magana
“Haba my Jalal, kwana na uku ban ganka ba, ban saka a idona ba duk na damu, gashi baka daga wayata ina ka shigane, I want surprise you”
Ran Ilham ne ya baci, dan haka cikin masifa tace “Ke dalla Malama dakata mahaukaciya, dabbar inace ke, to Wallahi bari kiji in gaya miki, ko ke kika kaso maita duniya bakisa ki auri Jalal ba, Jalal nawane ni kadai, inbiki kiyayeni ba wallahi se kinyi danasanin zuwanki duniya, gara tun wuri kisan inda dare yai miki, Jalal bashi da wata mata in ba niba, munafukar banza data wofi, maci amana”
Hannah tace
“Ke saurara Me kike da suna, karki kuskura kice zaki zageni, bani da lokacin ki, haduwarmu ta farko kin gayamin magana son ranki, na kyaleki, bani da lokacinki, kuma idan ina raye Wallahi karya kike kema ki auri Jalal muzuba nidake, dan halak ka fasa, sokuwa kawai”
Jin hargowar Ilham ne yasa JALAL fitowa daga bedroom dinsa, yana zuwa ya tarar da Ilham rike da wayarsa tanata bala’i da surutai, karasawa inda take yayi, yasa hannu ya karbe wayarsa, ya juya ya nufi dakinsa, mikewa Ilham tayi tabi bayan Jalal tana masifa, a kunnensa ya kara wayar
“Ya akayi?”
“haba Jalal, meyasa kanwarka mahaukaciya ce, toka gayamata idan a wancan lokacin mun hadu ta zageni na kyaleta ta kiyayeni(a zatonta Jalila ce Ilham) , kasan halina zan mata rashin mutunci, kuma ka gaggauta gaya mata, nida ita shege kafasa”
“meyasa ke baki gaya mata ba”?
“Hakama zaka ce? Shikenan Jalal, ina ta wahala akanka, amma wata tana cimin mutunci ko, shikenan zatasan wata zaga wallahi, kasani duk me shirin kawomin matsala tsakanina da kai, sena gwada masa ni a mata ta dabance”
“Look Hannah bana son shirme kaina kemin ciwo, kuje kuyi tayi, tunda daga ke har ita baku da hankali, banzaye kawai”
Hannah kuma Ilham ta faada a hankali ba Jalila ba, wace kuma hannah, inma rainamin hankali suke, zasuga tsiya, yana gama wayar ya ajiyeta, wannan jarababbun sun kara hargitsa masa lissafi ransa a matukar bace yake, ya balle rigarsa ya aje kan gado ya juyo, yaga still Ilham tana tsaye, tana huci
“Meye haka ina cire kaya kinzo kin sani gaba, malama ki wuce ki bani guri, bana son shirme ds hauka”
“Wallahi Yaya Jalal, bazaka tabbatar da nayi hauka ba se ranar dana fara yimaka haukan, ni kake cewa mahaukaciya ko?…….
Tinkarota yayi gadan2 ta juya da gudu ta fice, dan data bari ya karaso ta san sauran, amma shi a gurinsa yayine dan ya tsorata ta, saboda tun ranar da Jalila tace masa ragon namiji shike dukan mata, be kara dukan Ilham ba, sedai yayi mata tsawa, shiyasa tasamu damar kara yi masa shishshigi, tana juyawa ta tafi, ya dawo ya zauna yai shiru, sun kara dagula masa lissafi, ga maganganun Jalila sun tsaya masa a rai, daga baya yaga bashi da mafita, ya tashi ya dakko mutuniyar tasa, yaiwa kansa caji ya kwanta anan, yafara bacci.
Jalila ta fuskanci Jawwad fushi yake, a lokacin itama taga rashin dacewar abunda tayi amma ba yadda zatayi, itama bata san tayiba, tana cikin dimuwane, shikuma yasata gaba da jaraba, tana wannan tunanin bacci yai awon gaba da ita

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button