Uncategorized

ABDUL JALAL PART 1 HAUSA NOVEL

Mikewa yayi yayo wanka tareda alwala yazo yayi salla itama dai sallar gata nan wata kilama badan Jawwad yazoba bazeyi ba,

(Sallar karfe 10am Jalal kai lefunka naka sunyi yawa Allah ya yafe mana)
Bayan ya idar ne yafito ya tarar da Jawad a palour yasamu guri ya zauna a kujerar datake fuskantar Jawad

Jawad yayi gyaran murya yace “Jalal wai me akayi maka jiyane meyafaru”
Yayi shiru kaman ba zece komai ba

“Wata yarinya CE jiya da daddare ina magana da mummy kawai ta fito ta tsoma baki hadace min Mara tarbiyya”

Dan zaro ido Jawwad yayi aransa yace ai batayi karyaba abokina watakila ma rashin mutuncin kakewa mahaifiyarka agaban mutane amma a fili seyace
“Wace yarinyar CE”

“Toni ina nasanta naga dai kaman na taba ganinta amma namanta inda nasanta,
Amma tabbas duk ranar dana ganta sena mata abinda bazata manta dani ba zan tabbatar mata bani da tarbiyya sha³ yarinya”

“Yi hakuri bros yanzu taso muje gidanmu muci abinci tunda yanzu dai baka ganta ba kamanta kacigaba da harkokinka kawai”
Ya janyo hannunsa suka fita daga gidan, zuwa gidan su

Bayan sun kammala cin abincin ne Jawwad yayi gyaran murya yace
“mutumina Jalilana fa tazo yau kwananta hudu a kano”

“Wace hakan?” Jalal yafada cikin ko in kula
” kaifa kafiye wulakanci kanwata fa danake gayamaka ta Kaduna”

Murmushi Jalal yayi “to shine kake wannan fara ar haka?”
“Bazaka ganeba Jalal irin yadda nakesonta, ba iya son yan uwantaka nake mata ba Jalal ina kaunarta ne sonake in kasance tare da ita har karshen rayuwata ganinta kawai yana Sani farinciki Ina kaunar Jalila matuka zan iya komai akan farin cikinta”

Kyakyacewa Jalal yayi da dariya tare da kunna sigarinsa ya fesa hayakin sama tare da wani kasaitaccen murmushi,
“Gaskiya ka faller over bross irin wannan bege haka ina mamakin me akeji a soyayya ni har yanzu banga macen dazata Sani wannan sambatun ba”
ya karashe maganar da wata irin,
dariya
“Jalal irinkune soyayya bata muku ta dadi wato dariyama nabaka ko hmm rai dai Allah yabamu rai da lafiya”

“Yaya Jawwad barka da Sadiya INA fatan katashi lafiya, Abba yace kazo yanason ganinka,”

Daram kirjin Jalal ya buga muryarta ce!!,

“Yar halak taki ambato barka da safiya kanwata,
Jalal gata fa Jalila kenan danake gaya maka kanwata juyowa yayi suka yi ido hudu da ita

Kallonta yayi tabbas itace, yarinyar da tazageshi agaban mahaifiyarasa jiya da daddare nan da nan annurin fuskarsa ya dauke yafara zaro idanu,

Cikinta ne ya duri ruwa tafara rarraba idanu zuciyartace take bugawa da karfi yau kam ta shiga uku
(Marar kunyar karya kin debo ruwan dafa kanki)

More comments more typing……..

????️????️????️????️????️????️
[8/31, 8:26 AM] Safiyya: ????????
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

_ABDUL  JALAL_

  _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

           PAGE-  4

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa’azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

I want comments not stickers????????????????
Comments dinku shine kwarin gwiwata

Special thanks to u my motivator
I dedicate this page to you
Anty MARYAM

   _My first novel_

“Shigomana ya kika tsaya anan”

Dagewa tayi ta boye tsoronta ta dai dai ta nutsuwarta, tashiga cikin dakin

“Kanwata ga Abokina kuma Dan uwana wato Jalal dukda kin sanshi amma nasan bazaki tunashi ba lokacin kina Karama sosai “

Kallon Jalal tayi taga mugun kallon dayake mata amma ta basar
“Sannu”

abinda tafada kenan ta maida kallonta kan Jawwad

“Yaya naga kanada bako in kungama na dawo karka manta da kiran Abba”
Ta juya tafita tana godewa Allah a zuciyarta da Jalal bemata komai ba

“Wannan ce kanwartaka?”
“Yeah ya kaganta so gentle and innocent”
“Good”
shine abinda yafada kawai
Mikewa yayi tsaye zetafi

“Bros yazaka tafi muna magana”

“Inada abunyi ne”

Ya fice wato ma kanwar Jawwad ce tabdijan yanzu ta zagi banza kenan anya kuwa ze kyaleta ko dai yagaywa Jawwad yaja kunnen kanwarsa tafita a harkarsa, to meye amfanin hakan,

Tana ganin Jalal yafita ta koma gurin Jawwad tasameshi inda tabarshi be tashi ba, shiga tayi ta zauna tace
“Yaya Jawwad magana nakeson muyi”
“Am all ears sisyna ina jinki fadi abinda kikeso”

ta Dan gyara zamanta tana fuskantarsa Wanda bayan kujerar dayake ya kasance window ne

    Zancen zuci yacigaba gsky y zama dole ya dau mataki inma ya kyaleta taci bulus kenan yana cikin wannan tunaninne se jeje yafado masa bari ya kirashi yaji wani shawaran ze bashi ne, 

hannunsa ya zura a aljihu da niyyan ya dauka wayan se yaji babu yadan yi shiru seya tuna tana kan kujerar da ya zauna a dakin Jawwad

“Yaya Jawwad meye hadinka da mutumin nan ne?”
“Kina nufin Jalal?”
“Eh shi nake nufi”
“Abokina ne kuma Dan uwana”

“Ta Yaya yazama Dan uwanka Yaya Jawwad wannan ba aminin arziki bane halinku Sam ba daya bane kallafa sigari yake shamaka a daki da ganin idonsa kasan tarbiyya ba ta wadace shi ba, kalli askin kansa, daganin bakinsa wannan yana shaye²
Zamanka tare da shi mutane zasu zata halinku daya Sam bashi da tarbiyya”
ta daga kanta wazata gani kawai taga Jalal a tsaye a bakin window yana kallonta da jajayen idanuwansa
Wanda hakan ya tabbatar mata yaji abinda tace

Ras! Ras!! Ras!!! Gabanta yafadi

 cikin palourn ya shigo ya dauki wayarsa bece komai ba ya fice

Jawwad be kawo komai a ransa ba Dan yasan halayen Jalal shiyasa bekawo yaji wani abuba kuma yabawa window baya Dan haka besan yazo wajen ba.

“Kinaji kanwata Jalal mutumin arziki ne ba yadda kike tunaniba inayimasa addu a in Allah ya yadda wataran zakiga ya dena ze wuce kaman ba ayiba kema kisashi cikin adduo’inki kidinga masa fatan shiriya”

“Yayana ka kula da kanka Dan Allah karka bari dabi’unsa su rinjayeka wataran Dan Allah”

“Karki damu kanwata ba abinda ze faru mun Dade tare da Jalal da zan zama irinsa da tuni na zama shima abinda kikaga yanayi kaddara ce babu abinda ze faru da yaddar Allah”

“To shikenan” ta fada tana mikewa
“Karka manta da kiran Abba
“to shikenan zanje insha Allah “

Jalal kam Shiru yayi yana tunanin wani mataki yakamata ya dauka akan yarinyar nan gata kanwar amininsa kanwarma kuma wadda yakeso ta yaze hukunta yarinyar nan ya bakanta mata ba tare da Jawwad ya gane ba baya son batawa abokinsa rai Dan tabbas in yayi mata wani abun Jawwad bazeji dadi ba,
Ko in kira Jeje yabani shawara idan na kirashima mezemin? wata zuciyar taba shi amsa
Mara tarbiyya!!! Wai nine bani da tarbiyya mtseeww yaja tsaki zakiga rashin tarbiyya ganin idonki.

(Kai JALAL bafa karya tayiba )

Jalila kuwa Cikin gida ta koma tunda ta shigo maama ta bita da wani irin kallo na zanyi maganinki ita kuwa Jalila bata san tanayi ba,

Gurin Abba nufa ta durkusa tace

“Abba nagaya masa yace yana zuwa”
“To shikenan diyata”

Wucewa tayi dakin su ta je ta tarar da Nana tana ninkin kaya taje ta zauna kusa da ita
“Nana kinsan me yafaru?”
Nana ta juyo ta bata dukkan attention dinta
“A’a sekin fada”
“Ingaya miki Jalal nagani adakin Yaya Jawwad yana ta shan sigari”

“Hmmm to ai bakiga komai ba Dan dai sigari kawai karewa har giya yake sha masa a daki wataran in yaje yasha yana tambelansa Yaya Jawwad ne yake nemo shi a club yakawo shi dakinsa ya kwantar da shi har giyar ta sake shi
Ke baki San komai bane shiyasa nace miki rabashi da Jalal ba abune me sauki ba” Nana ta karashe zancen jikinta a sanyaye

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button